← Book details Ciwon So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 134

Sashe 29

Ciwon So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Na furta kamar wanda aka matsi bakinta kalmar ta fito, hankali yayi mugun tashi sai gani ina karawa kafafuwana mai kamar ba mai ciki ba na koma dakin da Deen yake da sauri, sai na samu Bahijja zaune har lokacin tana kuka kawarta na tsaye kanta tana bata hakuri, har kuma lokacin idon Deen a bude suke numfashi kuma yana tafiya a na'urar lura da numfashi, na karasa kusa da shi da sauri ina dubawa.
aba ya zo ya karbi takardar maganin, likitan ma ya sake zuwa ya duba shi amman be ce komai ba
Bahijja ta fada min, sai na kai hannu kamar na rufe masa idon unexpected na ji ya rika hannuna sai na kalli hannu hankali a tashe na sake kallon fuskarsa sai na yi arba da murmushi a fuskarsa sai dai har lokacin idanuwansa ba su nuna alamar yana kallona ba ko kuma ya san ni din ce ko akasin haka.
een...

Na fada da sauri Bahijja ma ta taso tana kallonsa.

Be amsa min ba a take na ji wani sabon kuka ya taso min sai nake ganin kamar bankwana yake min, na saki hannunsa da sauri na fice daga dakin, kai tsaye dakin da likitan yake na nufa sai na samu ba shi a ciki office din ma a kulle yake, na fito da saurina ina tambayar nurse din dazun inda likitan yaje.
na tunanin ya fita
an girman Allah ku kira min shi
a komai ba, ku kura shi ko kuma ku bani number shi akwai abun da zan tambaye shi
amar me?
e shafe ki ba, ki taimaka min dan girman Allah
Sai suka kalli junansu, kamin dayar ta ciro karamar wayarta ta kira shi.
octor Good afternoon wata ke nemanka
Kamar na san zai tambaya yace wacece sai na ce.
i ce masa Zahra ce mai ciki matar Zaharadeen wanda suka yi magana dazun
Ta fada masa kamar yadda na fada, sai ta miko min wayar, kamar mai tunani haka na tsaya kallon wayar sannan na mika hannu na karba na kara wayar a kunne.
afiya kike nema na?

Babu wani abun da zan iya yi ma mijinki a yanzu sai dai mu duba ma sarautar Allah ido
na son magana da kai ne akan maganar dazun
Jin nayi yayi shiru sai kuma yace.
o wacan maganar ta wuce ai, na samu wata
Kamin na ce komai ya yanke wayar, sai na mika mata hawaye na sauko min, na juya jiki a sanyaye na koma inda na fito wato dakin da Deen yake, sai dai wannan karon na samu idonsa a rufe.
e kika rufe masa idon?

Na tambayi Bahijja sai ta ce.

Na matsa ina ta kallon fuskarsa, mafarkin da na yi dazun yana ta dawo min.

'm sorry...

Na furta ina jin wani sabon kuka na taso min.

A kusa da shi na zauna, ni da su muna dakin har Baba ya dawo daga siyen maganin yana shigowa Likitan dazun shi ma ya turo kofar dakin ya shigo, da farko na yi zaton ko gurina ya zo, sai dai ganin ko kallona be yi ba ya karbi alurar da Baba ya siyo yayi ma Deen ya kuma fadi ka'idar bada maganin da abun da za ki masa idan ya farka sai na fahimci ba saboda ni ya zi nan ba.

Har ya gama abun da yake ya fice be kalle ni ba, hakan ya saka na fita daga dakin ba tare da nace da kowa komai ba, salin salin na isa office din ina turawa sai na same shi a bude, da sallama ta na shiga sai ya dago ya kalleni yana magana da wani da nake kyautata zaton shi ma Likita ne.
a aka yi?

Ya tambaya kamar be gane ni ba.
agana nake son yi da kai
kwai abun da nake yi a yanzu, ki dawo anjima
a taimaka min dan girman Allah
Na roka da magiya kamar na fasshe da kuka, mutumen da suke magana ya kalleshi sai kuma ya juyo ya kalleni.
r Sadiq excuse us please
Wanda aka kira da Dr Sadiq ya mike tsaye ba tare da yace komai ba ya fice daga office din sai na karasa kusa da teburinsa, shi kuma ya jingina da kujerar da yake zaune yana lilo.
a akai?

Cike da nauyin baki da hade yawu na furta.
a amince
Sai yayi murmushi irin na iko.
ou late, damar da na baki ta riga ta wuce
Ban san lokacin da na kai kasa ba na hade hannayena ina rokonsa.
a taimaka min da girman Allah, dan Allah ka taimaka bani da wata mafitar bayan wannan
ashi tashi tashi
Ya fada da sauri yana min alama dana tashi tsaye da hannu yana kallo kofa cike da tsoron kar wani ya zo ya tararda da mu a haka.

Ya dauki wata farar takardar yayi rubutu akai ya miko min.
i same ni a wannan addiren yanzu, kuma karki bari kowa ya sani
Na fada ina share hawaye ina jin kamar damuwata ta yaye, na juya da sauri na fita.

