← Book details Ciwon So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 134

Sashe 24

Ciwon So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da ace hawaye za su iya taruwa kamar ruwa mai yinsu yayi iyo a cikin, tabbas da hawayen da na zubar a yawan sun isa na yi iyo a cikin, da ace wani zai fada min ranar yau zata zo da zan yi kuka kamar na mutu ba zan yarda, ashe wacan kukam da na yi ranar da aka fasa aurena da Abiey sharar fage ne, yanzu ne kukan na gaske yake zuwa, a inda nake kuka babu kowa sai ni kadai da duniyata, babu wanda zai ce Zahra yi hakuri balle ya karfafa min guiwa, babu wanda zai min albishir cewar Deen ba zai mutu ba, ya gobena zata kasance idan na rasa mijina?

Waye zai nuna min soyayya ta gaskiya da kaunar kamar mijina?

Da wa zuciyata zata shaku kamar mijina?
uka ba zai miki maganin komai ba Zahra
Wata murya mai kama da ta Hajiya ta fada min a bayana, sai na juyo a hankali domin na tabbatar Hajiya ce ko kuma kunnuwa ne suka fara min yaye yaye.

Ganin Hajiya yasa na mike tsaye gaba daya ina kallonta fuskata har ta gama kumbura.
a kuka zai magance matsala da wanda kika a matsayinki na matarsa da wanda na yi a matsayina na mahaifiyarsa ya isa ya saka komai ya gyaru, amman kuka baya maganin komai
Sai tausayinta ya kamani domin ita ma kukan take.

Matsawo ta yi kusa da ni.
a sani, kin sani Abiey, kuma Deen ya tsane shi, amman a yanzu ba mu da wata mafita sai ta shi
Na mata kallon rashin fahimta.
an gane ba?
biey ne kawai zai iya taimaka mana mu ceto rayuwar Deen, Abiey yana da kudi Zahra kuma zai iya taimaka mana saboda ke
Na yi saurin matsawa baya cike da mamaki da kuma tsoro a lokaci daya.
biey fa kika ce Hajiya, kin san yadda na sani Abiey kuwa?

Kin san yadda Deen zai ji idan ya san kin yi wannan maganar?

Kin fi kowa sanin abun da Abiey yayi min
a saboda kowa zaki yi ba Zahra, saboda mijinki idan ba haka ba kina ji kina gani zamu rasa shi, karki tunanin abun da Abiey yayi miki a yanzu, ko kuma abun da Deen zai ji, rayuwarsa muke bukata
Na girgiza mata kai.
a zan iya ba
Sai ta fadi kasa ta rike hannayena tana wani irin kuka da ban taba ganin tana yi ba.
i taimaka min dan girman Allah, daga Deen sai Bahijja na haifa bayan su ba ni da kowa Zahra, ki taimaka kar na rasa dana, Zahra ki tuna irin son da Deen yake miki wane irin hali ne ba zai shiga ba saboda ya faranta miki?

Deen zai iya jefa kansa ko wane irin hali saboda ke Zahra, ki taimaka ki ceto rayuwar
Tana fadar hakan sai na ji an yaye min duk wani abu da nake da zai hana ko tare ni daga zuwa gurin Abiey, Tabbas Deen zai yi abun da ya fi wannan ma saboda ya faranta min balle kuma ace na rasa lafiyata.
a miki alkawari Deen ba zai tana sani ba, wannan a tsakaninmu ne, ko mahaifiyarki ba zata ji ba
Na daga mata kai cikin kuka, sai ta mike tsaye ta rumgume ni tana kuka tana fadin.
ole ce ta saka Zahra dole ce
Gaba daya sai na jikina ya kara yin sanyi kuzarin kukan ya cire min, sai dai hawayen ba su daina zuba ba.

Mun dade a haka sannan ta sake ni fuskarta har ta kumbura, tabbas ko ban akan kowa ba zan yi akan Hajiya domin bata taba nuna min tsana ba ko ta rana daya, a lokacin da nake zuwa gidanta har hana Bahijja take abu ni ta bani ko ta yi min saboda tana so na.
na Mama
Na tambaya muryata a dakishe kana ji kasan na sha kuka har na gode Allah.
un tafi gida tare da Maryam, saboda Maryam ta roka miki cewar kina son ki kwana a nan ni ma kuma na saka baki sai ta amince
aya fada miki ina nan?
abu nima zuwa na yi na samu guri na yi kuka sai na tarar ke ma kukan kike
Na sauke ajiyar zuciya na share hawayena.
anzu nake da damar zuwa, saboda Mama da Yaya Maryam basa nan
Ta daga min kai da sauri, ni kaina ji nake kamar ba zan iya kara bata lokaci ba, amman taya zan tunkari Abiey?

Anya ya cancanci na kalleshi ma?

Abiey ya cancanci jin furucina?

Balle har na je neman alfarma a gurinsa?

Kamar Hajiya tasan abun da nake sakawa a zuciya sai tace.
aboda Mijinki zaki yi Zahra
Na sake sauke numfashi sannan na ce.
ari naje na dauki jakata
A tare muka jero duk wanda zai kalli fuskata ko ya kalli Hajiya ya san ni da ita mun sha kuka, ni na fara shiga dakin na karasa kusa da Deen ina kallon fuskarsa hawaye ya sake cika idona, lallai dan a'adan ba abakin komai yake ba, yadda yake nishadi da walwala na ke hangowa yau kuma gashi kwance kamar gawa yana neman dauki.

