← Book details Ciwon So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 134

Sashe 44

Ciwon So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mun kusa awa daya a gurin sannan motarmu ta daga zuwa Kano, muka isa cikin lokaci ina fita motar sai gabana ya soma faduwa, sai na fito bakin tashar motar sannan na tari napep na hau na fada masa inda zai kai ni, kamin mu isa ina ta saka yadda zan fara yi ma Mama bayani amman na rasa mafita, domin har yanzu ban san me zan rika na yi amfani da shi a matsayin dalilina na guduwa ba, haka dai na fito Napep din ina jin kamar ace zan gudun ba, domin abun zai zame min matsala ne a yanzu, dari biyu na bashi sannan na juya ina tafiya kamar wanda bata son takawa na nufi kofar gidanmu, na kusan minti hudu a tsaye sannan na aga kafata na shiga cikin gidan cike da nauyin baki, ban san ta inda zan fara sallama ba.

Kamar rai ya ga mutuwa haka na ji lokacin da na yi arba da Mama a zaune tana gyaran wake, sai ta dago ta kalli kofar domin ganin wanda ya shigo muna yin ido hudu sai annurin fuskarta ya canja ya maida kanta gurin gyaran wanken da take ta cigaba ba tare da ta ce da ni komai ba.

Ni kuwa na yi tsaye a gurin kamar an dasani na san halin Mama idan ta yi fushi bata da kyau ba kasafai take saukowa da wuri ba.

Na cira kafata na fara takawa sai ta dakatar da ni.
saya nan karki karaso nan, me zaki zo ki min?
i yi hakuri Mama dan Allah
Na furta hawaye na sauko min muryata kamar mai koyon magana.
in san da hakuri kika tsallake kika bar dakinki zuwa wata uwa duniya?

A tunaninki idan kin gudu mutuwa zan yi?

Na rasa uwa ban mutu ba, na rasa uba ban mutu ba, na rasa mahaifinku tun kuna kanana na rayu da ku babu taimakon kowa sai Allah kuma ban mutu ba, sai dan kin gudu ke kaidai zai saka na fadi na mutu?

To na yafe ki kije duk uwa duniyar da zaki je, abun magana ne daman kin ja ma kanki kina takaba kin gudu an rasa inda kika yi
Na saki jakar hannuna ban damu da cikina ba na durkusa kasa na hade hannayena ina kuka.
ama dan Allah ki yafe min ban yi haka dan na bata miki rai ba, Mama baki san abun da ya saka na gudu ba...
a sani, Maryam ta fada min komai tashi ki fita...

Ta amsa min tana mikewa tsaye ta nuna min kofa.
ama dan Allah....
i fita na ce karki bari na maimaita kalmar nan a karo na uku Zahra...!

Na tashi tsaye da sauri domin har yanzu ban daina tsoron dukan da Mama take min lokacin da ina budurwa ba idan ta fara bata min da sauki sai an kawo min agaji.
i tafi duk inda zuciyarki ta raya miki ki gani ni mutuwa zan yi
Na dauki jakata ina hawaye na fice daga gidan Na duka na sauka wasu irin hawaye masu zafi suna sauko min.
ama na tafi?

Na tambaya ina jin kamar tace min aa Zahra dawo ki zauna.
o har sai na fada miki?

Kin manta halina wai?

Na juya na fara tafiya kamar bana son fita na bar gidan, kamin na isa titi ma wata uwa da ga duniya ce, haka na sake tare wani mai daidaita na shiga ya maida ni gidana, na saka makullin na bude na shiga ciki ina ganinsa kamar kangon gida, tsaye na ji a tsakar gidan bayan na tura na kara kofar ban rufe ba, ina kallon kofar falona, ji nake kamar na bude baki na ce Deen na dawo ya amsa min, ji nake kamar ya fito ya rumgume ni yana murna da ganina, amman babu hali saboda babu shi a tsaye.

Na karasa na bude falon na shiga na zauna sai na rasa ta ina zan fara kuka, ina zaune har aka kira zahar na tashi na yi alwala na yi sallah na yi ta ambaton Allah har wata sallah ta tararda ni, na gabatar da ita na kwanta a gurin ina jin yadda yunwa ke neman dauki a cikina.

Tashi na yi na bude jakar da tufafinsa suke ciki na fiddo wani fari yadi nasa da yake yawan sakawa ranar jumma'a na dauki filona dake kan katifa na saka masa rigar na kwantar da fito sai na dora kaina ina ta jin kamshin jikinsa, halshen dake cikin bakina har rawa yake saboda kukan da nake jikina na amsawa ta ko'ina.

A rayuwa babu bakincikin da ya kai na miji ya tafi ya bar matarsa tana begensa, abun nan yana da matukar zafi da ciwo, ka tuna cewar ba zaka kira mutun ya amsa maka ba ba zai san halin da kake ciki ba, kuma ba zai taba dawowa ba sai dai taka zuciyar tai ta begensa.
afiyarka ce ta haddasa komai Mijina, mutuwar ta yaye farincikina ta gusar da hasken da yake zuciyata, ina ma ina ina ma ka dawo Deen ga Zahra na ta begenka
Na karasa ina fashewa da wani irin kuka mai taba zuciya da dan kuzarin da ya rage min, ina cikin wannan hali wutar unguwar ta dauke gaba daya.

