← Book details Ciwon So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 74 OF 134

Sashe 74

Ciwon So Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Ni kuma na nufi kitchen da sauri na rufe aka bar Abiey shi kadai a falon, tab na kunna na jike jikina da ruwa na cire hijab dina na fara korar sauran zumar da ta biyo ni sannan na nufi kofar baya na bude na fice da gudu.
12/28/22, 11:06 - Buhainat: Gurin Haruna mai gadin na tafi shi ya karasa korar min zumar sannan na fita babu ko talkami a kafata haka na na tari abun hawa na hau na fada masa gurin da zai kai ni.
mman lafiya kafarki ba talkami kuma ba ki yi kama da masu tabin hankali ba
allahi zuma na jefa ta biyo ni sai na bar talkamin a can
Dariya ya fara yi, shi da mutumen dake cikin napep din da alama shi ma guri daya za a kai mu.
hiyasa kika jika kayan?

Daman kyakkyawan mata basa jin magana kina daya daga cikinsu da alama
Mutumen ya fada sai na yi dariya na rufe fuskata, muna kai wa kusa da wani shago ya bukaci mai nepep din ya tsaya sai ya kalleni.
ize nawa kike sakawa?

Ya fita, be dade ba sai gashi ya dawo da wasu talkamin roba masu kyau ya mika min na karba cikin jindadi da murna na saka ina masa godiya, daidai kofar gidansu Yaya Maryam aka sauke ni sai ya karbi number wayar Mama da nufin zai kira ni ni kuma na fita na shige cikin gidan, ina shiga na samu Mijinta a waje suna cin abinci tare.
yeee masoya
ismillahi yanzu zaki dagula mana lissafi
Mijinta ya fada sai na saka dariya na nufi kitchen dinta na dauki plate na zuba abinci.
uta kin samu yanci?

Ina kika fito da jikanken tufafi?

Ban fada mata ba saboda ina tsoron kar taje ta fadawa Mama wata rana, bayan na gama cin abincin mijin Yaya Maryam ya ara min wayarsa na yi ta game har sai da na gaji.

Da yamma ba yi sallama da gidan na mijinta ya bani kudin napep bayan na sato mata sabuwar atamfar da bata saka na boyeta a hijab na fito kamar ban dauki komai ba.

Idan na yi laifi bana tafi gida kai tsaye musamman idan na san Mama ko Baba na yi ma laifin na kan saka Deen agaba ne domin yana hana Mama dukana, idan har ya saka hannu ya dake ni to abun da ya shafi samari ne, ban tafi gidan kai tsaye ba sai na nufi gidan Hajiya.

Ko da na shiga na tarar Hajiya ta gama soya kaji tana kasawa.
aa mu kan Baba be kai mana ba
Shi ne abun da na fara fada farkon shigata gidan, ko sallama ban yi ba daman tun daga zauren gidan nake jiyo kamshi.
i ma ba kawo min Yaya ba, Yayana ya aiko min da abuna Wallahi, na san halinki zaki iya tafiya ki fada mata cewar an kawo mana nama ki hada fada
e ma Hajiya ai kin san sai na fada Wallahi
o ko Wallahi ba zan yi kashin nan dake ba, ba ke dai ba kya jin magana ba, to ai sai ki yi mu gani
Ban dauka da gaske Hajiya take ba har sai da ta kasa naman ta bawa Bahijja nata na Deen kuma tace a kai masa dakinshi ta dauke nata ta shige daki.

Abun ka da marar zuciya kuma kwadayayyina haka na je na zauna gindin murhun nan ina lasar tukunyar data soya kazar da ita.
ahra me kike nan
Deen da fitowarshi kenan daga wanka ya tambaya, juyowa na yi na kalleshi sai na yi dariya ina kallon kirjinsa dake kara fitarta mazantakansa wato Muscle, a zatonsa wani bangaren na jikinsa nake kallo domin yana daure da tawul ne, a take ya hade fuska.
iye haka Zahra?

Me ke damunki ne?
ikinka nake kallo fa na ga irin na masu daukar karfi ne
Ya kalli jikin nasa sannan ya sake kallona.
a aka yi kika fito?