A dakin na samu jakata da alama Hajiya ta kawo min ita a nan domin ni a waje na bar ta gurin da muka zauna da su Mama dazun, jakar na nufa na dauka ya juyo ya kalli Hajiya sai ta daga min kai cikin siffar tausayi da damuwa ni kuma na sauke kai na fara takawa kadan kadan har na fice, kamin na isa gate din na samu abun hawa ma aiki ba, ba dan ina jin wahalar tafiyar ba, sai dan nauyi yadda zan tunkari gidansu Abiey na nan ma ko baya nan?

Ba kasafai yake zama kasar ba, kasancewar dan kwallo, kuma ko yana nan be zama lallai ace yana gidan Ammy ba wata kila yana gidan Mai Martaba gurin Anty ko wani gurin, duk kuwa da kasancewar ya fi zama a gurin Ammy.

Ki tafi ko dan saboda Deen, ba dan ke ba, saboda shi da mahaifiyarsa.

Aa karki tafi mutum da ya watsa miki kasa a idon duniya zaki je neman taimakonsa?

Wanda ya guje a ranar da aka taru da sunan daurin aurenki?

Anya ma idan na je zai saurare ni?

Ya cancanci na roki alfarma a gurinsa?

Haka dai zuciyata ta yi ta raba min dayan biyu na rasa na dauka a tsakanin tafiyar da kuma fasa zuwan.

Daker na samu na yaki fushi na kawar da komai na tari napep na shiga, domin gaskiya Hajita ta fada idan ni ce a wannan halin Deen zai aikata fiye da haka domin ya ceto rayuwata, shin bana masa alkawarin zamu samu kudin ba?

Mi zai hana na cika masa alwarinsa?

Kamar na shigo wata sabuwar duniyar haka na ji a lokacin da dan sahu ya shiga unguwarsu Abiey, kusan ko a mafarki na dade ban bi ta hanyar ba balle kuma a zahiri balle kuma yanzu da gidansu zan nufa kai tsaye, cikin wani irin yanayi da shi bana tsoro ba ba kuma na fargaba ya sauke ni a kofar gidan ta futulu suka haske kamar rana.

Dari biyu na ciro na mika masa sannan na juya na nufi gate din, sai kuma na samu kaina da tsayuwa ina kallon gate din kamar matacciyar gawa, sau biyar ina kai hannu da zimmar na kwankwasa kofar sai na kasa daga karshe wata zuciyar tace min na juya na koma kar na aikata abun da nake da niya.

Haka kuwa aika yi sai na juya na fara sauri da zimmar barin gurin.
ahra ba zaki iya ba, wannan ce kadai damarki ta karshe kuma damar da zaki iya ceton Deen
Wata zuciyar da nake kyautata zaton sahibar zuciyace mai son Deen ta tunatar da ni abun da nake kokarin mantawa.

Sai kuma na juyo na dawo na kai hannu na kwankwasa gate din, kamar mai gadin gate din jira yake na kwankwasa sai gashi ya bude da kuzarinsa bayan ya leko ta karamar kofar ya ga mai buga gate din.
a nake gani kamar Zahra...

Almu ya fada yana kara tantance ni, domin ya san ni farin sani ni ma kuma na san shi a lokacin da gidan yake min dadin zuwa.
i ce ina wuni
llahu Akbar, Zahra rai kan ga rai?
mmy tana ciki?

Na tambaya Ammy amaimakon Abiey, domin damuwata ba zata bar ni na iya tsayawa amsa masa ba.
mmy ta fita tun rana, amman Abiey yana cikin gidan Yasmin ma tana ciki
aushe zata dawo
Na tambaya numfashina na rawa jin ya ambaci Abiey.
oh Wallahi ban sani ba, amman dai tun rana ta fita, ba zaki shiga ciki ba
Ya fada yana kallon yanayi domin ya fahimci akwai damuwa a tare da ni.
a dai zaka taimaka ka tambaya min yaushe zata dawo sai na jirata
oh Zahra kin san manyan nan ba son takura suke ba, ni ban aiketa ba zan ce yaushe zata dawo?

Sai dai ko nace ke kika tambaya?

Na daga masa kai zuciyata na bugawa fiye da kima.
oh shigo ciki mana kika tsaya kamar bakuwa
Na kusan second ashiri ina deciding tsakanin shiga da kuma tsayawa, kamin na mika kafa na shiga cikin gidan har lokacin wani bangaren fada min yake be dace na aikata haka ba.

Dakin mai gadi ya nufa daman a iya sanina a can telephone take idan za a kira cikin gidan, sai dai masu gadin da masu aikin da na gani suka baki ne ba wadanda na sani ba.

Ya dan jima a ciki sannan ya fito yana sanar da ni cewar ba a dauki wayar ba.
a dai kin daure kin shiga ciki inya so sai ki jirata
Da gangan na ki na musa masa domin ba a gurin Ammy na zo ba a gurin Abiey.

Ban ce masa komai ba na fara takawa zuwa inda main door din take, katon gidan yana nan da kyaunsa da ado kamar yadda na sanshi, sai dau an sabunta fenti kamar yadda aka saba duk bayan wata biyar.
Chapter 24 · 0% Book details