← Book details Ciwon So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 73 OF 134

Sashe 73

Ciwon So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai da ya wuce na je na shirya Mama ta ba ni kudin Napep tana min nasihar cewar na natsu na daina abun da abun da nake.
ina kallona idan ana dukanki ko kasheki za ayi babu wanda zai ce ayi hakuri, shi kuma idan ya tashi dukan na ki be san yayi miki da sauki ba, ke kuma zaton kike dadi nake ji idan yana dukanki, ko baka son
anka ai baka son ana dukanshi balle kuma kana kaunar abun ka, dan Allah ki zama mai jin magana Zahra
Tana rufe baki Baba ya shigo cikin gidan da sallama, ni da Mama muka amsa masa na karbi kayan hannunshi na kai daki sannan na fito na saka talkamina.
na zata je?
idansu yayarta na aike ta ta karbo min sako
Mama ta fadi haka ne saboda ta kare ni, domin ta san Baba zai iya cewa ba zan je ba.
mman dai kin san halin yarinyar nan, yaushe aka cire nata marin nan ma yanzu kuma zaki aiketa
aba to ai ba dade zan yi ba, kuma ka san ni marainiya ce Baba ya ba ku amana ta yace duk abun da nake so ayi min
Na fada cikin yanayin da ke nuna yana hana ni fitar zan saka masa kuka.
a dadewarce matsalar ba, rashin jin maganar ne matsalarki, kuma ni babanki be bar min amanarki ba ban sani ba dai ko ya barwa Mamanki, hakan kuma ba zai hana idan kika yi laifi na hukuntaki ba ko na saka Yayanku ya hukunta ki
anzu ai na shiryu baba, ba zan sake yin komai ba
oh gamu gani ai, muna nan dake ba sai an yi nisa ba yarinyar nan zata je ta dauko mana abun magana
alam ayi ta mata fatan shiriya, abun da take ba dadi yake min ba kuma yara ne sai da addu'a
oh Allah ya shirya, zuba min ruwanka ki kai min bandaki kamin ki wuce kafar yawo
Na dauki bokitin wanka da sauri na cika shi da ruwa na kai masa bandaki sannan na fice gidan zuciyata fes, rabon da na ga kofar gidan yau kwana tara kenan, sai da na bi ta gidansu Hafsat muka fara shiriricewa a can sannan na fito na kama hanya, ina tafiya na ci karo da yara suna jan mahaukaci ni dai ba mahaukaciya ba ce balle na biye musu hakan kuma be hana mahaukacin biyo ni su suke jan shi amman ni yake bi, Mama ta fada min ba a yi ma mahaukaci gudu hakan yasa ban yi gudu ba duk kuwa da bina da yake sai dai na hade masa fuska saboda kar ya ga dama ta.

Shuuuu na ji saukar bulala mai shegen zafi a bayana, wani tsalle na yi na fashe da kuka kamar na ce masa kara min sai ya kara auna min ta biyu har zuwa ta uku, duken da nake na yi cikinsa na kwashi kafafuwansa na mike tsaye sai gashi a kasa kamin ya tashi na yi hanzarin cire talkamina na kwada masa a kai sannan na juya na ranta a na kare, ina gudu yana bina ni, har muka iso gida da mugun gudu talkamina a hannu na shigo gidan ina fadin.
ahaukaci mahaukaci
Mama ta tsallake kwanon abincin da Baba ke ci ta fada
aki da gudu ta rufe, ni ma dakin na nufa sai dai rufewar da Mama ta yi yasa dole na na shige bandaki daman ya fi kusa, na san Baba da nauyin jiki wata kila be yi hanzarin tashi da wuri ba ne ko kuma mahaukacin ya rike shi oho Allah kadai ya sani, ihunshi kawai na ji yana fadin.
a dubi girman Allah Bawan Allah ka yi hakuri ban maka komai ba, ka dubi rahmar Allah ka yi hakuri ban maka komai, na tuba ka yi hakuri dan Allah wayyo jama'a a kawo agaji
Daker muryarsa take fita da dukan alama shakure wuyan Baba yayi ko kuma ya danne shi, daman mahaukacin irin manyan mazan nan ne masu kirar samudawa.
an Allah ka yi min rai, ni na jaka ba, Zahra ce ba ni ba ne ba a nan gidan ta shigo ba, kalli sama kalli sama gata a can sama tana maka magana, Zahra idan ba ki fito ba sai na halakaki, Malam ka dubi girman Allah ka tafi gata a can bandaki tana maka gwalo, Malam ba a nan ta shigo ba, na rantse da Allah da Al'kur'ane ban san ta, na rantse maka da Allah ban san ta ba, ba yar gidan nan ba ce, shiga uku zai kashe ni, ban maka komai ba, Zahra idan baki fito ba sai auren uwarki ya kare a gidan nan
Ina jin haka na rufe baki daman jikina mazari kawai yake, ruwan wanka da na kai ma Baba dazun kamin na fita na zubar na kife bokitin na daka na taura katangar bandakin daman bandakin mu irin wannan ne da baya da mufi a sama kuma gunin bashi da tsawo sosai domin irin na bayan gida ne dake tsakanin bayan gida da wani bayan gidan daga tsakiya an yi hanyar ruwa, ina hawan ginin na dire ta baya na auna da gudu na fita ta gaban wani gidan na fita ta wata hanyar, gidansu Abiey ya fi kusa hakan yasa ina fitowa kwararon na kwankwasa kofar gidan aka bude.
yoyo Zahra yaushe rabonki da gidan nan
Na watsawa Mai gadin harara na murguda masa baki na wuce cikin gidan kamar wata yar gidan, a bude na tarar da kofar falon sai na aje talkamin da suke hannuna a bakin kofar na shiga da sallama ina haki kana ganina kasan akwai abun da ya faru.
araba da Autata oyoyo na yi missing dinki
Ammy ta ware min hannayenta sai na karasa kusa da ita na rumgume irin side hug din nan, sannan na zauna a kasa.
mmy ya gidan
afiya Kalau Zahra Aliyu yana ta damuna da nemanki, ya damu naje na duba masa ke
mman baki je ba ai
ana son Mamanki ta ga laifina ai, kin ga zata ga kamar mu muke kara dora ki a hanya, kuma abun da yaron nan yayi min ban jidadinshi ba
i yi hakuri Deen haka yake yana da saurin ido sosai, Ammy ina Aliyun?
ana garden yanzun ya gama matsa min Kafafuwana dake ciwo
Na tashi na fice daga falon ba dan na san inda Garden din take ba, sai dan na san abun da ake kira da haka, gurin da nake hango itace na nufa ina shiga na same shi yana waya a daya daga cikin kujerun da suke gurin na zauna ina kallonshi murmushi ne kwance a kyakkyawar fuskarsa gashi fari tass hanci kamar na ara masa idanuwansa da haske sosai gashin kansa ma yayi baki wulik ya kwanta gwanin sha'awa.

