← Book details Ciwon So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 105 OF 134

Sashe 105

Ciwon So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A gurin da na fi samun abun dadi na nufa kamin ina isa kofar gate din gidan motar Abiey na isowa kofar gidan ni da masu gadi har rigen bude masa kofar muke, bayan na shiga ciki sai na saki kofar na karasa gurin motar da ya fito yana murmushi tare da wani sarauyin da ba zai wuce sa'arsa ba, nuna ni saurayin da nake kyautata zaton abokinsa ne ya yi.
ar dai ita ce wanda kake ba ni labari
ta ce fa
Na dan matsa baya ina kallonsu domin ban fahimci abun da suke magana a kai ba.
mman ba ta yi kama da wadanda za su aikata wani abun shirme ko kiriniya ba
'm telling you, Zahra mu shiga ciki ko
Abiey ya karasa yana nuna kofar dakin, sai na yi murmushi na wuce gaba domin gidan ba bakona ba ne, suka biyo bayana ni na fara shiga falon na zauna sannan Abiey ya haura sama abokinsa kuma ya zauna akan kujera yana kallona sai na ji kunya ta kamani.
mmy amman baki fada min ba ba, ba zan dawo yanzu ba, ga Zahra ma ra zo, Okay
Shi ne abun da Abiey ya sauko yana fada da waya a kunnensa kamin ya kalli abokinsa.
mmy ta fita kuma yunwa nake ji Wallahi
na mai aikinku
a yi tafiya, kuma ko tana nan kasan bana cin abincin masu aiki
i kai yunwarka ma mai sauki ce da ka sha tea zaka iya cewa ka koshi, amman ni idan ban ci abinci mai nauyi ba ba zan gane kan garin ba
Abiey ya kalli.
ahra zaki girkawa Abokina Sauban indomie?

Kin iya ai ko?

Na yi kuri da ido kamar marar gaskiya, can kuma na daga kai.
h na iya
a kitchen can
Ya nuna min hanyar kitchen din, sai na aje jakar hannuna na mike tsaye na nufi kitchen, kusan a tare muka shiga ya dauko min abubuwan da zan yi amfani da su, sannan ya shiga dorawa kansa ruwan tea yana zolayata.
yakkyawa ranar kika ja mana zuma kika gudu ko?

Na balle ni a baya da kai sosai fa Ammy kuma kin taimaka mata har tana cewa ashe zata iya gudu idan wani abun ya taso
Na yi dariyar da na tabbatar kara min kyau ta yi domin har wani wara ido yayi yana fadin.
ow Gaskiya Allah yayi hallita a gurin nan
Na rufe fuskata da sauri ina dariya.
ari na baki damarki kar na rudaki, idan ruwan tea nawa ya tafasa sai ki kirani
oh, amman karka dawo kitchen din sai idan na kira ka
es Ma'am
Ya juya ya fice cike da girmamawa, a nan na takarkare na cire hijabina na aje gefe daya na dora pot din da ya nuna min na zuba mai na fara gabatar da aiki, tarugu da albasa da ya nuna min na daka mai uban yawa na zuba a ciki, ina kallon ruwan ya gama tafasa har ya kashe kansa amman na ki yarda ma fada saboda ban gama girkin ba bana son ya shigo ya tararda ni a haka, na zuba gurinshi da magi a tare na zuba komai na saka indomie na ja na tsaya, ban yi minti biyu da rufe tukunyar ba na bude na saka abu na motsa miyar na lasa, wani tsabar azabar yajin da na ji ban san lokacin da na daka tsalle ba na wurgar da spoon din dake hannuna ko ni da nake mayya bana tunanin zan iya cin wannan abinci.

Kofar kitchen din ta falon na rufe na dauki hijab dina na saka na bude kofar baya na fice da gudu, kamar aljana haka na isa gida ina haki, Mama da Yaya Maryam suna zaune a inda na barsu zaune suna ta hira har lokacin.
e lafiya wani barakar kika yi kuma?

Mama ta tambaya Yaya Maryam kam sai barkewa ta yi da dariya.
ahra ashe haka kika yi da Baba?

Gaskiya dole ki sha duka hannun Deen kam
Ni kam ban bi ta kanta ba domin na san barakar da na tafka a yanzu ta ci uban dariyar da Yaya Maryam take.
ama wai Antyn su Hafsat tace na tambayeki me ake sakawa a abinci idan yayi yaji sosai
nya?

Ko dai wani abun kika yi?
a Mama cewa fa ta yi na tambaye ki, Islamiya ma zamu wuce yanzu da Hafsat
o ni Wallahi ban sani ba
na saka gawayi, ance yana rage yajin amman dai ban taba gwada yi ba
Yaya Maryam na bada amsar na mika hannu na saci dan kullin maganin da Mama tace na maza ne, na fice da sauri, sai da na bi ta gidansu Hafsat na samu gawayi domin na san ba za a samu gawayi a gidan Ammy ba su da suke amfani da gas me zai hada su da hawayi, kamar wanda ta yi sata haka na dawo cikin gidan na samu kofar a bude kamar yadda na barta, ban ko tsaya wanke gawayin ba na jefa shi haka a cikin indomie sannan na dauko soyayen naman da ya bani na saka na sake motsa taliyar yaran.

