← Book details Ciwon So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 72 OF 134

Sashe 72

Ciwon So Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Kai kuma ya aka yi ka zo?
hi ne abun tambayar ai
Na waige na kalli mutanen da suka ba mu masauki a gidansu, sannan na juyo na kalli Abiey na ce.
dan sun tambaye ka kai mijina ne ka ce musu eh, ni ma idan sun tambaya zan ce musu kai mijina ne ni matarka ce
aboda me?
o ai idan ba mu fadi haka ba, za a mana kallon yan iska ne ace miya kuka zo yi ba miji da mata ba
i kin min kankanta ba zan iya aurenki ba, kuma ban shirya auren yanzu ba ma
i ma ba da gaske na ke ba, saboda na kare mutuncina ne, kar ayi min kallon yar iska
Na fada ina zare masa ido yo ina ruwana da mukaminsa ko wani kudinsa ko girma na da yayi to me age it's just a number.
12/28/22, 11:06 - Buhainat: Da Ammy aka zo daukar mu, ta yi musu godiya sosai ta yi musu alheri sannan muka shiga motar da direbanta tare da wani dan'uwanta yake ja, muka kama hanyar gida.

Babu kalar fadan da Ammy bata mana ba a motar musamman ma Abiey shi ta fi dorawa laifi, muna isa gidan ta ba ni bandaki na yi wanka ta dauko min wata doguwar riga da ta yi min yawa na saka.

Sannan ta kawo min abinci na zauna a kasa ina ci ina kuma tana zaune a saman gadonta tana min wani sabon fadan.
anzu kin tashi hankalin Mamanki Allah kadai ya san halin da ta shiga, tace karki je biki amman kin kama kafa kin tafi konda yake ba lafinku ba ne laifin Aliyu ne
to ai na fada masa laifinshi ne amman be yarda ba, ai da be kai ni gidan ba da ba haka be faru ba
un tashi hankalinmu na kira wayarshi a kashe, yau da safe kamin mu tafi ma Mamanki ta aiko gidan nan gurin neman ki na fada mata cewar ba ku ma garin nan
mmy dan Allah ki rufa min asiri karki ce ni na taho da kafafuwana, ki ce Abiey sato ni yayi
a akan me zan lakawa
ana sata?

Ke kika aikata ai dole a miki hukunci
Duk yadda na so Ammy ta shirya karya ta yadda za a wanke ni a gurin Mama Ammy bata yarda ba, haka ta saka ni gaba muka tafi har gidan ita ta fara shiga, ina lafe kofar gidan sai ga Deen ya fito da saurinsa yana ganina ya dafa zuciyarsa ya zauna a dankali dake kofar gidan ya rufe ido ya dafe kai.
ahra kin daga min hankali
Na matsa baya, na san hukunci mai kauri ne ban daga masa hankalin ba ma ya hukunta ni balle kuma na daga masa hankali.
na mutumen nan ya kaiki?

Miya faru?
abu abun da ya faru, hannuna kawai ya rike sau uku be amman babu abun da ya faru
Ya mike tsaye a fusace ni kuma na fada masa gaskiyar ne saboda ban iya karya ba, kuma kar yayi tunanin ko wani abun ya faru yace zai min hukunci mai tsauri.
uce mu shiga cikin gida
Da gudu na shiga cikin gidan, sai na samu gidan na mu cike da Uncles dina da Hajiya da kuma Yaya Maryam, juyawa na yi zan koma saboda mugun kallon da Mama take min sai Deen ya riko ni riko bana wasa ba ya saka kafarshi ya buge nawa kafafuwan na fadi kasa ba kwari sai ihu ya biyo baya, a take ya cire belt dinsa ya fara dukana da shi aka rasa wanda zai ce uffan ko ya ta so ceceni a hannunsa sai Ammy dake kokarin tara jikinta ta maida ni bayanta
aban bawan Allah wannan mugun dukan kamar wanda ta yi kisan kai, wannan ai sai ka ji mata ciwo
Deen kamar jiranta yake sai yayo kanta yana kokarin sauke haushin
anta a kanta.
na ruwanki lokacin da zata bi
anki miyasa ba ki hana ba?

Yarinya kamae Zahra ace ta iya bin namiji suje su kwana a wani guri?

Ammy ta kalleshi da kyau ta girgiza kai.
aga ganin idonka yaron nan baka da tarbiya, taya zaka kalli idona ka fada min wannan maganar?

Ai ko ban san Zahra ba idan na ga zata yi abun da be kamata ba ba zan barta ba balle kuma ace da
ana zata aikata haka?

