Sashe 94
Ciwon So Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Nice munafukar kennan?, Ohk , lalle kuwa hajia kin fito da hanyar da zaki saka kanki a uku da kanki, maganar gida ai ni ba mahaukaciya bace na san na Babangida ne ba zan kankara hakori a jiki ba, ke fa bari ki ji kece gajiyayiya dan kuwa dama ni mai sana'a ce, dan na san mata suka fi fi yawa a Y'ayana ban zauna na yi jira aka bani ba, ke kuwa dole ki rikice kan abinda ba na ke daya da yayanki kadai ba, ki sake maida niya kafin ki tafin da yayanki mu nunawa junna wa yake wa a gidan nan!" Maman Furera ta fada tana zazaro ido, Mams kuwa idannuwanta a kan Babangida dake zaune bawan Allah yana kallon ikon Allah
"Hum" ya samu ya iya fada da kyar sannan ya sake zubawa yaran da yaa ga hankalinsu duk kamar ba a jikinsu ba, bama irin maganar gida da suka saka a gabansu kai tsayen nan bayan ba kowa ne ya dan maganar gidan na, hasalima manyan ne kawai suka sani na baya bayan nan ba sani suka yi ba, a ganninsa hakan bai dace ba, a kwakwaluwar yaro sai a hadasa masa wata fitinar ta rashin nutsuwar zuciya da tashin hankali, haka kuma in sunna neman fitina da suke wawurar Aunty Amarya ido rufe, ita kuma bakinta kamar an dinke ta yi shiru bata cewa kowa komai
A tausashe ya ce" Ku yi hakuri hajia, amma irin haka bana so, kar ku kuma kamantawa daga yau!"
A tausashe ya fada , magana mai kama da umarni wace ta saka wasu yi masa kallon mamaki duba da ai iyayensu ne, wasu kuwa jin sassauci a zukatansu
Sai kuma ya dora maganar a dake cewa" Gidan nan a daina dauka ana alakantashi da gidana kai tsaye, zan fi so a kire shi family house, saboda tun farkon dora tubalinsa da haka aka dora, sannan ina so baki dayanku ku sani du wani mai ra'ayin zama a cikinsa ya zauna kansa tsaye ya kuma rayu a sake a cikin mudin rayuwarsa dan gida ne na familly domin ba zan taba kauda sunnana a kansa ba, dan sunnan hajia ke sama, ya zamto gida ne na iyalin AHMAD SULAIMANE, Abu daya da muke da ja in ja da ku a nan shine babu wace zata fitar min da kanneina ta je min wani waje da su, namiji ko mace idan suka fita daga nan da nufin barin gidan nan dindindin da sunnan aure ne, koda Allah ya kiyaye wani abu ya samu aurensu nan ne wajen zamansu, wannan din ina da tabaci a kan haka sai kuma inda karfina ya kare!"
Da mamaki Umman Abul ta ce" Kamar yaya Babangida?Kana nufin tafia zan yi na bar yan Y'ayana kanana a nan a wajen wa toh?
Ka san dai ai Mama nata take riko, bayan wannan ma hannu daya zai iya da rigingimun yau da gobe kuwa ko zaka dora dokar sauran kannenka ma'aikata su ringa taimakawa?"
Sai a wannan lokacin Mamah ta budi bakinta, dan kuwa sosai ta fahimci Maman Abul so take yi sai ta raba abinda ba shikenan ba a gaban yara, shi kuma ba wani iya kare kansa zai yi ba da yawan magangannun, ko a yanzu ta yi mamakin da ya ringa binsu yana basu amsoshin nan , kuma lalle ta fahimci kamar zai rike amanar Abansa
Tana duban Maman Abul ta ce" Ke hajia dan Allah ki zauna ki kuma sassauta muryarki haka kuma ki tauna kalamanki kafin ki ringa saki dan baki daya nan ido a kanki yake!"
Tunda aka yi rasuwar sai yanzu suka ji muryar Mama da tauri haka, dan tunda ta zo a jigace take da rashi na masoyi, amma a yanzu da halin hakan ta kama ta yi ta kuma dora da fadin" Ke wanda ya hada kishinma ya tafi ba zaki nutsu a yi magana ba?
Inace damuwarki gado ne?
An ce za'a zo a raba a baki kasonki, ke yanzu idan kika dauki yayan nan su tara kika je gidan mahaifinki da su su rike su ta yayane?