Sai da ya gama wayar ya dube ni
ana da kyau Abiey
Na fada masa a bakin gaskiyata domin ko mace na gani mai kyau zan iya fada mata cewar tana da kyau domin ni a gurina fadar haka ba komai ba ne.
a yi kyaunki?
olayata kake ko?

Ya daga min gira daya.
a kike Zahra?

Ina son Ammy taje ta duba min ke amman bata je ba, ta fada min tun tana cikin gidan nan mugun ya fara dukanki ko?

Wallahi yayi sa'a da sai na hukunta shi ko dan abun da yayi miki da Ammy amman Ammy ta hanani daukar mataki
ar da mari ya saka min sai jiya aka cire min, bana zuwa ko'ina yayi min duka sosai
ari kuma?

Wannan mutumen ba shi da kirki duk da dai ban taba ganinshi ba, son ki yake ne?
a Wallahi, babu komai tsakanina da shi
mman yanzu ba a sani ba kika zo gidan nan ko?

Na daga masa kai ina dariya idona ya kai gurin icen mangoro.
biey zaka ciro min mangoro daya
Na kalleshi ashe kallona yake har lokaci be kuma dauke idonsa.
iye?
allonki dadi yake min silly girl, babu ruwanki yadda ta nuna miki haka kike yi i like your style
Na rufe fuskata ina dariya na dade a haka kamin na bude idon still idonsa na kai.
ina da saurin sabo da mutane Zahra, shiyasa mutane suke binki shi kuma wannan mahaukacin yake ta hauka
Kalmar mahaukaci da ya fada ta saka na tuna da mahaukacin da ya biyo ni yanzu, sai na kyalkyale da dariya ba bashi labari shi ma dariyar yayi sosai.
in ja masa kamar yadda kika min, har mafarki sai da na yi bayan na dawo fa
Na cize baki ina kallonsa.
biey ka cire min mangoro daya mana
Wannan karon a shagwabe na yi maganar ina son masa kuka.
kay bari na dauko abun cirewar, ko na kira Haruna mai aiki ya cire miki saboda akwai zuma a gurin sai an yi a hankali
Ya tashi ya fita daga gurin, ni kuma sai zuciyata ta kwadaita min son ganin zumar, sai ko na tashi na karasa gurin icen na daga kai sama ina kallon, katon gidan zuma na gani a gurin.
aaaa
Na fada ina mamaki ashe haka take yin katon guri, kuma Mama ta taba fada min cewar idan aka taba ta tana bin mutane, domin na tabbatar da gaske ne ko karya na dauki katon dutse na jefa mata be kai gurin ba ya fadi sai na sake dauka na sake jefawa haka na yi ta yi har sai da na same ta, aiko sai ta yi runduna ta nufo ni kuma na auna da gudu na fice Garden din amman zumar nan da karfi hali bata fasa bina ba, da gudu na shiga falon Ammy ina fadin
uma zuma zuma...

Abiey dake tsaye ya fadi kwance kamar wanda ya ga yan bindiga, Ammy kuma dake complain din ciwon kafa sai ga ta tsalleke Abiey ta haye stairs da gudunta tabur tabur domin mace ce mai jiki, ta banko kofar dakin gam....
Chapter 73 · 0% Book details