Sai da Hajiya ta taso ta shiga tsakani sannan Deen ya shafa min lafiya, Ammy ta fice rai a bace, daga ranar ban sake zuwa ko'ina ba kullum ina gida gidan na daga
aki sai daki idan na fito waje to fitsari zan yi ko na zagaya bandaki, Mari Deen ya saka min saboda kar na sake zuwa ko'ina ba sai dai idan zan yi fitsari ko bayan gidan Mama ta kan bude ni naje na yi idan na dawo sai na miki mata kafafuwana ta saka min.

Wata rana ina sanye da marin ina alwala kawata Hafsat ta shigo muka sha hira da ita da zata tafi bata sakon gaisuwar yan makarantar mu na Islamiya da kuma boko, har ina fadar na yi marmarin makaranta.

Bayan ta tafi na tashi ina tsalle cikin marin na shiga daki na yi sallah, sai na kwanta a gurin na yi shiru ina ta tunanin abun da na jawa kaina da ina da yanci na je duk inda nake so amman ban da yanzu da aka saka min mari a cikin gidan ma ba ni da wani walwala, gashi babu mai cewa komai babu saka baki ya ba da hakuri yace a cire min.

Ina tsaka da kukana Deen ya shigo da yar ledarshi kamar yadda ya saba min idan zai shigo ya kan shigo min da wani abun ci saboda ya san ni da kwadayi gashi kuma ya saka an saka min mari bana da gurin zuwa.
uka me kuma kike?
a gaji da wannan marin Yaya Deen dan Allah ka cire min, Wallahi zan rika jin magana ka yi hakuri dan Allah
Fuskar damuwa yayi yana kallon fuskata dake zubar da hawaye.
i ma bana jindadin ganinki cikin marin nan Zahra, amman rashin jin maganarki ne yake damuna, bana son yadda kike shigewa Maza, wani zafi zuciyata take min idan ana kallonki ma balle kuma ace alaka ta shiga tsakaninki da wani
a zan sake ba, idan na sake ka fille min kai, dan Allah ka cire min wannan abun ya ishe ni
Yadda na marairaice fuska kadai ya isa ya saka shi tausaya min, daman can kuma na san akwai tausayina a tare da shi.
an cire miki, amman zaki min alkawarin babu ruwanki da kowa dan Allah duk rashin da zaki yi ki yi amman ban da kula maza
oh ba zan yi ba, cire min
Na janye zanena na mike masa fafaren kafafuwana, ina jin motsin Mama na yi saurin janye kafafuwan domin fada take min idan ina sakin jiki a gaban Deen.
eeni ne?
h Mama ya gida?
afiya Kalau ina su Hajiya
uma suna lafiya, suna gaisheku
na amsawa
ama na ce yanzu kam za a cirewa Zahra marin nan mu ga ko zata natsu
a natsu ma Wallahi ba zan sake ba
llah yasa
Mama ta fada sannan ta tashi ta dauko makullin ta bude min da kanta, wani tsalle na yi ina murna ina jindadi, Deen kallona kawai yake yana murmushi, a ranar na wuni cikin yanci sai dai haka be saka Mama ta bar ni na tafi ko kofar gida ba, washe gari ma Deen ya zo gidan daman kusan kullum yana gidan mu saboda ni, sai dai hakan be taba sakawa na ayyana a raina cewar so na yake ba, tunani be bani wannan ba.

Da zai fita na bishi ina masa magiyar ya kai ni gidan Yaya Maryam.
dan nace za tafi Mama ba zata bari ba, kuma idan muka tafi tare ma wani ba zai min magana ba
e ki fadawa Mama ki dauko Hijabinki
Da sauri na koma cikin na sanar da Mama sai tace ba zan bishi ba.
adda kike ganin idan kin keba wadanda zai miki fada yana nuna miki ba daidai ba ne, haka shi ma ba muharramin ki ba ne ya kamata ki san da wannan bana son shege masa da kike
ayyo Mama ina son zuwa dan Allah
ari sai ya tafi zan baki kudin napep ki tafi ke kadai
Hakan da Mama ta yi ba karamin dadi yayi min ba, daman bana son da shi sai dole domin takura min yake idan muna tafiya a tare ko kallon maza na yi sai yayi ta min fada.

Zuwa na yi na sanar masa cewar ba Mama ta hana ba zan tafi ba, sai ya shiga da kanshi yayi mata magana amman bata amince ba a dole ya ba ni hakuri yace na bari sai nan gaba kadan idan ta yardar zai tafi da ni.
Chapter 72 · 0% Book details