Can na ji an turo kofar gidan ana haska ko'ina da fitila mai haske.
allamu Alaikum
Wata murya da nake jin kamar na sani tana ta doko sallama, sai dai ba ni da kuzarin amsawa sai na kuka, har cikin falo aka shigo wannan karon sunana ake kira sai na gane mai muryar tun kan ta karaso cikin dakina.
ahra...

Ta haska ni da fitila bana iya komai sai kuka.
ubhanallahi
Ta furta tana karaso kusa da ni da sauri.
iya faru kika zauna ke kadai kuma cikin hudu babu ko haske
Na mika mata hannuna sai ta miko min sannan nata ta tashe ni zaune ta haske fuskata da kyau, sai ta yi saurin aje wayarta akan tafitar ta rumgume ni.
a gode da kika zo Anty Zainab, na gode...

Na furta cikin wani irin kuka ina kankanmeta...
*Allah yasa ba ni kadai Zahra ta tabawa zuciya a yau ba*
10/9/22, 22:47 - Buhainat: *Littafin nan na kudi ne, karanta na sata daukarwa kanki hakki ne, domin sauke nauyi biya ki karanta cikin aminci, pay 500 to Zenith Bank Hadiza Abubakar 2451879008 and send the evidence of payment to 08036126660*
Kuka na yi sosai a kafadarta sannan ta dago ni ita ma idonta na zubar da hawaye ta ce.
iya same ki Zahra?

Miya kike wannan kuka haka?

Na yi shiru domin ban san me zan fada mata ba.
ina zaune ke kadai acikin duhu daman ke kadai kike kwana a gidan?

Na girgiza mata kai.
uduwa na yi sai yau na dawo, kuma Mama ta ki ta karbe ni
mman miyasa kika gudu?

Na kalleta kamar na fada mata sai kuma na ga fadin ba shi da amfani saboda ba zata sama min mafita ba, kuma dan'uwanta ma ba zai min ba domin be taimake ni a lokacin da nake bukatar taimakon ba balle yanzu, kuma fada mata zai kara bayyana sirrin dake rufe ne, a tonawa kaina da ita kanta Jamila asiri.
abu komai
abu komai zaki gudu?

Look Zahra na san kina jin haushina ni da dan'uwana amman wannan matsalar da kike ciki ba abu ne da ya shafe ni ko ya shafe shi ba, ki kawar da komai a ranki ki fada min damuwarki wata kila zamu iya samun mafita?

Na girgiza mata kai.
a komai, me kika zo yi nan?

Ta yi murmushi ta kai hannu ta shafa fuskata.
a komai na zo na duba lafiyar Kanwata ne kawai zan je gurin aiki sai kuma na tsaya ta nan na dubaki
Na sauke kaina kasa.
anzu fada min kina son Mama ta dawo ta zauna ne ko kuwa kina son ki koma gurinta ne da zama?
an koma gidanta
o taso muje
ace ba zan zauna ba, fushi take ni
an mata magana kuma zata ji i promise
Na sauko saman katifar na dauki hijab dina na saka na dauki makullin gidan, a tare muka fito ita ta rufe min gidan ta saka ni gaba har gurin motarta ta bude min gaba na shiga na zauna sannan ta zagaya ta shiga ta tashi motar, har muka isa gidan Mama hawaye na ke ga idona ciwo yake saboda kukan da na yi, ko da muka doshi kofar gidan sai na tsaya daga baya tana ganin haka sai ta riko hannuna ta wuce gaba sai da ta yi sallama aka amsa mata sannan ta shiga cikin gidan.

Mama ta fito daga daki tana kallonta da ni kamin ta ce.
annu da zuwa
ama ina wuni?
afiya kalau
Ta amsa da muryar da ke nuna har yanzu bata sauka daga fushin ba.
ama zamu iya zama?

Anty Zainab ta fada sannan Mama ta dauko tabarmar dake jingine ta shimfida mata muka zauna kaina na kasa.
ama na taso zan je gurin aiki sai na tsaya ta gidan Zahra da zimmar na duba halin da take ciki, sai na same ta tana zaune ita kadai a dakina tana ta kuka idonta har ya kumbura, ga hudu babu wuta a gidan na tambaye ta abun da ya faru bata fada min ba, sai tace kin ce ba zata zauna a gidanki ba haka ne?

Mama ta kalleni sannan ta amsa mata.
aka ne
an san girman laifin da Zahra ta aikata miki ba, amman a yanzu Zahra bata da wani gata sai na ki bata da wanda zai tsaya mata sai ke, tun da mijinta baya raye mahaifinta ma baya raye duka duka yaushe Deen ya rasu?

Bata gama fita daga jin zafin rashin mijinta ba sai kuma ace ta fuskanci wata damuwa daga gareki?

Ke fa uwace Mama kuma kin san yadda mace take ji idan ta rasa miji domin ke ma kin rasa mahaifinta, idan kika ce Zahra ba zata zauna tare da ke ba gurin waye kike son ta je ta zauna?
Chapter 44 · 0% Book details