← Book details Ciwon So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 134

Sashe 47

Ciwon So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ina son na zauna kusa da Zahra ko dan na rika sanin halin da take ciki
na nan ana bincikawa yawancin wadanda ake samu bana kusa da gidansu ba ne, amman akwai wani gida da aka fara gini aka bari shi kuma be da girma sosai gaskia
dan zai yiyu a siye na kusa da shi mana sai a hada in ya so sai a ninka musu, idan kuma haka be samu ba sai a siye shi nan ayi gidan sama
mman kai kana ganin zaka iya zama a nan Zahra bata gane ka
a zan taba bari ka gane, i just want to be close to her
hikenan zan bincika mana, Allah yasa Mai Martaba ya barka ka aureta kar wata matsala ta ta so kuma
o no kar ma kasa wannan a ranka, kar zuciyarka ta sake raya maka zan rasa Zahra
a fata nake ba, kawai ina sasashe ne
o ka daina wannan hasashen
Ya sauke wayarsa cike da rashin jindadin kalamin da Sauban yayi.

ZAHRA POV.

TWO WEEKS LATER...

Wani irin murdawa na ji marata na yi ta saba min haka sai dai
ba irin na yau ba yau kan ta tsananta min sosai, kusan jin nake kamar bayana zai balle gabana kuma kamar zai zazzago kasa ya cire gaba daya, a wahala na rarrafo zan fito saboda fitsarin da nake ji sai Mama ta rike ni.
na zaki?
itsari zan yi
a ba a hawan shadda (Masai) idan ana nakuda balle gashi har kin fara zubar da jini, ki yi fitsarin a nan zan gyara
Tana gama fadar hakan ta tashi ta cire ledar tsakar dakin ta maida gefe daya ta dauko wani katon tsohon zane ta shimfida.
i fitsarin ki dawo nan ki zauna
Na saki fitsarin a nan Mama ta dauko ruwa zata min tsarko na rike da sauri na karba na yi tsarkina ina ta karewa kar Mama ta gan ni, da taimakonta na isa gurin da ta shimfida min zanen na kwanta, sai tace na tashi zaune na bude kafafuwana.
a ni ba zan bude kafafuwan ba haba Mama ai da kunya?
unya?

Ni na haife ki fa?

Kuma ranar haihu mace har tana jin kunya ne?

Ai sai daga baya dai ko?
i dai gaskiya ba zan iya ba, ni tafi dakinki zan haihu da kaina
Murmushi ta yi.
i ko da sauran nakuda bata taso miki gaba daya ba shiyasa har kika da bakin fadin haka
Haka ne kuwa duk wani rufe kafafuwa da nake ina jin kunyar Mama na farko farko ne ina jin azabar ta asali ban san lokacin da na walgare kafafuwan ba na kwala ihu.
ama ciwo nake ji na shiga uku
Na fada ina jin wani irin azaba da ban san yadda zan kwatanta ba, a take na ji fitsarin sun kara taruwa a marata.
itsari nake ji
i yi su a nan, kuma ki rika ambaton Allah
Na yi yunkurin fitsarin sai na ji sun ki fitowa ashe ba fitsari ba ne tsabar azabar ciwo ne, na kai hannu na cire dankwalin kaina saboda wani zafi da nake jin ya baibaiye jikina, na kai hannu na fara tsife kitson dake kaina can kuma na mari cinyata.
nnalillahi Wa'inna Ilaihirraji'un Mama mutuwa zan yi, mama ku cire min abun nan Mama ki kira likita Mama ki kira shi ki fada masa ina nan ina shan azaba wayyo Allah
i bari sai idan kin
haihu sai a kira shi
a zan bari ba ba zan bari ba, ai ba jikinki ba ne baki san yadda nake ji ba, cikina fashewa zai yi marata ciwo take kasana ma barkewa zai yi, wayyo Allah marata
Murmushi kawai Mama ta yi ta cigaba da tufa min addu'a a kofi bayan ta gama ta ba ni na sha, ta shafa min ragowar a cikina.
llah ya sauke ki lafiya, ki yi ta ambaton Allah
o wai ba addu'a kika ga ina yi ba, ni dai ki kira likita wayyo Babana
Na fada da karfi ina kuka ji nake kamar na tashi na tafi har asibitin gurin likitan, wayarta ta dauka ta kira Yaya Maryam ta sanar da ita halin da muke ciki bata gama wayarba amai ya cika min baki na fara amai kamar ba gobe, lokacin na tabbatar da uwa uwa ce
babu kyama ta rike ni tana ta tausayina idan naje rufe kafafuwana sai ta bude, mikewa na yi tsari na fara yawo cikin dakin ina karanta duk addu'ar da ta zo kaina.
anarukuna bardan wassalamu ala ibrahim....

Ya hayyu ya kayyun...

Ya Allah na ya gwanina Allah ka kawo min sauki, wannan mutuwa da zan yi a yau ka kawo min saukinta
Mama ta rike ni ta zaunar sai na kai kaina na leka ina kallon yadda na komai ya canja.
ama haka kika ji da zaki haifi Zahra?

