← Book details Ciwon So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 107 OF 134

Sashe 107

Ciwon So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Idan kuma muka fita tare wani ya nuna yana so na sai yace musu ina da miji, idan kuma na kawo masa labarin samarina sai yayi ta fada da Ammy yana cewa ta gani ta gani ko zata ja masa matsala, kalamin Ammy daya a kullum na tsaya na maida hankali akan karatuna musamman da yake ina ajin karshe a makarantar secondary, duk wani tsadadden tufafi da zaka gani a jikin Ammy ko Abiey ya siya min, babu abun da zan je wa Ammy da shi ba zata karba min ba, har Dr Zainab da take yayarsa tana yi min hidima ta nuna min so saboda Abiey.

A lokacin da Deen ya kura da abun ya fara yawa sai ya taka min burki...
12/28/22, 11:06 - Buhainat: Hana ni zuwa gidan da Deen yayi sai ya yanke min jindadi, shi kansa Abiey sai ya fara damuwa, da kansa ya aiko Ammy ta bincika masa lafiyata, Mama ta sanar da ita lafiyata kalau yayana ya dakatar da ni daga fita ko'ina ne, har ma ta kara da nata cewar bata son yadda nake da rawar kai ina shigewa mutane.
i kiriniya ce kawai take damun Zahra amman bata da wani abun dake nuna rashin tarbiya a tare da ita, idan ba Zahra ta manta ba ko zama kusa da namiji bata yi sai dai tana iya mika hannu ta karbi abu ko kuma ta shiga a inda mazan suke bata dauki wannan a bakin komai ba, kin yi wa yarki tarbiya mai kyau, sai dai hali ne ko da yadda Allah ya shimfida masa nasa, kuma ina fahimtar haka na taba da ke, na yaba sosai da yadda kika tarbiyantar da yarki, sauran sai mu barwa Allah
Mama ta jidadin kalaman Ammy sosai, daman burinta a kullum kar na watsar da tarbiyar da tayi mini, ko zuwan da nake a gidansu Abiey tana yawan nanata min na kama kaina na rike mutuncina, a nan Ammy ke sanar da ni cewar za su koma gidansu da aka gama gyara kuma tana fatar idan zata koma ni da Mama da sauran makotan da bata sani ba za su mu rakata kuma zumunci zai daure, sam ban jidadin wannan maganar ta Ammy ba domin ina ganin zata yi nisa da ni.

Daga lokacin sai na fara satar kafa ina zuwa gidan, ina ta nunawa Ammy da Abiey zan yi kewarsu idan suka bar unguwar, sai Ammy tace ke da nake son iyayenki su mallaka mana ke ki dawo tare da mu, sai dai ban fahimci abun da take nufi ba, sai dai na ce mata ai Mama ba zata yarda ta ba ni ba, ko ma ta yarda Deen ba zai bari ba.

A lokacin da Deen ya gane na sake maida hankali a gidan, sai ya zaunar da ni yana karanta min cewar Abiey ba zai taba aurena ba, domin su yayan manya basa auren yayan talakawa musamman ma shi da yake sanannen mutum da duniya ta shaide shi, sai dai na tabbatar masa da cewar ba soyayya ce tsakanina da Abiey ba, amman ya kasa yarda.

Ranar da Ammy suka koma sabon gidanmu na yi kuka sosai kamar zai cire ido, a tunanin ba zan kasance da Ammy kamar da ba, ashe abun ba haka yake domin kuwa bayan tarewarsu a sabon gidan sai wata kalar shakuwa da aminta da shiga tsakanina da Ammy, idan zan tafi islamiya sai na sa ci kafa na tafi unguwar ina isa Ammy zata ba da kudin Napep na biya wanda ya kai ni, idan kuma na tashi komawa sai a kai ni da mota wani lokacin direbanta yake kai ni wani sa'in kuma Abiey zai maida ni gida, idan yayi min siyayya sai na boye ba zan bari Mama ta gani ba saboda kar ta yi min fada.

Wata rana bayan na je can Abiey ya dawo da ni ya sauke ni a kusa da Islamiyar mu ashe Deen na gurin daman yana zargin ba makaranta nake zuwa ba.

Tun daga gurin makarantar ya fara dukana har cikin gidanmu a ranar Deen yayi min dukan da sai da ya karya ni, Mama ta yi fushi sosai fushin da kawar da kawaicin da take masa ya saka ta gargadeshi cewar kar ya sake saka min hannu a jiki, ranta ya bace sosai domin duka yayi min wanda ya saka yan'unguwa suka yi zargin ya kamani da wani ne, cikin kankanen lokaci sunana ya bace.

Da aka kwana biyu Ammy bata gan ni ba sai ta zo da kanta domin duba ni, a lokacin ne Mama ta fada mata ba zan sake zuwa gidan ba, kuma ba jidadin zuwan da nake ba a gidan ba da sunan zuwa makaranta amman Ammy bata taba koroni ba.

