← Book details Ciwon So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 70 OF 134

Sashe 70

Ciwon So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da taimakon video dake playing na yi musu farfesun nama zallarshi, yadda na ga suna zuba abubuwa haka na yi sai dai ban saka kayan kamshi ba domin ban ga ko daya ba, sinadarin dandano ma daker na ganoshi, sai da na gama na sauke sannan na fasa kwai na soya, ban yi tunanin dandanawa na ji yadda girki yake ba domin na gama girkin ne cikin rashin natsuwa ina ta fargabar kar Hajiya Jamila ko Mijinta su shigo su same ni da wayar, wannan yasa idan na kalla sai na boye wayar a cikin zane, domin idan wani ya same ni da ita ban san me zan ce ba musamman ma shi wata kila zai ce sata na yi, sai dai cikin hikimar Allah babu wanda leko kitchen din har na gama girkin.

Manyan kuloli na dauko na zuba komai a dabam dabam sannan na dauka na nufi dinning na jera sannan koma kitchen din na dauki wayar na da na aje bayan cups na yi clearing video din da na kalla na rufe data na fito ina ta kalle kalle har na yi nasarar aje wayar a gurin da na dauke ta, wani wawan tsalle na daka ina jindadin yadda na shirya komai ba tare da kowa ya gane komai ba, ba tare da tunanin komai ba na haura sama ba kwankwasa kofar dakinta tun kamin, daga inda nake tsaye ina jiyo sautin Ummiter, hakan ya fahimtar da ni hira suke mai cike da nishadi, ashe kuwa na canka a daidai domin dariyar dake take yi a yanzu ya tabbatar min da haka.
ahra
a'am Hajiya tana ciki
Na amsa ba tare da na gaishe ta ba daman can zuciyata bata taba raya min na gaishe ta ba, taya zan gaishe da matar da bata wuce sa'a ta ba.
h tana ciki
Ta bude kofar dakin gaba daya, hakan ya bani damar hango Alhaji Bashir dake zaune kan kujera Hajiya Jamila kuma tana zaune kusa da shi, sai dai na ga tsabanin abun da na gani a fuskar Ummiter da Alhaji Bashir, ita kam sam babu ko kufan murmushi a tare da ita balle dariya har ya kaita ga nishadi.
12/28/22, 11:06 - Buhainat: Bayan na sanar musu cewar na gama na sauko na daya a dayan set din cushion din domin bana son na tsaya a kusa da inda ya zauna dazun yayi zaton ko na taba mashi waya, babu mai iya sanin farincikina sai Allah da ya amince min na girka wannan breakfast a yau na shirya komai ba tare da sanin kowa ba, balle a gane cewar ban iya ba.

Ummiter ce ta fara saukowa jikinta sanye da tufafin bachi wando da riga ta nade kanta da wani abun da nake kyautata zaton tawul ne.

Alhaji Bashir ne na biyu sannan Hajiya Jamila, a duk lokacin da muka hada ido harara take aiko min da ita, mijinta kam ban da murmushi babu abun da yake, ba na ce ina ganinshi kullum ba balle na ba da shaidar kyakkyawan murmushin sake fita tsakanin kumatunshi amman tabbas tsakanin jiya da na fara bashi labarina zuwa yau na lura nishadin shi dabam yake.
in cire na ki ko?
a ban zuba ba
e da girki, mu da fara ci zo ki zuba na ki mana
Na dauki plate din da yake nan na bude cooler na zuba, na sake daukar dayan na zuba dankali da kwai, sannan na dauka zan tafi.
ea fa?

Na juyo na kalleshi sai kuma na kalli Hajiya Jamila wacce ta hade min fuska.
a wannan ya isa
Ban jira ya sake cewa wani abu ba na fito falon da saurina, kamin na karasa bq na tsaya na dandana abinci domin tun a cikin yawuna ya tsinke, saranda na yi ina fidda ido waje, anyi ba'ayi ba kenan ni kaina ban taba cin girki marar dadi irin wannan gashi dai be nuna ba kuma ga rashin dadi wani gurin ma kamar gishiri ya zarce.
nnalillahi Wa'inna Ilaihirraji'un
Na fada cikin tashin hankali, da gudu na karasa bq din a waje na aje plates din hannuna na dawo da gudu zuwa main house din jikina har mazari yake, ala ala nake idan ba su ci ba ina shiga cikin falon muryar Hajiya Jamila ta dira a kunne
i gaskiya ba zan iya cin wannan abincin ba
Ummiter kuma sai kwasar dariya take, tsaye na yi jikin kofar falon irin yadda yara suke idan sun yi laifi fuskana na bayyana rashin jindadin abun da na aikata, sai suka dago suna dubana, Alhaji Bashir da fuskarsa take sake har yanzu ya ce.
ahra karaso mana
Kamar ance karasa ki jr ga ajalinki haka na ji, sai na samu kaina da kara matsawa baya na kwalla sharrr daman can haka nake zarar zan aikata laifi to kuka ne zai biyo baya tun kam ayi min hukunci.
an iskanci kin san baki iya girki ba kika karba kika yi?

Shi wannan abinci mai kama da guba da kika girka mana so kike mu ci mu mutu ne?