Sai da na lake addireshin a cikin jikina sannan na koma dakin na bude jakata ma dauki yan canjin da na san zasu isheni na hau abun hawa, na fito ba tare da na fadawa Bahijja inda zan je ba, daman ban tararda Baba dakin ba.

Ina kusa fita ward din na hango Yaya Maryam da Mama tafe sai na yi saurin canja direction har sai da suka wuce sannan na fito ina ta zuba sauri na fice.

Tafiyar minti arba'in ta kai ni unguwar Zoo road ciki har da fitowa daga cikin asbiti da kuma tsayawa taron abun hawa.

Daidai inda ya fada min na tsaya ko minti uku ba ayi ba wata mota fara mai bakin gilashi ta faka kusa da ni, gilashin motar aka sauke sai na yi arba da likitan alama yayi min da na shigo, sai na shiga cikin motar.
ahra har a zuciyarki kin shirya yin wannan abun
Na daga masa kai.
sakani da Allah ba wai zan yi dan na cuce ki ba, kuma bana son ya zama kamar na cilasta ki
a shirya
mman miyasa yanzu kika yarda a rana daya bayan dazun da na miki magana baki aminta ba?
aboda na ceci rayuwar mijina bana da wata mafita bayan wannan, idan ya rayu zamu samu wasu yayan, idan kuma na rasa shi na rasa shi kenan fa har a bada
Tare da hawaye na karasa maganar, sai na ji ya sauke ajiyar zuciya.
i da ke duka taimakon juna zamu yi, so yanzu zan kaiki gurin matar, amman ina son idan mun tafi ki nuna mata cewar mun kare magana da ke, ni na fada mata kudin da zata bada kin ga idan mun gama komai cikin lokaci sai a shiga aikin da shi
a a iya gama komai a yau ayi masa aikin a yau?
a sai dai ayi gama komai a yau, inya so gobe sai a shiga aikin da shi, domin ba ni kadai zan yi aikin ba, kuma dole sai an shirya amman zamu iya saka kudin aikin a yau, sannan wannan kuka da kike kar ki kuskura ki yi shi a gabanta, kuma daga yanzu har zuwa lokacin da zaki haihu karki sake tuntubar wani Likita sai ni
Na daga masa kai ina kokarin ganin na tsayar da hawayen tun a yanzu.

Gorar ruwa ya dauko ya miko min sai na karba na sha, sannan ya tashi motar, cikon Allah da karfin hali sai idanuwa suka washe kamar ban taba kuka ba, sai dai idona ya kumbura saboda kukan da na yi a dazun, amman hawayen ya tsaya min.

Ba mu yi wata tafiya mai isa ba muka iso gaban wani gida mai kyau, sai ya ciro wayarsa ya kira wanda nake kyautata zaton namiji ne saboda yanayin maganarsa.
arrister gamu kofar gidan
Sai kuma na ga ya kashe ya sake kiran wata number.
in iso?

Ya furta sannan ya sauke wayar ya hanna horn aka bude masa, ya shiga ciki, kusa da wata motar ya faka ya bude ya fita.

Na bude na fita kamar yadda ya bukata na zagaya na bi bayansa domin tuni ya nufi wata karamar kofa dake can nisa da inda ya aje motarsa.

Yana gaba ina biye sai a lokacin tsoro ya fara kamani idan wani abun zai min, hakan yasa na ja na tsaya sai da be lura ba har sai da ya kai bakin kofar shiga.
afiya?

Ya dawo kusa da ni yana sake tambaya sai na ce.
llah yasa ba cutar da ni zaka yi ba
allahi ba zan cutar da ke ba Zahra, wannan abun ma idan baki aminta ba ba zan yi ba, idan kuma kin canja shawara ne zamu iya komawa
Na girgiza masa kai sai dai kamin na furta komai na hango wani mutum ya fito daga dakin da Dr ya nufa dazun.
r Hamid Bismillah ku karaso mana
A tare muka rika takawa har muka isa gurin, Dr Hamid din ne ya bude min kofa na shiga sannan suka shigo, tun kamin su ce na zauna na zauna sai muka gaisa da wanda nake zaton shi ne Barrister sannan na koro min da bayanin abun da zayi ya kuma tambayi ko da amincewa za ayi ko kuma cilasta min aka yi, na amsa masa cewar ni nayi ra'ayi da kaina, sai ya tambaye ni cikin yana da uba ko shege.
an sunna ne
Na amsa ina jin wani abu har cikin raina sai dai babu damar hawaye domin Dr Hamid ya gargade ne tun kamin mu shigo.
mman miyasa zaki siyar da dan cikinki?

A wannan gabar Dr Hamid ne yayi masa bayani da kansa, sai ya jinjina kai alamar gamsuwa sannan dauki wata jaka dake kusa da shi ya bude ya dauko takardu ya fara rubutu akai, yana tsaka da rubutu sai ga matar ta shigo da katon cikinta da sallamarta.

Da na kalleta da kyau sai na ga suna kama sosai da Dr Hamid din kamar yan'uwa.

Kusa da ni ta zauna fuskarta da murmushi kana ganinta ka san matar manya ce kuma yar manyan mutane, domin fatar jikinta da suturarta sun nuna haka.
Chapter 29 · 0% Book details