← Book details Ciwon So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 69 OF 134

Sashe 69

Ciwon So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai da ya waiga ko'ina na falon ya tabbatar mu ne kadai a falon sannan yayi kasa da murya ya ce.
r Zainab ta mince ta karbi kudin kuma ta ba ni takardun yau zan maida nata da su, bayan na canja shiyasa na ce ni da kaina zan miki wannan albishir din kin ga sai ki kwantar da hankalinki ki sake yadda kike so a yanzu
Ya san kwanciyar hankalin nawa domin wannan maganar na daya cikin abun da ya kwantar min da hankali a yanzu, fargaba be wuce ace watan tonuwar asirina ya kama ba, amman amincewar da ta yi zai sanya salama a zukantan mu, sai dai ban san miya na kasa murna da haka ba ina ta jin kamar ba mu aikata abu mai kyau ba.
o ba ki yi farinciki ba ne Zahra?
a yi murna mana na ji dadi
Na fada ba domin na ji dadin ba sai domin na kare kaina, idon Hajiya Jamila yana kaina wani kalar kallo take min da ban san na minene ba, har sai da na soma tsawalla ina unkurin tashi na musu sallama Dr Hamid ya riga ni.
ari na tafi saboda ina da aiki da yawa yau kuma ya kamata na maida takardun hannun Dr Zainab kamin lokacin ya kure
mman Yaya da zaka dan dakatar da zuwa domin na kura idon Hubby kamar yana kan mu bana son ya kula da yawan zuwanka ko kuma yawan kebewa da Zahra
Dr Hamid ya kalleta.
a miki wata maganar ne?
a lura dai na yi da hakan, ya kamata mu yi taka tsantsan dukanmu
eah you're right, zan kiyaye see you later
Ya karasa yana kallona tare da sakar min murmushi, kofar da Dr Hamid ya rufe bayan ya fita falon bana tunanin ta gama rufuwa aka bude yar'uwarta dake can kusa da stairs.

Mijin Hajiya Jamila ne sanye da kananan kaya da suka karbe domin ni ma kaina sai da na yaba yadda kyaushi ya kara bayyana a tufafi balle kuma ita da take matarshi.

Da sauri ta mike tsaye ta nufi shi sai dai hakan be hana shi barinta ya karaso gurin Set din kujerun da muke zaune ba zauna a kujerar da Dr Hamid ya tashi, cikin hanzari na mike tsaye ina mika masa gaisuwa.
na kwana Yallabai
n tashi lafiya
afiya kalau
Na juya da zimmar ficewa sai ya kira ni.
ahra
Na juyo sai dai ban yarda na kalleshi ba, duk kuwa da jikina ya ba ni cewar shi din kallona yake.
adam me kika shirya mana na breakfast?

Hajiya Jamila da a yanzu ta karaso kusa da mijina ta amsa tana kallon yadda yake kallona.
un makara ba mu barka da wuri ba, shiyasa ban dora komai ba Ummiter ma yau ba zata je aiki ba kai ma i thought bachi kake yi shiyasa ban girka komai ba, amman zan dora yanzu
Ya daga mata hannu yana kallona ni ma kallonshi nake a munafunce ina dauke ido.
o no ya kamata ki huta, bari Zahra ta shirya mana abun karyawa, Zahra kin iya girki?

A take ido suka rain fata a duniyar nan ba abun da na tsana kamar ace min na yi girki ba dan bana son girkin ba sai dan ban iya ba, gudun na kunyata kaina ya saka na daga kaina har sau uku a na hudu na samu na iya furta.
h na iya
ood the kitchen is yours now ki girka mana farfesu sai ki soya mana dankali bana cin kwai amman Matata tana ci ke ma idan kina ra'ayi zaki iya soyawa Ummiter ma tana so, and Wife ina ganin a maida girkin su tare da na mu gaba daya ba dole sai sun girka na su dabam ba
Karashe maganar yayi yana kallonta kamar mai neman shawara.
o ba zan iya ba, girkin mutum uku na ya nake yinsa balle na mutun biyar?

Already ka zuba musu abin ci a store to miye na neman a hade abinci da masu gida?
dan ba zaki iya ba Zahra sai ta cigaba da girka mana
Ni kaina mamakinshi na ke balle kuma ita da mamakin ya bayyana a fuskarta.
xcuse me, Hubby baka cin abincin masu aiki fa?