Ran Ammy ya bace sosai irin bacin da ban yi zaton zata sake zuwa gidan ba.

Daga baya Deen ya zo ya bawa Mama da ni hakurin abun da ya faru, sai ya koma yana kula da ni kamar dai, sai dai hakan be saka Mama sake masa fuska kamar yadda ta saba ba, a lokacin da na fara warkewa ina dan fita na taka kafar Dr Zainab yayar Abiey ta zo duba ni, take min albishir da wata maganar da ta kusan ruda tunanina wai Abiey zai aiko a tambaya masa aurena, sai dai tace min sirri ne kar na fadawa kowa.

A ranar na wuni a tunani daman Abiey so na yake ko kuma dai abun da ya faru ne ya saka shi yin haka, amman ban iya boye jindadina ba Mama sai da ta fahimci ina cikin farinciki a ranar, sai dai ban fada mata komai ba.

Ba tabbatar da gaske Dr Zainab take ba har sai da Baba ya shigo gidan cikin wani yanayi mai kama da farinciki kuma ba farincikin ba, domin a ranar ba girkin Mama ne ba, jikinsa na dan rawa, sai da ya kalleni ya jinjina kai har sau uku sannan ya natsu ya labartawa Mama wai.

Wasu mutame masu daraja daga gidan sarauta sun same shi da zancen nemawa
ansu auren Zahra.

Mama ta daki kirji tana tambayar wace Zahrar kuma su waye domin bata taba sanin Abiey
an Mai Martaba ba ne sai a yau, ni ce kawai na sani ni ma kuma sanin da na yi ban dauka
ansa na cikinsa ba ne domin babu wani good relationship a tsakaninsu irin na uba da
aman Abiey
an Mai Martaba ne?

Shi ne abun da Mama ta tambaya ni dai kai kawai na iya daga mata farincikin dake raina ya isa ya hana duk wani yaki da za'a gudanar a duniyar nan a nan gaba, ba wai ina son Abiey saboda yana da kudi ko dan yana dan manyan mutane ba, sai dan ra'ayina da nasa da nake ganin kamar ya zo daya, kuma yana biyewa shirme ne idan ma shirmen ne, yana nuna kulawa baya taba gajiya da duk wani abu na bacin rai da zan yi masa, wani lokacin idan na yi ba daidai ba zai nuna min cikin hikima, yace min Zahra ba haka ake ba kaza ya kamata ki yi cikin kwanciyar hankali babu fada, idan kuma ya gan ni da wani ba zai min fada miyasa nake tsayuwa da maza ba sai dai shi ya fadawa mazan cewar ina da miji ba kamar Deen dake dukana ba.
a fada musu zan tambayi yarinyar idan ta amince sai na mayar musu da amsa ranar irin ta yau
Abun da Baba ya fada kenan sannan ya tambaye ni ko ina son Abiey babu bata lokaci na ce masa ina sonsa, ba dan na tabbatar ina sonsa a lokacin ba sai dan ina son kasance tare da shi kuma ina son hallayarsa da ta Ammy.

A ranar Deen ya shigo gidan ya gaisa da Mama idonsa akaina duk wani motsi da zan yi baya dauke ido akaina, da zai fita sai ya bukaci na rakashi zuwa kofar gida, a can ya fara karantar min wadansu labarai da suka sanyaya min guiwa, wai Abiey yayi haka ne kawai saboda ya zamu damar shiga jikina kuma da zarar ya samu abun da yake so zai guje ni, shi dai yana min tsoron ranar da Abiey zai kunyata.

Labaransa ba su tasirin hana ni amincewa ba, sai dai na kagagara na ga Abiey domin na tambaye shi ko zai guje min amman samu dama ba saboda ban samu saka Abiey a ido ba sai a ranar da aka yi mana baiko.

A ranar unguwar mu ta dauka domin kayan baikon da aka kawo irin masu janyo magana ne da tseguma abu ne da ba kasafai ake ganinsa a gidajen talakawa ba sai yayan manya.

Mama ta boyewa kowa wanda zan aura sai dai ko da wanda yake fada har da masu cewar tsoho aka bawa ni saboda an ga kudi a tunaninsa idan ba tsoho ba ne babu abun da zai saka mu boye ko waye.

A ranar da aka yi min baikon Deen ya wuni yana bachi kamar matacce tun daga lokacin kuma be saka lafiya ba, daga ni har Mama muka rasa gane abun da yake damunsa, idan muka tambayi Baba sai yace mana ulcer ce.

Daga lokacin muka fara cin arzikin Ammy, ta saka aka gyara mana gidanmu inda gini yayi kadan aka kara inda ke bukar gambu aka saka sannan aka yi mana tayis ko'ina a gidan.

Idan Abiey zai zo hira zai so a bakar mota saboda kawaice idon mutane wani lokacin kuma sai na tafi gidan Yaya Maryam a can zamu yi hira.
Chapter 107 · 0% Book details