← Book details Ciwon So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 134

Sashe 21

Ciwon So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ki bi Yayarki ki kwana a gidanta, idan kuma gidana kike son kwana sai mu tafi
Shi ne abun da Mama ta fada a lokacin data karasa kusa da mu.
an kwana a nan
Na fada muryar a sanyaye kamar cike da damuwa.
a ba zaki kwana a nan ba, damuwar kuma ta isa haka, idan kika kwana a a nan ba zaki dauke masa ciwo ba, ki yi ta addu'a kawai
Zan bude baki na yi magana Yaya Maryam ta rika fuskarsa.
ar kanwata ki rika jin magana jin?

Tun da Mama tace mu tafi ki bini mu tafi mana
Na daga kai a hankali akamar toh ba san ina son zuwan ba, sai dan bana son na yi musu a yanzu, domin bani da karfin musun da dai a da ne zan iya har sai sun yarda sun barni.
ari na yi ma Mama sallama
Na fada ina juyaawa na koma inda na fito, tafiya kamar wanda ke jin nauyin kafa haka nake takawa har na isa cikin dakin na tura na shiga sai na samu Hajiya ita kadai a dakin Bahijja ta fita, wata kila an aike ta siyo wani abun ne ko kuma waya take oho.
ajiya zan bi Yaya Maryam ma kwana a can
oh Allah ya tashe mu lafiya, Zahra dan Allah ki kwantar da hankalinki kin ji
Na kalleta kawai na dauke kai na kalli Deen na matsa kusa da shi na kai hannu zan taba na ji ko jikinsa da zafi ko akasin haka sai Hajiya ta yi saurin rike hannuna.
arki taba shi, baki ji abun da likitoci suka ce ba?

Na kalleta da sauri ina mamakin yadda yau ciwo zai hana ni taba mijina, kamin na juyo na kalli Deen da ya bude idonsa a hankali ya kalleni har yanzu idonsa ba su koma daidai ba, suna nan da kalar rawaya wato yellow sai ma kara kala da suka yi, murmushi ya sakar min, a yau kuma sai murmushinsa yafi min kyau fiye da ko yaushe, sai na ji kamar be taba murmushi mai kyau irin wannan ba, hawayen da ya cika idona ya sauko a fuskarta be riga na shi saukowa ba, wata kila shi ma yaji wani banbara gwai ance kar na taba shi abun da ni da shi ba mu saba ba.
she wannan ranar zata zo Zahra, ranar da wani zai mana shamaki
Ban san lokacin dana kurfa a gurin ba na fara kuka, sai ya maida dubansa a gurin cikina.
llah ya raya min abun da zaki haifa min
Har lokacin hawaye yake irin hawayen da ke nuna shi kansa ya yanke kauna daga samun lafiya.

A take Hajiya ta tashi ta fice dakin da sauri tana kuka, ni kuma sai na matsa kusa da shi na kama hannunsa na dora saman cikin na kasa magana sai kuka.

'm sorry soyayyarki da kaunar kasancewa da ke ta saka, na kasa yanke mu'ala da alaka da ke, ina son ki Zahra ina kaunarki sosai, ina kishin ace bayan rayuwata zaki sake auren wani namijin, ina jin kamar zuciyarki ta kasance dan ni ni kadai...

Ya yunkura ya tashi zaune sai ya kasa hakan yasa ni na dago na kama hannunsa na rike dai ya jimke hannun nawa.
i min alkawari Zahra...

Ki daukar min alkawarin da ko da bana raye ba zaki karya shi ba...

Shigowar Mama ce ta katse komai ciki har da furucin da Deen be karasa ba, balle na san wane irin alkawarin da yake son na yi masa, wanda na tabbatar da zan iya masa shi ko da kuwa rai na zai bar jikina.
ahra...

Yayarki na kiranki
Mama ta fada tana kallona ta kalleshi tana kokarin fahimtar abun da yake faruwa, domin har lokacin hannuna yana tsarke cikin nasa.

Sai dai jin furucin Mama ya saka ya zare hannunsa daga nawa ya lumshe ido.
ama zaki iya ba mu minti biyu?

Na tambaya daker saboda kuka.
kwai wata matsala ne?

Baki tunanin mijinki na bukatar hutu?

Da safe ai sai ku karasa maganar
Na saka hannuna na share hawayena na mike tsaye ina jin kamar ba zan iya tafiya ba, zuciyata na raya min kamar idan na tafi zan dawo na tararda gawar Deen ne.

Sai da na kai kofa sai kuma na juyo na kalleshi ni yake kallo fuskarsa na nuna akwai magana a tare da shi, sai dai ban iya komai ba na juya na fita taku daya biyu ana uku sai ga Mama ta fito, sai dai bata ce min komai ba har sai da muka yi nisa da gurin.
i kiyaye abun da likita ya fada kuma ki yi ta addu'a
Na daga mata kai.
mman Mama ina son na yi magana da Deen akwai abun da yake son ya fada min
kan ciwonsa ne?

