← Book details Ciwon So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 106 OF 134

Sashe 106

Ciwon So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Na tashi na karasa kusa da Abiey na bude qur'ane na fara binsa ina karanta masa ina tofawa, idan na yi kamar aya goma sai na dawo gurin abokinsa Sauban na karanta masa shi ma na tofa masa, amman ba wani canj, Sauban din sai bin kujeru yake yana son ya tashi tsaye ya kasa.
ayyo Jama'a a kai ni gida
Jin haka yasa na rufe kur'ane na maida a cikin jakata na aje jakar a gefen kujera na nufi inda suka aje keys din motar wato kan hannun kujera na nufi kofar na bude na fita na nufi motar da suka zo na saka key din ina da murdawa daker na samu kofar ta bude sai na bude ganbu na dawo falon na rika Sauban daya gagara mikewa sai cewa yake a kai shi gida.
acece ke?
ahra
ahra wa?
atima Zahra
ina nake?
idan Ammy
acece Ammy?
ahaifiyar abokinka Abiey?
inene kuma Abii?

Yanzu kam ban san kalar amsar da zan bashi ba, sai dai na yi iya kokarina na ganin na mikar da shi tsaye amman na kasa, domin ni babu karfi shi ma kuma sai shan yaji yake yana lasar baki kamar tsohon maye.
na Matata?
na zan sani ni, kana da mata ne?
a dauka ina da ita, to Ina Mamata ko ita ba ba ni da ita?

Kin san gidanmu?

Ina ne nan?
an sani ba ni dai dan Allah ka yi shiru
Ya ki yayi shiru sai tambayoyi yake sako min kala kala da ban san amsarsu ba, Abiey kuma ya ki ya zauna sai zagaye falon yake yana ta yi ma bakin da ban san su waye ba maraba da zuwa, cikin iya Allah na rika Sauban na mika mike tsaye sai ya sako min nauyinsa ni da shi mika fadi a kasa, sai na yi saurin tashi ina rika shi.
an Allah ki kai ni gida
o ai shi ne nake son ka shiga motar sai na tuka ka tafi gida, ni ina zan san gidanku
a can ake bi, sai abi nan sai abi can
Ya nuna min kofar kitchen, jin kamar tsayawar mota yasa na sake shi da sauri na nufi inda na aje talkamina na dauka na dauki jakata na nufi kofar kitchen na bude na tsaya a kitchen din har sai da na ji shigowar Ammy, salati ta saka ita da Anty Zainab tana tambayar lafiya, amman babu mai amsa mata a cikinsu Sauban din sai kiran a kai shi gida yake, Abiey kuma yana fadin gidan da baki babu gurin zama.
llah yasa ba wani sammun aka yi masa ba, matan uban nan sun saka shi gaba ga kuma makiya abokan wasansa
Ina jin haka sai wata zuciyar tace min na fito na fadawa Ammy abun da ya faru, wata kuma tace min na ranta a na kare, sai na bude kofar baya cikin sanda na fice daga kitchen din, kamin na isa gate din na samu na fice jinina ya hau kusan tari biyar ma domin ji nake kamae ma'aikatan gidan tare ni za su yi.

Na isa na fadawa Mama da Yaya Maryam aika aikar da na yi sai Mama ta kwashi yan tufafinta da za su wadaceta ta yi kwana biyu ni ma na debi nawa muka bar unguwar, Family house dinsu muka tare babu fadan da ban sha ba a lokacin da Mama ta fada musu dalilin guduwarmu, Ba dama na san da sai Deen ya same ni a can yayi min dukan daya saba domin ya shata min line tsakanina da Abiey amman ban ji gashi na sake komawa gidan har na sake aikata laifi, sai dai ban tsira da dukanba domin Mama ta yi min nata da kanta sai dai nata dukan mai sauki be ne ba irin wanda Deen yake min ba na fitar hankali.

Jin shiru ba a zo nemanmu ba Mama ta tambaya a unguwa aka fada mata cewar babu wanda ya zo nemanmu sannan muka dawo gidan, tun daga lokacin sai ya zamana idan zan tafi makarantar Islamiya sai Mama ta raka ni ta tabbatar na shiga sannan ta dawo, idan kuma muka taso bana yarda na bi ta gaban gidansu Abiey ma saboda Mama ta fada min cewar abun da na yi wata kila idan Ammy ta kama ni zata mika ni hannun sojoji yan sanda kuma za su tuhume ni da mu'amala da kayan maye, ba dan wannan tsoron ba da babu abun da zai hana na koma gidan ko dan na bawa Ammy da shi kanshi Abiey hakurin abun da ya faru.

A haka na kwashe wata biyu ko kofar gidan bana yarda na bi balle ya mutanen gidan su gan ni.

Wata rana ina zaune ina wanke uniform din makarantar Islamiyar mu sai ga Ammy ta sallamo a gidan tana sanye da bakar abaya ta yafa katon mayafi a sama dayan hannunta rike da jakar alfarma, sai kamshin turare take zubawa irin na manyan matan masu kudi, fuskarta a sake tana ta murmushi.

