← Book details Ciwon So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 134

Sashe 27

Ciwon So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mikewa na yi tsaye ina gaishe shi sai ya amsa yana kallon fuskata.
a mai jiki?
ashi nan
Na amsa masa murya kasa kasa irin ta wanda ya rasa makama.
a fada muku ku yi kokari ku hada kudin maganin nan saboda Wallahi akwai matsala
A take na ji hankalina ya kara tashi, sai ya karasa kusa da Deen da tun jiya be farka ba, ni na rasa gane wane irin bachi ne yake ma.
udin ne muka kan hadawa, ban san ko kuna karbar rabi ba, ko kuma kuna yin aikin bashi in yaso daga baya sai mu biya, dan Allah a tainaka mana
a ina...

Ai ba a haka
an Allah a taimaka mana likita, mijina shi ne rayuwata idan na rasa shi zan shiga wani hali
Ya kalleni kamar mai nazari sai kuma ya cigaba da duba Deen da yake ya sake yin rubutu a jikin takardar magani ya miko min.
u nemo wadannan alluran ya farka yau da safen nan?
un jiya be farka ba har yanzu
dan ya farka ku kira likita, kuma a tabbatar a nemo wannan allurar dana rubuta miki
ohm, likita dan Allah a taimaka mana a karbi rabin daga baya zamu ciko, Wallahi zamu cika maka kudinka casss
okar asibiti ce, ba a karba rabi ba mu ake ba kudin ba, a account din asibiti ake sakawa, so kin ga kenan ba hurumi na ba ne
Ya amsa min sai na kara cire hope a lokacin na kalli mijina na sake kallon likita dake daf da fice.
ikita to zai yi a cire hantata mai lafiya a saka masa?

Ya juyo ba shi na jar nurse din suke tare da shi sai da suka kalleni da mamaki dayar har da zare ido.
allai kina son mijinki sosai, yanzu dai yadda za'ayi ki same ni office anjima kadan zan miki bayanin yadda komai yake
oh na gode
Na fada sannan na zauna saman kujerar ina kallon Deen, rayuwarmu ta baya nake tunawa yadda yake kula da ni yake nuna kauna da soyayya, yau kuma gashi kwance be ma san ina tsaye kansa ba.
llah ya baka lafiya
Na fada ina jin hawayen da suka min nisan zango sun durfafo idanuwa da gudunsu.

Ban iya jira har sai anjima da ya ce min ba, domin kuwa ba zan iya jiran ba, mafita nake nema ko ta halin yaya.

Dan haka na fita daga dakin kuwa da kasancewar na san Deen kadai zan bari a dakin domin Mama ta yi latti zuwa Hajiya kuma ta tafi yin wanka ta canza tufafi, dan haka ni kadai aka bari.

Office din likitan na tafi na tsaya daga bakin kofar har ya gama abun da zai yi ya shigo corridor da be da tsayi sosai sai ya same ni a tsaye ina jiransa.
anzu kika zo?
un dazu
Murmushi yayi ya tura kofar office din ya shiga.
ismillah
Ya fada sai na bi bayansa, da kansa ya nuna min inda zan zauna, ina zama aka kwankwaso kofar aka turo wani mutum ne mai kayan likitoci ya shigo suka yi magana ya fita, sannan ya likitan da har yanzu be san sunansa ya kalleni ya ce.
a sunanki ma?
ahra
Na amsa da sauri abun ka da mai nema, domin gani nake kamar taimaka mana zai yi yayi mana aikin bashi.
ahra
Ya kira sunana sai kuma yayi shiru ya dauko wayarsa ya tana sannan ya fara magana
ahra wannan cikin na ki na nawa ne?

Shekarar nawa da aure?

Kuma watan cikin nan nawa?

Ba tare da tunanin komai ba na amsa masa.
hekarar mu daya da wata hudu, cikina kuma yana cikin wata na takwas yanzu
ina zuwa awo?

Abun da ke cikinki lafiyarsa kalau?
h ina zuwa, kuma sun ce babu wata matsala
un fada miki abun da zaki haifa?
a ba mu yi wannan hoto ba, tun hoton da muka yi lokacin da cikin yana karami ba mu sake yin wani ba
rayuwata ban taba ganin mace mai tausayi da kaunarsa kamar ke ba, ban tana gani ba, da dai labarai ne sai na ce na tana ji shi ma ba kasafai ba
Na sauke kaina kasa.
ijina shi ne rayuwata, ya nuna kauna da gata a lokacin da nake tsananin bukatarsu, duk yadda zan fada maka mijina yake na maka karya, Wallahi ya wuce duk yadda kake tunani
llah sarki Allah ya bashi lafiya
aganar gaskiya ba a karbar kudin aiki rabi, ko naira biyar ce babu ba za a karba ba sai kin cika
anzu babu wata mafita kenan likita?

Babu wani taimako da zaka iya mana?

