Sashe 109
Ciwon So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kuma Allah ya taimake ni yayana suka samu tarbiya da suka gama karatu na suka samu aiki, Aliyu kuma ya karkara a bangaren kwallon kafa domin abun da ya fi so kenan ni kuma na goya masa baya
12/28/22, 11:06 - Buhainat:
ashin samun kula daga mahaifi yana matukar tayarwa Aliyu hankali yana damunsa sosai, har yan'uwansa suke son yi masa gori da haka, wata rana da kaina na aka shi a mota na shiga dashi har cikin fadar na zaunar da shi a gaban matan Mai Martaba da yayansa na ce ya fadawa Aliyu da duniyar cewar ba shi ya haifi Aliyu ba, sai ya girgiza kai yace Aliyu
ansa ne ko be fada ba kowa ya kalli fuskarsa zai san da haka, yace Aliyu jininsa ne, a gaban matansa yace Zainab ma da ba yata ba ina sonta kamar yata Umaima saboda ta fito daga cikinki balle Abiey da yake jinina.
Daga lokacin sai ya samu kwanciyar hankali, nima na dan samu amman na gagara mantawa, sai dai samun ki da Aliyu yayi, na ga farinciki a tare da shi irin wanda ban taba gani ba, kuma kin kawarda tunaninsa kin dauke hankalinsa daga damuwar da mahaifinsa ya saka masa, neman aurenki ma da aka je sai kanensa ne da yan'uwa suka je, amman shi be ce komai ba
A rayuwata ban taba jin tausayin wani mutun kamar yadda zuciyata take tausayin Ammy a yanzu ba, daker na iya takaita kukana na share hawayena na ce.
mmy babu wanda baya kuskure, kuma abun da kika aikata Allah ya kaddara sai kin aikata haka din saboda haka ba ki isa ki tsallake haka din ba, ki saka a ranki komai be faru ba, kuma na miki alkawari ba zan taba gudun Abiey ba
Rumgume ni ta yi tana dariya tare da kuka a lokaci daya tana saka min albarka.
Muna cikin wannan halin Abiey ya shigo dakin ya same mu a lokacin da har mun dauko wata hirar ta duniya, sai dai ina jikin Ammy ne idanuwana da nata sum kumbura.
e kuke yi ma kuka
Abiey ya tambaya cikin fargaba duk da kasancewar ya ga murmushi a fuskarmu, ni kuma sai na amsa masa da cewar, ina bawa Ammy labarin mahaifina da ya rasu ne shi ne abun ya saka mu kuka, ya fada cikin labarin da muke aka dasa wata sabuwar hira.
Na dade a gidan sannan Abiey ya maida ni bayan ya bi da ni ta gida.
Hiayatee haka Abiey yake kirana tun daga lokacin da aka yi ana baiko, muka cigaba da rayuwa da nunawa juna soyayyah, Ranar da na gama graduation na Secondary school na ga gata kamar yar wani minister duk wani abu da zan rawa kawaye da kuma wanda na yi amfani da shi Ammy ce ta yi min, sannan ta tara yan'uwanta da Anty Amarya daga bangaren Mai Martaba suka zo.
A lokacin ne Abiey yayi min kyauta da wayar hannu daman na dade ina mafarkin samun wayar amman ba dama domin Mama ba zata siya min ba, na san kuma idan na yi ma Ammy ko wani magana za a ce na bari sai nan gaba, ashe gaban a kusa take.
Daga lokacin sai shakuwa da soyayya ta karu tsakanina da Abiey wayar safe dabam ta rana dabam haka ma ta dare, ban tabbatar ina Abiey sosai da sosai ba har sai da na fara damuwa da alakar dake tsakaninsa da Safeena, duk kuwa da na san kawarsa ce tun kamin ya hadu da ni, sai dai a yanzu kawance su na cutar da ni, ko dariya yayi mata sai na ji raina ya bace, sanadin haka na shata musu line da ban yi zaton Abiey zai bi ba, sai gashi ya saurareni kuma ya jingine abotarsu a gafe.
Bayan kammala bikin makarantar sai aka fara maganar aure a tsakanina da Abiey, a lokacin ne Mama ta tuntubi Baba domin ya fara bata wani abu a cikin kudin gadon mu da ta bashi ta fara siya min wasu abubuwan, sai ya fara kame kame daga karshe ya sanar da ita cewar ya taba kudin kuma sa'ar siyar da Furnitures da ya fara abun be karbu ba, ba Mama kadai ba ni ma kaina na shiga tashin hankali a lokacin, domin na san da kudin Mama ta dogara kamar yadda ta yi ma Yaya Maryam hidima da su.
Yaya Maryam da Mama suka rika siyen abubuwa da be fi karfinsu ba suna aje min.