Ko gwamna ne shi in fada maki wahalar d'a sai nasa!, Ke din dai zasu iya rikewar da dadin rai garkenki kuwa zasu gajiya yau ko gobe!, Muma ba dan mun isa ba, ba kuma dan muna takamar dukiya ba, ba kuma niyarmu mu dorawa yayanki kawo dan na talafawa karshen wata dan a ciyar da yara ba, Allah ya hanne mu, zamu sake mikewa mu kama salati mu kuma nema, bi'izinillah ba zamu kwana bamu saka a bakunnanmu na salati ba, mun shirya tsaf mun kuma san abubuwan dake gabanmu, mu ba mahaukata bane, haka kuma mutuwar Docter ba tana nufin zaku wargaza mana ahali bane, Bango ya fadi hakane, amma da tubali a girke, zamu ci gaba da dorawa ne ta yadda zamu sake gini mai kargo koda muma mun tafi mun bar baya ta yada koda shima ya tafi zai bar baya mai kyau bi'izinillah!, Ina so ki kama kanki ko ki tashi ki yi tafiyarki bangarenki, zan kuma fada a gabanku baki daya na isa da
an Docter, ta laluma ko ta masifa dole zasu gyara kansu su rike kansu mu ci gaba da tafia bisa turbar addini da tarbiya, wanda ya ki kuma mu zuba mu gani ni da shi!, Tun jiya da kika yi magana na saka wayar nan a caji, wace ke dauke da magangannun Docter muna cikin jirgi da saukarmu a kasar katar har zuwa zamansa a asibiti kafin a shiga aiki da shi , zan kunna kowa ya saurara, ruwanki ki bi ko kar ki bi, ni dai na san na bi na gama sai dai fatan Allah ya kama min, in kin yi niya mu hadu mu rike a haka idan kin samu mijin ko me kike ikirari ki tafi ba damuwa bane, in kuwa gidan zaki je ki gama rufin kan duka ke ta gano amma banda su ABUL!"
Daga nan ta laluba yar karamar jakarta ta fata ta ciro wayar nan wace Ya zubawa ido yana kallo
Da sauri ya mike ya karasa ya amshi wayar da nufin komawa wajen da yake zaune dazu, amma Mama ta hanna ta saka shi zama daf da ita a nutse ta ce" Komai fa sai kowa ya ji?" Hakan ya saka shi yin wani iri yana kallonta, karshe a dole ya danna dan ta riga ta hade fuska babu sauran magana
A kan kannensa kawai ya dora dubbansa, bayan ya kunna ya saka duka kaf amsa amon wayar ya zuba masu ido yana kallon r
action din kowa, domin ABAH a lokacin yana cikin yan tsokanar ne, yace wannan yace wannan yana neman rigima da Mama ita kuma tana kaucewa tana saka shi dariya, sai kuma ya ce " Hajiar likita dan taya ni zayano
an da ni din nan na haifa mu ji?, Kar aje tsufan ya taba kan nawa ko kuma na tara su ne kamar duniya.......?
A kadan fa na tara arba'in ko?, Mu irga na gani abu da ba saban ba ina gannin ina iya samu na rufe ido na yi ta baku kunna juye min abina .....a fara daga kanki uwar gida sarautar mata bismillah".........
Dan murmushi kawai ta yi ta ce" Babangida Aisha,............."
"Dan dakata, kin ga a tafi a hankali, Babangida,Sulaimana kennan, ABAHNA, farin cikina, mai dauke da sunnan Babana, mai son farin cikina, Abahna kana ji dole zaka saurareni kuma na hanneka katse min magana ko katse daukan nan da aka kunna, Abahna girma ya hau kanka, girma ya hau kanka ABAHNA, dama da girman a kanka ama ba kamar idan ina gefe ba, a yanzu ne zaka dauki abubuwa hudu ka rike, Hakuri, jajircewa, tsanani Addu'a, in ba haka ba zaka ga rashin kirki a tarbiyar ya'ya, ABAH ka ga dole gida ya zamto da namiji baba in ba haka ba kowani marar da'a na iya zuwa ya nemi karya maka kara a ido, hakan na nufin dole zaka yi hakuri ka kauro gidanka sannan ka zauna a wajen da zaka fi hangen du wani shige da fice watau bangarena........." Docter ke fada a tausashe yana kallon fuskar MARSHAL da ta dauki ja
A dan birkice MARSHAL ya ce" Abah, menene ya kawo magangannun nan dan Allah?, Cuta ai ba mutuwa bace ko?, Zaka dawo ka koma dakinka ka kula da yayanka da kanka Abahna, ni ba zan zauna a dakinka ba"
Abah ya yi murmushi ya kamo hannayensa gannin har kamar kwallah ke cika a idannuwansa a tausashe ya ce" Kuka zaka yi?, Sai kana cicijewa kana daure fuska kai a dole baka kuka amma ka wani zauna min ni a gabana ka min kuka, gaskiya a daina dan nima ai ba wani son kukan nake yi ba, kuma da kake cewa na yi shiru yanzu da nake da damar maganar ai gwara na yi ko ABAH?
Idan karfina ya kare fa?