Ko rance dan Allah Wallahi zamu biya
Na fada da dukan gaskiyata ina magiya, sai yayi murmushi.
bun da yasa na same ni a officeafita zan fada miki, sai dai be zama lallai ki aminta ba, amman ni na aminta da ke, ina da yakin zaki rike min sirrina ko da abun da nake kudiri be karbu a gurinki ba
octor ni fa mafita nake nema, ko ma minene ka fada min Wallahi zan aikata indai zan samu kudin
Yayi jimmm kamar ba zai ce komai ba, sai kuma ya sake kallona ya ce.
na son ki min rantsuwa
Na kalleshi da mamaki.
antsuwa kuma na me?
aboda abun da zan fada miki be zama lallai ki aminta ba, sai dai abu ne da zamu taimaki juna ni da ke, ni ma wata zan taimaka domin tana cikin tsananin damuwa da bakinciki
oc ban gane ba, i thought magana kake yi sai kuma na ji kana zancen wata
Yaja dogon numfashi ya sauke, sannan ya bude laptop din dake gabansa yayi dan dane danen da zai yi ya juyo min da laptop din ya dawo gafe na yana nuna min hoton da aka dauka na ciwon Deen.
in ga yanayin yadda hantarsa take, daga nan zuwa nan kin ga har na fara baki, so dole sai mun bude gurin mun wanke mun saka magani sannan a dora shi akan wasu magunguna dazai wata 8 zuwa 12 yana sha, da kuma ba shi kula ta musamman, sannan akwai tests din da zamu masa before then like chest X-ray, electrocardiogram, urinalysis, white blood count da sauran, kuma zan fada miki tsakani da Allah idan ciwon ya kara wasu kwanaki zaki iya rasa mijinki
Na kalleshi hawaye na sauko min.
a zo nan ne saboda neman mafita, ba
dan ka kara daga min hankali ba
a sani, ina son na fada miki komai ne, domin bana son ki ga kamar zan yi hakan ne saboda kawai ina neman wata mafita
an Allah ka taimaka ka fada min
Na koma gurinsa ya zauna yayi shiru na dan mintuna, sannan ya ce.
kwai wata mata mai suna Jamila sherarta tara da aure, tana zaune da mijin lafiya kamin abubuwa su fara canjawa, saboda Allah be bata haihuwa ba tun da ta yi aure har zuwa yanzu da nake maganar nan da ke, sanadin hakan yan'uwan mijinta da shi kanshi mijinta sai suke fara canjawa mata har ya fara neman aure zai kara mata saboda likitoci ciki har da ni sun fada masa ba shi matsala ita kuma ba ta da matsalar komai lokaci ne kawai be yi ba
an ga ta inda labarin wannan matar ya shafe ni
Na fada domin har ga Allah ban ga alakar labarinta da matsalata ba.
a sani, ina shimfida miki abun ne ta yadda zaki fahimta da kyau, tana tsoron kar mijinta yayi aure ya rabu da ita, ko kuma yan'uwan mijin da mijin su juya mata baya kamar yadda suka fara yi mata yanzu, sanadin hakan ya saka ta same ni tana kuka tana neman taimako...

Ban bari ya karasa ba, na tari numfashinsa.
a ka takaita labarin wata kila zan fi fahimta, domin ba labarin mijin Jamila ko yan'uwanta ko ita kanta ne yake gabana ba
Ya sauke ajiyar zuciya ya gyara zamansa.
na son na kai ki a gabar da zan taimake ki ne.

Na kawo mata shawarwari daban daban sai dai ta nuna min mijinta irin mazan nan masu akida ba lallai ne ya yarda da abun da zata gabatar masa ba, ko kuma ni na gabatar masa, daga karshe sai muka cin ma wata matsaya ko kuma na ce mafita ni da ita, sai ta fara yin laulauyi na karya da aka je asibiti sai na auna cikin na yi ma mijinta bushara cewar tana dauke da juna biyu, sanadin hakan ya fasa nenan auren da yake, yan'uwan mijin kuma suka dawo suna kaunarta, aka yi ya tafiya a haka, na yi mata allurar da zata hana period dinta zuwa, lokacin da cikin ya kai matakin girma kuma sai na bata magunguna da allurar da duk ya kamata ayi mata cikin ya kumbura yanzu idan kika ganta zaki dauka cikin na gaske ne, alhalin babu komai a ciki sai iska, amman har hoto na yi mata na bata ta nuna ma mijinta cewar mace zata haifa, sai dai banbancinki da ita tana wata na tara ne, ke kuma kina wata na takwas
i ban gane wannan labarin ba
Na fada ina masa kallon rashin fahimta da kuma mamaki a lokaci daya.
abar ce zan kaiki a yanzu, mun shirya ni da ita cewar idan zata haihu zamu samu wanda ta haihu a lokacin sai ta bata danta a matsayin danta
e kake kokarin fada min?

Sai ya jingina da kujerar da yake zaune.
dan kin shirya cigaba da rayuwa da mijinki, kin shirya ceton rayuwarsa, zamu biya kudin aiki zamu dauki nauyin duk wata dawainiya tasa har sai ya warke bisa yarjeje ni da sa hannu cewar abun da zaki haifa na Jamila ne, zamu yi hakan a gaban sheidu kamar lauyanta ni ke kuma zamu baki copy yarjejeniyar mu dauki dayan copy kuma bisa sharadin cewar ba zaki taba karya alkawarinmu ba
Na mike tsaye da sauri tsoro ya kamani, a take jikina ya fara rawa.
i kuma na yi yaya?
amu baki matacce wanda zaki shaidawa duniya da yan'uwanki cewar abun da kika haifa be zo da rai ba
nya kasan darajar
a?

Ka taba haihu?

Miyasa ba zaka ce matarka ta bata nata ba?

Ka san wahalar daukar ciki tun yana wata daya har a haife?
Chapter 27 · 0% Book details