← Book details Ciwon So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 134

Sashe 2

Ciwon So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya kalleta yana murmushi tare da kai hannu ya rika hannunta.
an taba ganin wata kanwa mai son yayanta wanda suka hada uba daya ba kamar yarda tawa kanwar take so na, ban tana ganin matar uba mai son dan mijinta ba, kamar yadda Anty take so na
Murmushi tai ta kwantar da kanta kafardarsa cike da kanwar dan'uwanta, ko da rana daya bata taba daukar Abiey uba kadai suka hada ba, tana masa wani irin so da take jin kamar Anty Amarya ce ta haife shi.
anzu dai ka tashi ka karya, sai ka tafi gurin Sauban na san yanzu yana can yana ta jira
Tana rufe baki wayar Abiey dake vibration ta fara ruri alamar kira, da sauri ta tashi ta nufi wayar ta dauka.
auban ne...

Abiey ya fada yana nufar inda ta aje masa breakfast din.
ello Ango
Ta fada bayan ta daga kiran ta kai wayar kunnenta.
i fadawa yayanki ya kyauta
ashi nan zuwa Ango, breakfast yake yi
et him talk
won't...

Ta katse wayar.

Abiey ya juyo rike da mug ya kalleta.
a katse
Ta karasa kusa da shi ta mika masa wayar, sai ya karba ya saka aljihu ya mika mata mug din, ya nufi gurin da jerin turarunkansa suke ya dauko wani expensive perfume ya fesa sannan ya juyo ya dauki babbar rigarsa ya saka Aisha ta yi saurin daukar hular data gani aje ta mika masa, sai ya karba ya saka.
ow Maa Shaa Allah, Tsarki ya tabbata ga Ubangijina da ya hallinci wannan kyakkyawar sura
Murmushi ya yi, shi kansa ya san zai yi ma kayan kyau, domin be yarda tufafin za su masa kyau ba, sai dai shi yayi musu kyau, domin da zai shiga gasar kyau ta mazan duniya babu abun da zai hana shi yin na biyu Shi ma kuma idan be ci na daya ba.

A hankali yake gyara daidatuwar tsayuwar agogon hannunsa na miliyan biyu da rabi.
ar ki cewa Anty ban ci komai ba, ki zauna a nan ki cinye komai sai ki ce mata ni na cinye
mman ni ai na ci nawa
elp a brother please..

Ta daga masa kai dan dole ba dan ta so ba.

Murmushi yayi yana tuna ya taba saka Zahra yin haka sai dai ita bata rufa masa asiri ba, sai da ta fadawa Ammy bayan ta cinye komai.

Ajiyar zuciya ya sauke ya nufi kofar dakin ya bude ya fita yana murmushin dake kara masa kyau, haiba da kwarjini.
ow Maa Shaa Allah
Anty ta fada tana kallon yadda yake saukowa kamar wani ango.
arjis je ki dauko min key motana
Ya fada yana karasa saukowa, Narjis ta mike tsaye da sauri tana yaba yayanta ta nufi upstairs din da ya sauko.
amin ka fita ka fara zuwa bangaren Mai Martaba ka gaishe shi
o yanzu sauri nake ba zan iya zuwa ba
aba Abiey wai sai yaushe za ku fahimci juna ne kai da mahaifinka?

Sai yaushe?

Ya daga kafadunsa yana kokarin ganin bata baahi laifi ba.
don't know, ba rana ba wata ba shekara, Anty kin sani he don't love me, he hate me and...

I...
nd you hate him too
Anty ta karasa masa kalmar daya rike ya kasa karasawa.
o how would i hate my own biological father?

I admire that i mean to say, kuma idan ba son kike mood dina ya lalace na je gurin daurin auren nan da bacin rai ba mu bar maganar nan please
Cike da damuwa Anty ta ce.
hikenan, amman ka yi min alkawari idan ka dawo zaka je ka gaishe shi
promise
Ya fada sannan ya mika hannunsa ya karbi key din da Narjis take mika masa ya nufi kofar fita daga katon falon fuskarsa ba yabo ba fallasa.

ZAHRA POV.
wata duniyar ke matacciya ce, a duniyata kuma ke rayayyiya ce, rayuwar da zata raya tawa rayuwar zamu kafa tarihi a duniya Zahra, zamu zama wasu mutane abun kwatance, zamu rayu mu gina wata alkarya mai cike da iyalai masu alfahari da mu
Murmushi na yi.
llah ya nuna mana wannan ranar Deen
meen
Ya furta sannan ya dora kansa a wuyana hannayensa zagaye da cikina
an wata bakwai.

Lumshe ido na yi ina maida numfashi a hankali, wani sabon farinciki na ratsani, tabbas a wata duniyar ni matacciya ce, a duniyata kuma ni rayayyiya ce, rayuwa mai cike da albarka da kuma tarin farinciki.

Hannuna na dora saman hannun mijina ina shafawa a hankali.
aka siyo mana komai ba yau
a zan fita na bar miki fruit ai
Ya fada har lokacinsa kansa na saman kafata ya lumshe ido yana ta shakar kamshin turaren humrar dake jikina.
oh ai fruit ne ba kayan kwalama ba, kuma ni yunwa nake ji, abun da na girka ba zan iya cinsa ba
Ya bude idon ya juyo daga kansa daga jikina ya juyo da ni ta yadda zan fuskanci kyakkyawar fuskar mijina.
aboda me?