Ba Mama tace karki fita ba?
a bata hakuri ne sai tace na tafi, kuma a hanyata ta tafi na ga mahaukaci ya bini shi ne nake son ka rakani gida
o tashi a nan
ai nake lasa, Hajiya bata ba ni ko tsinke daya ba wai saboda na ce sai na fadawa Mama an siya mata nama
Dakin Hajiya ya nufa ya dage labulen ya leka.
ajiya ina nama na?
ana dakinka
Ta amsa mishi tana cin naman, sai ya saki labulen ya juyo ya kalleni.
e ki dauki nawa ki ci
Na mike da sauri na nufi dakin na dauki na san inda ake aje masa abu sai na nufi gurin na dauki kwanon naman na hado da wata yar karamar leda dake gurin, sai da na fito sannan ya shiga ya shirya ni kuma na saka naman a gaba ina ta ci na boye ledar da na dauko ina lalabawa na ji abu mai kamar haki a ciki.

Hajiya na fitowa ta same ni ina cin naman sai ta fara fada wai shi yake daure min ina kara lalacewa.
aba Hajiya ya za'ayi ki bani nama Zahra tana gidan nan kuma ki yi tsammanin zan iya cinsa na hanata?

Ai kara ki bata abu ki hana ni da ki ba ni ki hanata, bana son abun da zai taba yarinyar nan Wallahi
Shi ne abun da Deen ya amsawa Hajiya da shi, sai ta bude wani sabon babin na fada
o yayi kyau sai ka cigaba da yi ai, gashi nan sai kara lalacewa take kuna goya mata baya
Yana ganin na bata fuska zan yi kuka yayi hanzarin janyo kofar dakinsa ya rufe.
ashi muje
Haka na fito da robar naman sai da muka kawo zaure ya cire dankwalin kaina ya goge min bakina ya gyara min fuskata.
aya Deen ka siya min lemu dan Allah idan na je gida zan fi jindadin cin nama
Ya amsa min da kai fuskarsa babu yabo ba fallasa daman can be fiye dariya ba, na bude naman na ci na mika masa ragowar.
a ci wannan
a ni na bakinki
Ya fada yana kallon yadda nake tauna naman a bakina dariya na fara yi domin ban dauka da gaske yake ba, har sai da ya kai hannunshi cikin bakin nawa ya ciro naman ya saka a bakinki.
aka kyama?

Na tambaya ina yatsina fuska domin kazantar hakan nake ji.
na yi mana, amman dai ke bana kyamarki
Da murmushi yayi min furucin sannan ya wuce gaba na bi bayansa.

Sai da muka iso titi ya bukaci na tsaya zai tsallaka ya siyon min lemun, sai na matsa jikin wata transformer na tsaya shi kuma ya tsallaka titi, gefena na ji ana sallama sai na juyo a hankali na kalli mutumen dake sanye da rigar wandon jean da T-shirt, sanin Deen zai iya hango ni ya saka na matsa gefe ba amsa masa ba, sai ya sake matsowa wannan ya sake min sallamar.
a'alaissalam
annu yan mata ya kike?
adda kake
Na amsa ina ta son nayi yanga kuma ban iya ba, dariya yayi ya juya ya kalli wata motar sojoji dake can gefe sannan ya sake kallona.
ana son na tsaya magana dake a hanya, ina ne gidanku?

Ko kuma number waya zaki ba ni da zan kira ki
Kamin na amsa masa har Deen ya karaso gurin yana zuwa ya fara hararata.
e baki da hankali ko?

Ko wane kare da mussa ya tare ki sai kin tsaya ne?

Malam tafiya?

Mutumen mai kirar masu karfi ya kalleshi.
aye kai?
na ruwanka da waye ni?

Ku da kun ga mata sai neman musu magana kamar kun haukace
Mutumen ya kalleni.
iye alakarki da shi
a mu da alakar komai
Mutumen kamar jira yake ina rufe baki, ya dauke Deen da mari, cikin zafi nama Deen ya rama marin har ya kara masa da gyara, kamar kyabtawa da Bismilla haka motar sojojin dake fake gefe ta karaso kusa da mu sojiojin ciki suka zagaye mu ashe akwai wata motar ma dama da ni ban lura sai a lokacin da suka suka karaso suka zagaye mu, Deen na ganin haka ya durkusa kasa kamar mai neman gafara.
an Allah ka yi hakuri, mahaukaci ne ni Wallahi sam sam sam ba ni da hankali dan Allah ka yi hakuri, idan ni din ba mahaukaci ne ba Allah ya tsinen
Mutum ya dauke Deen da mari, jikin Deen sai rawa yake kamar ba shi ba.
e na san ki ma?

Deen ya tambaye ni yana kanne min ido daya alamar yana son na amsa.
a baka san ni ba
a gani ko?

Idan ba mahaukaci ba waye zai yi haka?
Chapter 74 · 0% Book details