Sai dai hakan be hana na tashi na koma bayan Mama na boya ba gabana sai faduwa yake ina ganin kamar ta zo ta yi wata magana ne ko ta saka a kamani kamar yadda Mama take min hasashe.
in san kin yi rashin gaskiya shiyasa kike boya ko?

Maganarta ya saka hankalina ya dan kanta domin a cikin wani yanayi mai kama da raha ta yi min maganar, Mama ta tashi da sauri ta dauko mata tabarma ta shimfida mata ta dora carpet din sallah akai jikinta har kyarma yake.
annu da zuwa Hajiya Sannu da zuwa, Allah yasa ba wanin laifin Zahra ta sake yi ba?
a ni da na zo na ji dalilin rashin zuwan Zahra a gidana, ko dai ke kika hanata?

Tare da Aliyu mike yana waje shi ya matsa min da maganar Zahra ya dame ni na zo na ji dalilin daina zuwanta
A yadda na kura Ammy mace ce mai far'a da son mutane, kuma bata kyamar talaka haka ma
anta Abiey.

Sun dauki lokaci suna hira da Mama sannan ta sanar min cewar Abiey yana waje yana jirana na tafi gunsa mu gaisa.

Wanke kafafuwa na yi na saka hijabina na nufi kofar gida, tafiya kadan na hango inda suka faka motarsu, domin kalar motar kadai ya isa ya saka na gane cewar ita ce motar da Ammy ta shigo, tafiya nake ina jin wani abu mai kama da marmarin ganin Abiey yana sallamo min har na isa, bakin gilashin motar ya sauke karaf idonsa cikin nawa wani kalar kwarjinsa da kimarsa suka cika idona, a take na samu kaina da faduwar gaba da kuma jin kunya a lokaci daya.
i idonta sarkin kiriniya how are you?

'm fine
Na dan kalleshi kadan na dauke ido da sauri, kwana biyun nan da ban saka shi a ido ba na lura har wani kyau da haske ya kara.

Mun dade a tsaye muna hira sannan miko min ledar chocolate yana zolayata wai ya san yara chocolate ko ice cream suke sha shiyasa ya siyo min.

Daga lokacin sai wani irin shakuwa ta shiga tsakanina da shi, Mama kuma ta sabu da Ammy wani lokacin ma idan Ammy tana son wani abu a gurin Mama zata aiko ta nema mata, ni kuwa sai ya zamana ba ni da wani aboki sai Abiey komai an dauko a duniyar nan Abiey daman can ina son mutumen da zai iya daukar matsalata, kuma ya zamana yana sakar kin fuska yana nuna min kulawa ba duka ba kyara ba kamar Deen, sai dai duk da irin shakuwar da ke tsakaninmu Abiey baya yarsa ya sha abun hannuna ko ya ci sai idan tare muka siya, Ammy ma bata yarda na shigar mata kitchen idan ma zan ci abinci a gidan sai ta zuba min da kanta ko kuma na zuba a kan idonta.

Ban taba yarda Deen ya san da alaka ta da Abiey ba Mama ba ban bari ta sani ba, domin na san idan ta sani zata iya hanani yawan fitar da nake da shi a sace da kuma zuwa gidajen yan'uwansa ko na Ammy da muke, kamar idan an aike mu ko kuma ziyarar ta tashi.

A duk cikin yan'uwa na lura Abiey ya fi shakuwa da Dr Zainab duk wani sirri nasa ta sani, duk wata shawara da ita yake, yana yawan zuwa gidanta da ni ko ba ni ya wuni, ban san Abiey babban mutum ba ne har sai da ya taba daukata muka shiga gidan Sarauta gurin step Mother dinsa wato Anty Amarya, ita ma tana da yara biyu mata Aisha da Narji, su ma dai babu ruwansu da daukar kai cikin kankanen lokaci muka sabu.

Idan Abiey ya shirya tafiya gurin buga wasansa na kwallo sai na ji kamar zai yi tafiyar da babu dawowa ne saboda shakuwar dake tsakaninmu a ranar bana iya cin abinci haka zan wuni kamar marar lafiya, idan Mama ta lura da na daina zuwa gidan kwana biyu sai nace mata Ammy ta yi tafiya bata nan, idan ya kira waya ko video call a gidan Ammy da sunan mu gaisa sai na ji kamar na shige cikin wayar tsabar farinciki.

A lokacin da Deen ya lura da hankalina ya dauke daga kan samari da kuma duk wata shiririta da nake bana da gurin zuwa sai gidan Ammy Ammy dai, ko da na zauna a gida Abiey zai aiko kirana da sunan Ammy na tafi a gidan na wuni, wani lokacin mu yi ta game ko wasan tsere tun Ammy na yi mana fada har ta gaji ta saka mana ido, idan muka yi wani abun sai dai ta yi dariya.

Idan Abiey na yi arba da wata budurwa da nake ganin ya dace Abiey ya aureta ko ya so ta, sai na tareta na karbo masa numberta amman ba zai ba ni hadin kai ba, ko da ya fara waya da ita kwana biyu sai ya kawo dalilin da zai saka su yi fada.
Chapter 106 · 0% Book details