← Book details Ciwon So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 125 OF 134

Sashe 125

Ciwon So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Agajiya ya zauna yana sauke gajiya ya labartawa Ammy cewar be samu Zahra ba.
llah yasa da sauki to
meen, ni ma abun da nake fata kenan, domin hankalinta a tashe yake saboda abun nan da ya faru
mman da ka kirata ko a waya ne
a kirata ya fi a kirga amman bata daga ba, ina tunanin ko ta bar wayar gida ne ko kuma wani abun ya faru da bata iya amsa wayar
llah ya sauwake
meen
A daren Abiey ya raya shi da nafila yana ta zuba godiya da yabonsa ga Allah, be kwanta ba sai da yayi sallah asuba. 8 na safe ya farka da sauri ya sauka saman gadon ya zura talkaminsa ba bedroom ya nufi gurin da yake aje tufafin daya cire ya raba jikinsa da jallabiya ya daura tawul ya wuce bathroom, wanka yayi ya fito jikinsa na ta kamshi expensive shower gel, madubi ya nufo yana goge jikinaa da tawul just like that yake jin he just want to dance yana kallon kirjinsa a madubin, rawa ya fara yi yana ba tare da kida ba sai jujjuyawa yake sai kai karshen dakin ya juyo ya dawo gurin madubin, can kuma ya aje tawul din hannunsa ya nufi wayarsa ya dauka ya kunna waka ya aje wayar kan drawer ya dauki fillo ya rike yana ta takawa kiyasi yake ace Zahra ce a gabansa, ya sumbanci fillon ya rumgume shi.
love You Babe
Ya kusan bata waya biyu a dakin sannan ya shirya ya fito sanye da blue jean sai bakar rigar da ta kara masa kyau da kwarjini da haiba, kitchen ya leka ganin Jummai ya karasa ciki ya dauki tsoka daya a cikin ferfesun data sauki ya fito yana goge hannunsa da tissue bayan ya wanke a sink, be takurawa kansa tsayawa ya karya ba da ma ace Ammy na nan ita zata takura masa da cewar sai ya karya zai fita, motar da ya dade be hau ba ya nufa ya bude ya saka mata key ya kunna motar. 8:30 ta yi masa ne a kofar gidan Alhaji Bashir bayan ya tambaya masu gadin sun fada masa cewar Zahra bata dawo ba, sai ya nemi guri ya faka so that ya jirata maybe zata dawo yin wani abu ko ita ko Mama.

Sai kusan karfe goma napep ta sauke Zahra bakin gate din gidan, da sauri Abiey ya fito motarsa ya nufo inda take sai da ta mikawa mai Napep dinsa sannan ta kalli Abiey cike da damuwa.
iayatee...

Bata amsa ba sai kallonsa take ta tabe irin yadda yara suke idan suna son a taba su fara kuka, be yarda ya sake ce mata komai ba ya jata jikinsa ya rumgume.

'm here
nce ba a gane abun da yake damunsa ba, yanzu ma sun sake shiga da shi gurin wani gwaje gwaje, Mama tace wai yana son zama a hannun Mr Bashir ne, ni kuma gani nake kamar mutuwa zai yi
12/28/22, 11:23 - Buhainat: Ya dagota daga kirjinsa ya rika fuskarta da hannanyen yana ta yawo da idonsa akan fuskar tata.
ai ji sauki, kar bakinki ya sake furta haka ba zaki sake fuskantar wani bakinciki ko damuwa ba Inshallah
Ya share mata hawayen da suka zubo mata, bata dama da ganin a bakin gate suke ba ta maida kanta kirjinsa domin tana son kasancewa da shi, kamshin turarensa na daga abun da ke kwantar mata da hankali, ga wata natsuwa da rahma da take ji idan ya rumgume ta.
a yi magana da Ammy da Mai Martaba?
h Ammy ma ta aiko ni tun jiya na dauko ki, sai masu gadi suka fada min kun tafi asbiti, kuma ba kira wayarki baki daga ba
Da sauri ta dago daga kirjinsa ta kalli fuskarsa.
mmy?

Ni miye nawa a ciki to?

Ai ba da sanina aka yi komai ba, ka ga zata zo ta mana fada a tare ko kuma cewa zata yi ka sake ni
Ta fashe da kuka, sai ya rumgume yana murmushi da be bari ta gani ba.
o ni ma dai ban san abun da yasa ba, amman dai ya kamata muje sai mu ji ko ma minene
i ba zan je ba Wallahi ka je ka ce mata na bata, baka gan ni ba idan kuma ta ce ka sake ni ne ai ba dole sai mun je can ba
o dole mu tafi mana, ya kamata mu ji dalilin kiranta be kamata ki yanke hukunci ba tun yanzu
i dai ba zan je ba, waya sani ko faffala min mari zata yi ma, kuma ta ci min mutunci ta ce min mayya
Be san lokacin da dariya ya so subuce masa ba, sai yayi saurin kawar da kanshi.
aboda kin auri
anta zata ce miki manya ta falla miki mari kuma?
h mana sai tace na nace nace na lake maka, alhalin ba da sanina aka yi ba
anzu dai kamin ki shiga ciki ki fara zuwa gurin Ammy, ko ma dai minene sai mu je
Sai da yayi da gaske sannan ta yarda ta shiga motar, yana hawan titin ya kwantar da ita jikinsa yana driving da hannu daya, ita kuma sai rara kuka take a hankali, sai da ya faka motarsa a harabar gidan sannan ta dago ta kalleshi.
dan tace ka sake ni sakina zaka yi ko?
a zan iya yanke hukunci a yanzu ba
Ya sumbaci hancinta, sannan ya bude gefensa ya fita.