Ko akanki
an sani ba, ni dai yace na masa alkawari ko bayan ba ransa to be karasa min ba kika shigo ban san mi yake son na masa ba
Tsayawa kallona Mama ta yi sannan ta hade yawu ta ce.
a safe ai sai ku yi magana kinji ko?

Ki tafi kar ki barta tana ta jira ita da mijinta mi zan koma gurin Deen din
Na amsa sannan ya cigaba da tafiyar na barta a nan tsaye kamar mai tunani, ina fitowa na samu Yaya Maryam tana jira ita da mijinta bata ce min komai ba muka fara tafiya sai suka yi gaba suka bar a baya ina ta waigen ward din ina jin kamar na koma gurin mijina.

Ganin hakan ya saka Yaya Maryam ta dawo ta rika ni.
ahra...

Sai na fashe da kuka marar sauti.
allahi ji nake kamar idan na tafi ba zan dawo na tararda Deen ba
abu abun da zai faru da yardar Allah, ki kwantar da hankalinki abun da yafi ma yanzu ki fara tunanin hanyar da zamu bi mu samu kudin aiki
Na daga nata kai ina hawaye sai ta rumgume ni muka nufi inda mijinta ya faka motarsa.

Ba dan raina ya so ba na bi ta gidanta na kwana, ita da mijinta suka yi ta kokarin kwantar min da hankali, haka dai na daure na sha ruwan tea ba dan na ji ina son komai ba, gaba daya tunanina ya tafi akan yadda zan yi na samu kudin aikin Deen.

Cikin kwana uku na bi na lalace na rame kamar ni ce mai ciwon, muna ta fafutukar neman kudin amman hanyoyi sun taushe mana, muka rasa mai siyen gidan sai muka koma neman wanda zamu bawa jingina ya bamu kudi, Yaya Maryam ta siyar da wayarta da kayan dakinta ta damka min kudin, mijinta ma ya taimake mu da abun da zai iya, Hajiya ma ta yi iya nata Baba ma haka sai dai gaba daya kudin da muka hada be wuce miliyan uku da rabi ba, shi ma daker da sudin goshi muka samu muka hada ciki kuwa da da gidan da muka siyar a arha banza saboda muna bukatar kudin, ni ma na siyar da kayan dakina da Mama ta yi min, har na koma bibiyar dangin mahaifina wai ko zan samu a taimaka mana saboda suna da rufin asiri amman sai dai su yi mana alkawari wasu kuma su dauki abun da be taka kara balle ya karya ba su bani, sai dai ba laifi sun yi ta zuwa ganinsa a asibiti daga su har dangin mahaifiyata, ta bangare Hajiya da Baba ma an samu taimako sai dai taimako ba irin wanda muke bukata ba, gashi kudin da muka tara a cikin ake cira ana masa wasu kanann magungunan da scanning.

Gashi na lura ciwon nasa sai kara gaba yake, domin a yanzu kamar ma bata gane wanda ya zo kansa, duk kuma yadda na so na samu damar kebewa na yi magana da shi Mama bata bari ba, idan kuma bata nan Hajiya na nan idan Hajiya bata nan yana bachi, tun daga wacan rana ban samu wata rana da yi wata doguwar magana da shi ba, ko sannu na yi masa sai dai ya daga min kai ko hannu shi ma daker, a haka kuma yake karfin halin yi min murmushi sai kuma yawan kallon cikina da yake.

Kusan yau ita ce rana ta karshe da Likitoci suka tabbatar mana idan har ba mu samu kawo kudin aikin a cikin satin nan ba, zamu iya rasa shi, kuma na lura da haka domin ciwo ya ci shi har ya sauya kamanin, cikin abun da be fi sati biyu zuwa uku ba, Deen ya canja ya koma kwance baya iya komai zai an masa.

Ba tare da sanin kowa ba na silala na fita asibitin zuwa gidan wani dan'uwan mahaifina, domin mutum ne mai rufin asibiti kuma mahaifina ya taimake shi sosai a lokacin da yake raye, ba tare da tunanin komai na shiga gidansa duk da kasancewar na sanar da shi halin da nake ciki a wacan karon yace min zai waiwayeni sai dai shiri gashi yau kusan kwana hudu kenan.

A lokacin da na shiga gidansa matarsa ta tarbeni da far'a kamar yadda ta saba, ta saka aka kawo min abinci da abun sha, ni dai ko ruwan da aka kawo min ban taba ba balle na ci abinci domin ba shi ne gabana ba.

Haka na zauna a falon tun zaman na min dadi har na fara takura na mike tsaye na sake zama, be fito ba da matarsa ta fito na sake mata magana sai tace min ta fada masa yace na jira yana da baki ne, a take zuciyata ta sosu ina tuna lokacin da yake zuwa gurin mahaifina idan ya shigo Abbana na maraba da shi yana girmama shi, mu kuma yana nuna mana so kamar ya cinye mu saboda mahaifinmu yana raye kuma yana da rufin asiri a lokacin, yanzu kuma da ba shi a raye yana da wasu bakin da suka yayan yan'uwanshi kuma amininsa.
Chapter 21 · 0% Book details