A kokarin ganin na burge Abiey na bude kofin ruwan zafin na kwance maganin na zuba masa maganin na kwayar dai sai da na murje na ganyen kuma a haka na zuba masa shi, na sake kunna hitar ta sake tafasawa da yayi na zube na tace masa na dauki cup biyu na zuba dora a tray na bude kofar na fito kai tsaye na nufi dinning na dauki kalolin lipton na saka na saka suga kadan na zuba kayan kamshin da na gani sannan na nufo inda suke zaune na risina na aje musu.
h Zahra sannu da kokari ai da kin bar shi kin kira ni kawai na hada
Abun da baka saba ba, jikina har rawa yake na yi musu hidimar, Sauban ma sai yawa yake da kokarina yana tambayar taliyarsa bata yi ba.
a kusa yanzu zan kawo
a naga abun yayi dark green?

Abiey ya tambaya sai na ce.
a hada kalolin liptons ne maybe shiyasa
kay thank you duk da dai ba ko wane kalar Lipton nake sha ba
Ina jin lokacin da Sauban din yake ce masa.
ar dai ka gasale ta ka daure kawai ka sha
Ni dai ban bi ta kansu ba na dawo kitchen din na cigaba da kula da indomie da ruwan cikin ma yayi mata yawa kuma yajin be rage ba sai ma baki da abincin ya dan yi wani bangare, sai na na sauke tukunyar na tsame rabin naman ciki na wanke a ruwa na cinye, sannan na rage ruwan dahuwar indomie na zuba magudanar ruwa da na gani a kitchen din na dauko plate na zuba musu na saka spoon biyu, na bude kofar kitchen din na fito sai na samu Abiey a tsaye yana ta wani abu mai kama da shillo yana kallon sama, Sauban kuma yana zaune a kasa da rabin kofin tea ya dafe kai, Abiey kam gaba daya ya shanye.

A gaban Sauban na aje plate din indomie.
ashi nan
Sauban ya dago daker ya kalleni sai kuma ya kalli indomie.
e kika saka a shayin nan?
an saka komai ba
Na amsa ina dan natsawa baya cike da tsoro.
iyasa nake juyawa?

Miyasa komai yake juyawa?
unwa ce ka ci abincin gashi nan na dafa maka
Kitchen din na koma na dauko wani plate ina fifita nasa saboda abincib ya sha iska, har lokacin Abiey na tsaye sai gidaya yake da hannu.
a ci ta sha iska
Kamar mai jiran umarnina sai ya bude kafafuwa ya fara auna abinci soma daya ya daki kansa ya tande baki.
ai mutuwa....

Minenen wannan kuma
Ya sake aika cibi na biyu, ni dai ina ta kallonsa ina jinjina kokarinsa har ya cinye rabin plate wata kila dai saboda yana jin yunwa ne, sai dai ina ganin wani abu mai kama da fitar hayyaci a tare da su, musamman Abiey da ya gagara zama sai kallon sama yake kamin na koma kallon cushion din gidan.

Tashi na yi na isa gabansa na tsaya ina kallonsa.
biey Lafiya?
na fa lafiya?

Baki ne duk sun cika mana gida, ga su nan zai shigowa suke
Na juya gabas da yamma kudu da arewa ban ga kowa ba, amman Abiey sai sannu da zuwa yake musu sai kuma ya dafe kansa yana lumshe ido.
a salam, wadannan bakin da muke biki ake ne?

Na waiga na kalli Sauban dake ta shan yaji yana son mikewa, amman ya kasa sai juya kai yake yana wani zazzago halshe kamar maye.

Zuciyata bata raya min cewar abun da na zuba musu a tea ne ya saka su wannan abun ba, domin Mama ta fada min cewar maganin maza ne, ba na maye ba wata kila dai lokacin na shiga Kitchen wasu aljannu suka shigo cikin gidan suka shafe su, musamnan ma Abiey da baya cikin hayyacinsa gaba daya.

A dole na rika shi ina kokarin zaunarwa ya ki ya zauna sai cewa yake wai bana ganin falon ya cika da jama'a, sai ya fara safa da marwa cikin falon kamar mai rafeti.

Tsaye na yi cikin falon ina kallon ikon Allah, Sauban ya zama kamar dan maye yana ta aikin shan yaji yana shafa jikinsa da kansa, ban san lokacin da na fashe da kuka ba na nufi jakata na dauka na rumgume.
i dai na shiga uku ban san kuma abun da ya faru ba, miyasa suke yin layi?
Chapter 105 · 0% Book details