ZAHRA POV.

Zagayowa yayi ya bude min na fito wasu hawayen na taruwa a idona, tunanin maganar Mama da kuma kiran da Ammy take min sai ya zame min biyu, daman can ina ta tunanin yadda Ammy zata ji idan ta san gaskiya, side hug yayi min wata kila ya manta a cikin gidan Ammy muke ko kuma dai kunyar tasa ce ta yi karamce oho, muka nufi kofar shiga falon, yana bude kofar falon na ji fitsari ya cika min mara, da sauri na janye jikina daga nashi amman hakan be hana shi miko hannunsaya rika hannuna, muna kokarin shiga falon ina buge masa hannu alamar so nake ya sake ni kar Ammy ta gani.

Da sallama ya shiga falon na ina jin muryar Ammy ta amsa masa yan hanjina suka kara kadawa, a zaune muka same ta ni dai ina kallonta na yi saurin rufe ido har sai da Abiey ya zaunar da ni, ido daya na fara bude na kalli saitin inda Ammy take ganin ni take kallo fuska ba yabo ba fallasa ya saka dole na bude idon gaba daya, na kara matsawa kusa da Abiey sosai domin gani nake kamar ma zata iya aiko min da marin daga inda take.
allahi Ammy ba ni na ce yayi ba, ba da hadin bakina aka aikata ba, ban san sun shirya hakan ba sai da komai ya faru, dan Allah ki yi hakuri
Na fada tuni na fara kuka, kokari akwai nake na wanke kaina kar Ammy ta dora min laifi.
anzu ya kike so ayi?

Na bar shi ya cigaba da zama da ke ko kuma na ce ya sake ki
Ammy ta tambaya tana kallona babu wasa a fuskarta.
12/28/22, 11:23 - Buhainat:
dan har baki son aure zaki iya cewa ya sake ni, amman dai ni ina son shi, kuma shi ma yana so na, idan kina ganin akwai maslaha a sakin, ni ba ruwana sai ya sake ni
Plate din dake jikinta ta aje ta mike tsaye ta nufo inda muke zaune a take natsuwata ta bar jikina zuciyata na raya min marina zata yi, na matse Abiey sosai kamar zan shige jikinsa.
an Allah ki yi hakuri
Abiey ya dora hannunsa a jikina kamar zai rumgume ni kuma be rumgume ni din ba, zuwa ta yi ta kama hannuna ta dora akan na Abiey.
ahra fitinanniya, kin fitini zuciyar
ana kin hana shi sukuni har sai da ya auro ki ko?

To ga amanar shi nan na baki, karki kuskura ya kawo min kararki cewar kin masa laifi, zan miki hukunci mai tsanani, Allah ya sakawa auren da kuka yi albarka ya ba ku zama lafiya ya albarkacin yaran da zaku haifa da zuri'ar ku, Mai Martaba ma ya sakawa aurenku albarka shiyasa na ce Aliyu ya kawo min ke ni zan miki wannan albishir din
Ta karasa tana murmushi, da sauri na kalli Abiey sai ya sumbaci goshina yana murmushi ko kunyar Ammy ba ya ji, fashewa na yi da kuka na mike tsaye na rumgume Ammy, sai ta saka dariya ya kankame ni.
o Shagwababbiya, mijinki zaki yi ma wannan ba ni ba
Ban yi zaton komai zai zo mana da sauki kamar haka ba, kamar wata Sarauniya haka na zama a gidan Ammy Abiey kam be da madubi sai ni, tare da ita muka koma asibiti ta duba Amir a nan ta sanar da Mama abun da ya faru ni ma na kara shan labari yadda komai ya faru, ni kaina na yi farinciki jin cewar Abiey ya shirya da mahaifinsa.

Da dare likitoci suka sake tabbatar mana cewar ba su ga wata matsala a tare da Amir ba, gashi kuma be daina kukan da yake ba, sai dai ya sha nono na kadan sai ya saki ya cigaba da kuka, muna a wannan halin Mr Bashir ya shigo tare da Ummiter da wata da ba zata wuce sa'ar Ummiter ba ko kuma ta dara ta kadan kamannin dake fuskar Ummiter ne suke zube a fuskar Matar da nake kyautata zaton budurwa ce ita ma.

Bayan mun gaisa ta sake dubana ta ce.
e ce Zahra?
Chapter 125 · 0% Book details