Kallona yayi sai na yi saurin sauke ido kasa ina jin bugawar gaba.
annan tana da tsabta kuma na ga kin aminta da ita, daman ni kazanta ce bana so a kula da tsabta kin ji Zahra
Na daga mashi kai sannan na juya na nufi kofa sai ya sake kirana ina juyowa ya nuna min kitchen.
i girka mana abu na ce
Kamar a rikice na nufi kitchen din ina jin wani abu mai kama da kuka na neman hanya a idona, katon kitchen da komai a akwai a ciki wani abun ma ban san amfaninshi ba ban kuma san abun da ake da shi ba balle na san yadda ake kunnawa ko kashewa, ba abun da ya tsaya min a rai kamar dafa farfesu, har ga Allah ban san yadda ake yin farfasu ba domin ban taba yi ba, a gidan Ammy ma na ga ana yi ban tana tsayawa na kalli yadda ake ba, haka ma Mama da take girkawa wani lokacin ban san yadda take ba sai dai idan ta girka ta na ci.
arfesun ma na miye zan yi?

Na tambaya kaina da muryar da kuka ke son ya ci karfinta, dankalin na fara gyarawa na kunna gas sannan na dora fraying pan na bude cabinet ina dubawa sai ko zan ga mai, daker na gano inda take aje mai na dauka an zuba, da na lura ba rawa ba tumame sai na cire hijab dina na aje gefe daya na takarkade ina ta soya dankalin sai da na yi kwasar farko, sannan na leka falon ban ga kowa ba daga ita Hajiyar uwar izza har mijin nata, sai dai idona ya sauka akan wayar dake hannun kujerar da Alhaji Bashir ya zauna, kafafuwan na sauko na fito daga kitchen din ina kallon stairs na karaso gurin wayar kamar na kai hannu na dauka sai kuma tsoro ya kamani, na juya na koma kitchen din cikin tsanda.
dan ban dauko wayar ba kuma da me zan yi farfesun?

Ko kuma na ce musu ba iya ba?

Ai kuma dai da kunya ace ban iya ba, to ko dai na tafi na dauko tawa wayar?

Kuma ai ba ni da data, ko kyma na kira Mama ta zo ta girka musu?

Haka dai na yi ta magana da kaina, saga karshe na yanke shawarar dauko wayar da nake kyautata zaton ta Alhaji Bashir din ce ya manta na duba yadda ake farfesun.

Kamar wanda zata yi sata haka na dawo falon ina ta waige waige har na samu nasarar kai hannu na dauki wayar, tun da nake a rayuwata ban taba daukar wayar na ji tana neman subucewa a hannuna ba irin wannan saboda sulbin da take da shi, lallai kayan kamfani daban da na shago abun manya na manya ne a duk inda yake, maida kofar kitchen din na yi na rufe a hankali ba tare da na bari kara ta fito ba, sannan na taba wayar hoton Amir ne a gaban wayar yana bachi, a take tausayin Alhaji Bashir ya kamani ,domin yana kallon Amir a matsayin
anshi ne alhalin ba jininshi ba ne, a yanzu kam ina jin rashin kyautawa a abun da na aikata, ko da yake ni dole ce ta saka amman Hajiya Jamila ta yaudari mijinta yaudara mai girma kuma yaudarar da babu wanda zai san gaskiya sai Allah.

Na raba kaina da
ana zai girma be san ni a matsayin mahaifiyarshi ba, ban san Mama a matsayin kakarshi ba sai wasu familyn na dabam a matsayin familynshi, anya hakkin yaron nan ba zai kamani ba?

Da kuma amanar Alhaji Bashir din na hada baki da ni a zalinci mutun da na lura babu komai a tare da shi sai alheri da son kyautatawa?

Na share hawayen da suka zubo miki na nisa ina taushe wani numfashi mai wuyar zama a masarafarsa.
an yi da mugun nufi ba Amir, kuma ban aikata hakan saboda bana sonka ba, sai dai na ceto rayuwar mahaifinka rayuwar da bata tsaya ba
Na aje wayar na dora hannuna akan sink hawaye wasu na rigan wasu sauko min, ina matukar jin kaunar yarona kalaman da Deen ya taba yi min da kuma wasikar da na karanta a gidan Hajiya suka tsaya min a rai.
i kula min da abun da zaki haifa ko da bana raye ki tarbiyantar da shi
arki tsani yayana saboda abun da na aikata
Kuka na yi sosai sannan na share hawayena na wanke hannuna da fuskata a jikin fanfon kitchen ko na kwashe dankalin daya soya, na rage wutar gas din na maida hankalina gurin wayar sai a lokacin tunanin pin din wayar ya zo a kai, ga mamakina ina taba samn wayar sai ta bude ashe babu password a jiki, ba karamin dadi hakan yayi min ba a take na kunna data wayar na saka wayar a silent na shiga cikin ina dubawa har na gano YouTube, kai tsaye na shiga na rubuta farfesu, a take aka nuna min video kala kala, farfesun kaza na kifi na kan garo na kayan ciki and so on.

Freezer na nufa na bude na ina dubawa, babu komai a cikin sai kayan marmari, rufeta na yi na nufi dayar dake kwance na bude sai na yi arba da nama kala kala.
Chapter 69 · 0% Book details