← Book details Ciwon So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 134

Sashe 18

Ciwon So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai daf da sallah La'asar muka yi wanka shi ya fita zuwa masallaci ni kuma na yi tawa Sallar a gida, babu komai a cikin addu'a sai sai namawa mahaifina gafara da kuma rokon Allah ya ba mijina lafiya ya bude mana hanyar da zamu samu kudin magani, daman ita ce addu'a tun daga lokacin da muka shiga wannan matsalar.

Baya na gama na dauki carbi ya fara addu'ar da Mama ta sha fada min cewar tana maganin ko wane kalar damuwa kuma tana yaye bakinciki ta kawo haske cikin al'amurra wato La'ilaha illa anta subhanaka inni kuttu minal zalimin.

Ban aje carbin ba sai da aka kira sallah magariba, abun ka da mai ciki sai da na sake dauko wata alwalar sannan na gabatar da sallah, ina sallamewa na ji muryar mijina ya shigo sai dai addu'ar da nake bata bani damar amsa masa ba, ina kokarin na juyo na kalleshi sai na ji ya rumgume me.
aman Zahra i love you di you know that
Na daga masa kai sai ya dawo gabana ya zauna yana min murmushi.
llah ya sauke ki lafiya, i can't wait na ga abun da zaki haifa min ina son Allah ya muna wannan ranar
Ya fada da irin sigar dake bani kamar mijina ba zai ga abun da zan haifa ba.
an haihu Deen kuma zaka ga abun da na haifa da yardar Allah
Na fada ina kai hannu na taba fuskarsa ga mamakina sai hawaye suka sauko masa fuskarsa kuma dauke da murmushi.
ada min Deen wani ciwon kake ji?
o bana jin komai
Ya fada min yana girgiza kai, a take hankalina ya tashi domin ganin hawaye a idon mijina abu mai matukar wahala, ba kasai abu ke kasa Deen zubda hawaye ba.

Wata kila kuma yana cin ciwon ne boye min yake ko kuma wani yanayi yake ji na dabam sai na rasa gane ko daya.
an Allah ka fada min idan wani abu kake ji
azun dai ina ji, amman yanzu bana jin komai amman wannan ciwon Zahra bana tashi ba ne na sani, kuma ban san a wane hali zan barku ba, ke da abun da zaki haifa
Cikin dakiku hawaye suka hadu a idona suka taru suka zubo a fuskata.
ashi muje asibiti
ikita ba shi ne Allah ba, ba zai iya canja abun da Allah ya tsara zai faru ba
hy are you telling me this Deen?

Why?
aboda ina son ki zama mai karfin hali, and ina son ki rika neman min gafarar Allah bayan mutuwa
Gaba daya sai na ji kamar mafarki nake, domin Deen be taba fada min wata magana da zata tashi hankalina ba irin wannan, wata kila wani yanayin yake ji na dabam.

Fashewa na yi da kuka sai ya matso kusa da ni ya rumgume ni ya dora hannunsa saman cikina, a take cikin nawa ya fara motsi kamar zai fasa fatar cikin ya fito ni kaina sai da na yi mamaki domin be taba min haka ba hasalima cikina ba mai motsi ba ne sai idan ina jin yunwa ko kuma can ba a rasa ba, murmushi yayi mai sauti ya daga hijabi ya sumbanci cikin ya dora kansa a sama ya lumshe ido.

Haka muka zauna tsit na kasa cewa komai shi ma kuma be dago ba har aka kira sallah Isha'i, sannan ya daga ya mike tsaye sai na bishi da kallo har ya fice.

Juyowa na yi na fuskanci alkibla na daga hannuna sama.
a Allah ni baiwarka ce mai yawan zunubi mai yawan aikaa kuskure, Allah ga baiwar Zahra, Allah makaskanciya a cikin bayinka, Allah ba ni da gata sai naka, ba ni da kowa sai kai Allah, ya Allah dan mijina zai yi rayuwa mai tsawo da wannan ciwon ka sani, idan kuma ba zai yi ba Allah ka sani, Allah ka dauki rayuwata kamin ta mijina, Allah karka bari na dandani dacin rashin mijina a kusa da ni...

Na fada addu'ar da wasu irin hawaye da ban san adadinsu ba, sannan na kwanta a gurin ina kuka kamar raina zai fita, daker na samu kukuna ya kwanta min har na samu na yi sallah Isha'i, sai na kasa tashi sai rarrafe na yi na isa kusa da gadona na janyo filo na dora na kwanta ina yadda kaina yake sara kamar zai fashe.

Ban kwanta dan bachi ba sai dan na samu salama a zuciyata da kuma ruhina, sai kuma bachin ya bani hadin kai yace fir ba sai idonki ba Zahra, har tara da rabi ido na rufe amman babu alamar bachi a kusa ni, sai kusan goma na ji shigowarsa cikin falon bayan ya rufe gidan ya karaso cikin dakin rike da ledar, da gangan na ki na bude ido har ya karaso kusa da ni ya leki fuskata.
ahraty...