Kina nufin tun da na fita baki ci komai ba?
akociyata ta aiko min da shimkafa da wake na ci amman tun 12pm fa
aki son tuwon samo ne?
ai kace sai an tafasa ruwa ake girkawa, shi ne na tafasa ruwa na kwafa garin sai na dama shi kamar kamu, sai ya zama kamun be yi tuwo ba
Na fada a shagwabe.

Murmushi ya yi ya saka hannayensa biyu masu albarka ya rika fara kuma kyakkyawar fuskata.
aka zamu yi ta zaman aure baki iya girka komai ba Zahra?

Yayan da suka tashi a gidan masu kudi yan hutu su na san suna wannan rayuwar da rashin iya girki su ma kuma wasu, amman ke da kika tashi a irin familynmu ace komai kika girka sai ya lalace?
o ai Mama ce bata koya min ba
Na sake fada ina bata fuska kamar na ya taba ni na fashe masa da kuka.
iriniyarki ai ba zata bari Mama ta koya miki ba, amman zamu koya soon za mu iya okay...?

Na daga masa kai, sai ya sumbanci goshina, ni kuma na yi ma kaina masauki a kirjinsa ya rumgume ni.
ari na siyo miki wani abu ki ci, sai na dora mana wani tuwon, kin yi miji?
a tuwon be yi ba, shi ne ni kuma ban yi miyar ba
kay to bari na dora mana shimkafa zaki ci ko?
h amman a saka kwai
Ya lalaba aljihunsa sai ya dora bakinsa saitin kunnena ya rada min.
na da yan canji yau, har da kifi zan siyo na saka miki
Na rumgume shi ina kaunarsa na karuwa a zuciyata.
love you Deen
love you more Babe na
Ya fada min sannan ya sake ni, na zauna a saman cushion shi kuma ya fice daga falon.

Bani akwai wata mace da mijinta yake sonta kamar yadda Deen yake so na, ban yarda akwai wata macen da ta fini soyuwa a zuciyar mijinta kamar yadda so na y shiga zuciyar nawa mijin ya nemi tsabtataccen guri ya zauna ba.

Ban jin akwai wata mata da take son mijinta kamar ni Zahra nake son nawa mijin ba, hakika ni Zahra na yi dace da irin mijin da mata da yawa suke mafarkin samu, a tsawon shekara da wata hudu da muka kwashe a tare ko da rana daya Deen be taba ganin laifina ba, idan ma ya gani baya taba nuna, idan kuma na yi masa ba daidai zai fahimtar da ni cikin kwanciyar hankali da hikima ta yadda zan fahimta.

ABIEY POV.

Yana shigowa Falon Sauban ya mike tsaye da sauri suna kallon juna cike da kauna irin ta abokantata.

Abiey na mamakin yadda kalar shaddarsu ta zama daya dinkin ma iri daya hular kansu ce kawai ta banbanta.
a akai muka saka tufafi daya?

Sauban yayi murmushi ya nufi Abiey yana fadin.
nty ta dinka mana
Rumgume juna suka yi.
know you will make it, Welcome home Dude
Abiey yayi murmushi.
ongratulations Dude Happy marriage life, Allah ya baku zama lafiya
min Thank you
ayi kyau ango
Abiey ya fada bayan sun saki juna.
i dole na yi kyau, ango ne ni fa yau
Abiey ya yi murmushi ya nufi wata karamar kujera ya zauna.
need something to eat, ban ci komai ba since my last flight
Sauban asked, sai ya daga kafadunsa yana dan tabe baki.
ari na kira a kawo maka wani abu ka ci
etter
Ya furta tare da saka hannunsa aljihu ya ciro wayarsa ya soma dannawa.

Sauban ya kira wayar kanwarsa.

Sai da wayar ta kusa yankewa sannan ta yi piciking.
ello Yaya
i samo ma Abiey wani abu ya ci
aya wanka zan shiga, amman zana aiko wata ta kawo
Ya katse wayar ba tare da yace komai ba.

After like 10min wata kyakkyawar budurwa ta shigo falon dauke da plate din masa (Waina) ta nufi inda Abiey yake ya duka ta aje masa, tana kokarin mikewa tsaye Abiey ya dago cike da kasaita ya kalleta sai ta mike tsaye tare da idanuwansa.
ou're Pretty...

A tsakanin furucin da kuma ganinsa sai ta rasa wane ya fi bata mamaki.
hank You Abiey
Ya gyara zaman idanuwansa a fuskarta.
o you know me
ou're famous waye be sanka ba?

Sauban ya amsa masa, juyawa ya yi ya kalli Sauban kamin ya juyo ya sake kallon yarinyar form head to toe.
hat if i told you i like you
Murmushi ta yi ta juya ta fice daga falon.

Sauban kallonsa kawai yake da mamaki.
hat if i say i like her?
Chapter 2 · 0% Book details