Mama ki yafe min Mama na yafe miki, da na san haka abun nan yake da ban yarda na raini cikin nan ba, na shiga uku na lalace, wayyo duniya wayyo lahira
Sai da na yi awa daya a haka sannan Yaya Maryam ta zo, tana isowa ta sanar da Mama tare take da Dr Hamid sai na mike tsaye jiki ba tufafi zan fita na tafi waje gurin Dr Hamid din sai da Mama ta rike ni.
e babu tufafi a jikin ba
ama ina ruwana da tufafi wai?

Kowa ya gan ni mana, ke dai baki san yadda nake ji ba
Na fada ina son na kwace kaina domin jin nake kamar da naje gurin likitan cire min cikin zai yi an samu sukuni.

Yaya Maryam ta daura min zane ta saka min Hijab.
ace a fito da ita ba a nan zata haihu ba?
o ina zai kaita?
i dai be fada min ba, amman yace na fito da ita mu tafi wani gurin
o kuwa da ni za a tafi, ba zan bari ku tafi ku ka dai ba da yata a wannan hali
A take na sako fitsari mai tare da jini, Mama ta rika ni ta dayan bangaren Yaya Maryam ta rika dayan bangaren muka fito sai da aka sani ni motar Dr Hamid din sannan Mama ta koma ta rufe gidan sai Dr ya kalli Yaya Maryam.
a ita zamu je?

Kamar yace wani abu sai kuma ya zagaya ya shiga mazaunin direba Mama ta shiga baya tare da ni yaja motar kamar zai tashi sama, kamin mu isa inda zai kai ni na fara rokon Mama yafiya ina bar mata wasiya.
ahra hakuri ake duk haka muka ji
Yaya Maryam ta fada ban san lokacin da na kai mata duka ba.
arya kike ba haka kika ji ba, muguwa ni kadai na san me nake ji, Wayyo Babana Wayyo Deen
Mama addu'a kawai take tana tofa min, wata private hospital muka nufa, ko da muka isa mun tararda an aje kujerar daukar marar lafiya, da alama ya shiryawa komai tun kamin a kawo ni, Mama da Yaya Maryam suka dora ni kan kujerar wata nurse ta turawa da gudunta, su Mama suna biye, wani katon daki aka shiga da ni, aka dora ni saman gado aka janyo wani karfe aka dora kafafuwana a kai.

Matar ta cire zane na ta dauko wani ta dora ta rufe min kafafuwan zuwa cikina, sai ga Dr Hamid ya shigo cikin shiga irinta ta masu shiga tiyata ya rufe fuskarsa da mask hannayensa kuma da safa, ya daura drip ya saka min a hannu sannan yayi allurar a cikin ruwa, ya kalli Mama da Yaya Maryam yace su fita.
u fita please
a ni babu inda zan je sai ta haihu
ama babu abunda zai faru, dan Allah ki fita dan ma yana private hospital ne da asibitin gwannati ce ba za a bari ma ku shigo nan ba, dan Allah ki fita
Daker da sudin goshi Yaya Maryam da nurse din suka lallaba Mama ta fita bayan ta bugawa Dr Hamid warning cewar idan na mutu ta rantse masa da Allah sai ta yi shari'a da shi.

Hannunsa ya fara saka min a ciki sai wani ruwa ya fashe da karfi ya watso masa har a jiki da karfi yayi tsalle yayi baya sai dai haka be hana ruwan bata masa jiki ba.
annu sannu
Shi ne abun da yake ta fada.
i yi nishi
a kare nishin
e kare ba daure ki yi kin ga kan babynki yana kusa na fara jinsa
Sai na yunkuro zan kai hannu na taba ni ma naji abun da ya ji sai nurse din ta maida ni ta kwantar.
ush Zahra ki yi nishi
Na yi nishin sai na ji kan wani abu ya tsaya min a gaba kamar ya tare kofar, ga wani azaba da nake ji a gurin kamar an yanka ni.
a kyau yi nishi
Na sake gwada nishin sai na ji ba zan iya ba, gaba daya na gaji karfina ya kare, sai na kwanta a gadon kamar tsumma, duk wata dabara da Dr zai min na yi nishi yayi idan na yunkura na yi nishin sai na ji ba zan iya ba ko kuma na yi kadan.
can't breathe I'm so weak
Na furta ina tuna yadda Deen yace zai zo ya rike ni idan zan haihu, kuka nake sosai, can sai ga wani irin karfi ya zo min na nisa sai na ji abu ya fara fitowa ashe nishin haihuwa ba mutum yake yinsa karan kansa ba Allah ne yake kawo masa wannan karfin, ina sake nisawa a karo na biyu sai kukan abun da na haifa hawaye na sauko min Dr ya saka hannu ya karasa cire shi ya dago shi haka nan da jini ya doro min saman kirji.
in haifi
a namiji Zahra Congratulations
Sai na fashe da wani irin kuka marar sauti ina kallon yadda idonsa yake rufe yana ta rusar kuka, fari ni sol kasancewata ni da mahaifinsa duka farare ne, sai dai ba zan iya shaida waya biyo ba domin babu kamanin kowa a fuskarsa, sai dai kyakkyawa ne mai dogon hanci sosai.
Chapter 47 · 0% Book details