Ban amsa ba, ban kuma motsa ba, hakan yasa shi aje ledar hannunsa ya saka hannunsa biyu ya dauke ni ya dora saman gado ya cire min hijab ya gyara min kwanciyata yadda zata min dadi, sannan ya warware net din dake nade ya rabe iskar fankar dake aiki, ya nufo wayata dake ringing ya dauka.
ello Mama
Ban ji abun da Mama tace masa ba, sai bayan sun gaisa na ji yana fadin.
a yi Bachi da safe zan fada mata kin kira Inshallah mun gode
Sannan ya aje wayar tare da sauke ajiyar zuciya, ya tashi ya nufi bandaki ina jin motsin ruwa sannan ya fito ya nufo ni ya taba ni.
abe na tashi ki yi wanka kar dare yayi jiki jikinki ba dade, kin san ba ki saba bachi ba ki yi wankan dare ba
ana son wanka ni dai hau gadon ka rumgume ni
Na fada ba tare da na bude idon ba.
aman ba bachi kike ba?

Toh Bari na yi wankan sai na zo na rumgume ki
anzu fa
Sai ya dawo da sauri ya sauro saman gadon ya rumgume ni, wanka da ba mu yi ba kenan daga ni har shi kuma muka kasa bachi dare sai ya zame mana rana.

Akan idona aka kira sallah azuba ina kokarin barin jikinsa sai ya rigani tashi ya rika ni muka shiga bandakin da taimakonsa muka yi alwala bayan mun fito ya shimfida min abun sallah shi kuma ya fita zuwa masallaci daman sallahr jam'i bata wuce shi tun da na sani har yanzu da muke tare.

Ina lazimi ya shigo, ya juyo na gaishe shi muryar cike da damuwa sai ya amsa cikin far'a da karfin hali irin nasa.
i kwanta ki yi bachi zan hada miki breakfast
u kwanta tare idan na tashi sai mu sha tea
Ya amsa min, sai na tashi muka sake komawa saman gadon da niyar bachi sai dai shi a gurinsa ba bachin ne a ransa ba, a take ya sauya salon bachi zuwa biyan bukatarsa.

Sai kusan takwas na samu bachi yayi gaba da ni, guraren goma da yan mintuna na farko babu kowa a bayana sai filo ga breakfast dina saman bedside drawer, ina yunkurawa na tashi na ji kaina na sara irin tsararwa da be taba yi ba, yayi min wani irin nauyi kamar ya hadu gaba da yamma an dora min a saman kam.
nnalillahi Wa'inna Ilaihirraji'un
Shi ne abun da na furta sannan na samu sukunin tashi.

Ya gyara dakin kamar yadda ya saba, falon ma tsab ya goge ko'ina tsakar gidan tass kamar ni na gyara ya share ko'ina ya wanke komai da muka bata.

Komawa na yi daki na samu dankwali na saka a kaina sannan na shiga na hada ruwan wanka na watsa a jikina na fito na saka kokon a gaba na kasa sha, sai hawaye daman idan ban yi kuka ba me zan yi?

Haka na wuni cikin damuwa da tunani har wani abu nake jin yana min yawo a zuciyata gashi an ce ba a son mai ciki tana yawan tunani saboda zai iya haifar mata da matsala.

Bayan na yi sallah azahar na dawo falo na kunna kallo wai ko zan samu sukunin zuciyata wata kila na iya saka wani abu a cikina, amman sai kallo ya ki burge ni, babu dadi sai kawai na ji ina hawaye.

Sai da na yi da gasken gaske na yi ta ambaton Allah sannan na samu hawayen suka tsaya min.

Misalin karfe uku na rana na ji ana kwankwasa kofar gidan a take gabana ya fadi for now reason, ba tare da tunanin komai ba na nufi kofar na leka sai na abokan aikinsa Usman da Sani suna rike da Deen idonsa a lumshe yana numfashi a wahale.

Da sauri na bude kofar hawaye har sun gama wanke min fuska.
na ganin Maleria ce ta yi masa mugun kamu, muna aiki kawai muka ga ya fadi jikinsa yayi zafi sosai, amman dai mun kai shi chemist an amsa allura
Usman ya fada, sai na kasa ce musu komai kuma na kasa janyewa jikin kofar su shigo da shi sai kallon fuskar mijina nake, kamar ya san ina kallonsa sai ya dan dago idonsa ya kalleni, gaba daya kalar idonsa ta canja ta zama rawaya kamar mai yellow fever, baya baya na yi na rufe baki ina fadin.
nnalillahi Wa'inna Ilaihirraji'un
10/1/22, 22:03 - Buhainat: *
CIWON - SO
By Khadeeja Candy
ABIEY POV.

Dawowa yayi falon ya zauna, Anty Amarya ta tsare shi da ido irin kallon nan na babban da ya tsare yaro da bayan jin magana, and ba zai iya daga ido ya kalleta ba, sai shafa kansa yake.

Cikin abun da be fi minti talatin ba da yan dakiku Ammy ta iso gidan, yanayin yadda ta turo kofar falon ta shigo ya isa ya karantar da su a fusace take.
bu dai kamar wasa sai gashi kin zo
Anty Amarya ta fada tana dan murmushi domin ta san Ammy ba kanwar lasa bace, sai dai wani lokacin ta kan dauke ido akan abun da ya shafi Masarautar ko Mai Martaba.
u ba zan zo ba, sai na zuba ido a saka min da a gaba?

So kike su sake samun wata hanyar ta bata masa suna?
Chapter 18 · 0% Book details