Na girgiza kai daga inda nake tsaye, sai Alhaji Bashir yayi alama da na zo da hannu, cikin karfin hali na taka na karasa gurin ina mai tsananin jin kunya taya mace kamar ni ace ban iya girki ba, ai da kunya ba ma karama ba.
iriniya bata barki kin tsaya kin ko yi girki ba ko Zahra?

Na sauke kai na kasa ina jin sautin murmushinsa.
ideo da kika gani a waya suna tsallaken time ne ke kuma kin yi amfani da yadda suke kika girka mana wannan ba ki yi la'akari da haka ba
Wata kunya ce ta kama ni, ya aka yi ya san na dauki wayar har na duba?ko dai akwai camera a falon da kitchen din ne?

Wata kila Hajiya Jamila ta boye min ne saboda na saki jiki na aikata wani abun ta gani, wannan maganar da mijinta yayi ya tabbatar min da akwai camera a falon ba kamar yadda Hajiya Jamila tace min a waje kawai aka saka camerar tsaron ba.

Yanayin yadda muryarsa ke fita ya isa ya karantar da ni cewar ranshi be bace ba, musamman da na daga kai na kalli fuskarsa sai na yi arba da murmushi irin na mazan dake da kokarin fin karfin zuciyarsu ko da an musu ba daidai ba su kasa nunawa.

Ummiter kallon mamaki take min tana yi ma Alhaji Bashir sai kuma ta kalli Hajiya Jamila da ta kusa mutuwa tsaye.
a ki iya girki ba Zahra?

Ya tambaya, sai na daga masa kai ina dan turo baki ji nake kamar ya muzantani a bainar nasi.
a kamata ki koya ko dan gaba, maza suna son mace da ta iya girki misali irina ina son mace mai girki kala kala, kuma ya kamata ki koyi amfani da wasu abubuwan like wannan dankali akwai inda ake soya shi ba sai an saka cikin ruwan mai ba, Wife ina tunanin catering school zamu nema mata what do you think?

Ya karasa yana kallonta wata uwar harara da ta jefo masa ni kaina sai da na nemi natsuwata na rasa, Ummiter kam abun da take nema ne ya bude mata kofa wato gulma har bakin Alhaji Bashir dake motsi kallon take balle kuma reaction dina da na Hajiya Jamila.
ubby ina son magana da kai
Tana fadar haka ta mike tsaye har wani hura hanci take kallo daya zaka yi mata ka fahimci ranta a bace yake, daman kuma na lura da hakan tun a jiya.
kay gani nan shigowa
Amsa mata yake amman idonshi akai yake kamar zata wulgar da kujerar data zauna haka ta jata baya ta bar dinning a matukar fusace, a take na karanci jindadi a fuskar Ummiter sai kallona take da mamaki.
mmiter shiga kitchen ki shirya mana wani abun da zamu ci
kay dan'uwana Yayana
Ya mike tsaye tare da jan kujerar a baya a hankali ta sauka dinning din ta shiga kitchen.
auna
Yayi min nuna da kujerar da Hajiya Jamila ta tashi.
allabai...

Ban karasa fadar abun da zan fada ba ya daga min hannu.
i ce Bashir idan yayi miki nauyi ki kira da Mr Bashir
Sai da na ji faduwar gaba for no reason.
ajiya Jamila zata iya fada, tace kar na sake kebewa da kai
Murmushi yayi ya dauki dankalin ya kai bakinshi.
na ta karanta abubuwa akanki, har yanzu akwai kurciya da wauta irin ta yan auta a tare da ke, taya Jamila zata yi miki magana cewar karki sake kebewa da mijinta kuma ki fada min?

Dazun ma zuciyarki bata raya miki da sanina na bar wayata akan kujera ba?

Ba ki yi mamakin wayar babu password ba?

I expect ki dauka ki duba wani abu kuma kin yi
Risinawa na yi kasa ina kuka.
allahi ba bincike na yi maka ba video kawai na duba na abinci
Da hannu yayi alama da na tashi tsaye.
ina tauye kanki kuma ba ki iya tsayawa ki yi tunani Mai Kyau kamin aikata abu, ya kamata ki fito kai tsaye ki fada min ban iya girki ba, daman na saka ran haka yara irin da basa jin magana ba komai suka iya ba, sai kuka da shagwaba, i wonder how mijinki ya iya zama da ke?

Yanayin yadda ya karashe maganar ya nuna tambaya yake da neman sani, sai na share hawayena.
aman ai ya saba da halina tun a gida
hi Abiey?
a Deen
Yayi murmushi.
hi ma kin taba masa kenan?

Zauna ki tsakura min ya kuka kare da Abiey?

Na kalli hanyar stairs yan hanjin cikina na kadawa ba dan tsoron Hajiya Jamila ba sai dan gudun bacin rai, kallon stairs din yayi ya kalleni
ook Zahra daga Jamila har abun da yake karkashinta iko na ne mallakina na ne, saboda haka ki natsu kuma ki bi duk umarnin da zan baki wata kila hakan zai goge shafukan laifukan da kike da su a gurina
Zaunawa na yi idona na kanshi irin na marasa gaskiya.
aya ce na ni wani abu?

Wani laifin aka ce na maka?

Ko kuma na aikata cikin rashin sani ne?
Chapter 70 · 0% Book details