Ana sauran wata biyu bikinmu Ammy ta samu Mama ta fada mata cewar ba za su kawo lefe a yanzu ba saboda gujewa idon mutane tace za a aje min komai a dakina sai dai na tararda shi acan, amman za su min tufafin da zan saka na biki, a nan ta yi ma Mama albishir da cewar bata bukatar komai daga garemu apart from kayan daki har zuwa na kitchen ta tanadi komai, idan an daura aure ni kawai za a kai musu, a ranar Mama ta kwana da farinciki domin samun mace irin Ammy abu ne mai matukar wahala.
Bayan sati daya da faruwar hakan Ammy ta maida ni gidanta aka fara min gyaran jiki ana ba ni kulawa, kar ka so ganin yadda fatata ta zama, fari na ya kara fitowa kyauna ma ba a magana, hankalina a kwance muna ta zuba soyayya ni da Abiey, sai dai duk tsawon lokaci Deen ya dauke kafa daga zuwa gidanmu sai dai dukanmu mun dora hakan a kan rashin lafiyar da aka ce yana yi, na sha zuwa duba shi kamar yadda Mama ma take zuwa, sai dai daga lokacin da na koma gidan Ammy da zama sai ya zamana bana fita ko'ina daga gida sai gida, Abiey ma sai a waya muke hira, idan kuma yana son ganina sai dai yayi irin shigowar nan da babu sanarwa ko kuma ya ritsamu a falo ko
aki.
Ba ni da wani damuwa ko tashin hankali ina rayuwar kamar wata yar sarki kauna ake nuna min ga ko'ina, har auren mu ya gabato ban ga wani canji a gurin Abiey ko iyayensa ba har sai da ya rage sauran kwana biyu bikimmu, duk wasu shagulgula an gabatar kamin ranar sai dai na lura Ammy da Dr Zainab kamar akwai abun da suke boye min, Abiey ma na fahimci akwai damuwa a tare da shi ta hanyar hirar da muke, Dr Zainab ta zo ta dauki jinina ta fada min cewar ta dauki na Abiey zata je ta gwada, ban kawo komai a raina ba duk da kasancewar an dauki na farko tun kamin a saka mana rana, sai na dogara da abun da ta fada cewar ba zata bari a daura auren ba tare da ta sake yi mana gwaji ba, ba a matsayinta na yayar miji kuma likita, ni kam ban dauki abun da muhimmanci ba, har zuwa ranar da za a daura aure ban samu wata matsala ba, ina wani dakin Ammy ana min kwalliya na kira Abiey na tambaye wane kalar tufafi ya saka sai yace min farare kamar nawa.
Bayan na aje wayar ya sake kirana yace yana son magana da ni a kebe, na ji tsoro sosai kuma na samu kaina da faduwar gaba.
Shi ya fada min dakin da zan same shi na taka da kafa cikin farin lace da mayafi na isa har gurin na shiga cikin dakin, sai na same shi rai a matukar bace har baya iya kallona.
ahra....
Sai yayi shiru, hakan ya saka na tari gabansa ina kallonsa fuskata da murmushi.
inene?
Be iya fada min ba ya fice ya bar ni, cikin tunani da sake sake kala kala, dawowa na yi dakin Ammy na zauna cikin damuwa da sanyin jiki, mutane da ke cike da dakin sai tambayar damuwata amman na kasa furta komai domin ni ma ban san damuwar tawa ba, kawai dai na fahimci akwai matsala ne.
Babu wanda ya iya fada min komai sai Ammy da kanta ta kori kowa a dakin ta zaunar da ni tana karantamin yadda kaddara take zuwa da yadda ake son bawa ya karbe ta.
mmy duk ban gane wannan ba, mi ke faruwa ne?
ahra ina son ki dauki wannan a cikin kaddararki, ina mai baki hakuri kuma ina mai bakinciki sanar da ke cewar ba za a iya daura aurenki da Abiey ba a yau...
With full confidence Ammy ta fada min haka, da farko ban yarda ba sai na dauka wasa suke min, har sai da ta jaddamin cewar da gaske ne ba za a daura ba, da na nemi hujja sai ta dauko takardar gwajin da Dr Zainab ta yi ta, bana bukatar wani ya karanta min abun da takardar da kunsa domin ni ma na yi karatu kuma ina cikin yan gaba gaban da makaranta take alfahari da su saboda kokarinsu.
mmy ko dai ba daidai ba ne
Na tambaya bayan hawayen idona sun gama jika takardar jikina yana ta rawa.
i yi hakuri Zahra kadarar ku kenan, shi kansa Aliyu yana cikin wani, shiyasa ya kasa sanar da ke
na son na ganshi Ammy, Ammy wannan takardar da gaske ne?
Kai kawai ta daga min ta share hawayen da suka cika idonta ta juya ta fice a daki, kamar makauniya haka na fadi ina lalaben abun da be bata ba, kuka ya hado kayansa yayi masauki a gurina.