← Book details Ciwon So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 55 OF 134

Sashe 55

Ciwon So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dr Hamid ya aje numfashi a hankali.
e zama lallai ba, saboda nonon ki ba ainahin na haihuwa ba ne sai da aka hada wasu abubuwan sannan ruwan nonon ya zo
o madarar dake saka shi ciwon kiki fa?
aman ba kowane cikin jinjiri ke daukar shan madara ba, kawai mu yi fatan idan ya sha zai samu lafiya ba zai saka shi komai ba
e hakan ke nufi?
ai a rika karbo masa mana, ko kuma ta dawo nan ta zauna har zuwa lokacin da zai fara cin abinci sai a yaye shi
Ta yi wani shu'umin murmushi.
a dan kana dan'uwana ba da sai na ce Zahra hada kai ta yi da kai saboda ta samu abun da take so
iya ta same ni office na mata abun da be kamata na yi mata ba, saboda na samu ta rika nisanta kanta da ni gudun kar ta ja mana matsala, sai dai ganin ba mu da wata mafita ya saka na yi bita da lalama ina tambayar dalilin hakan yasa ta kira shi saboda ta ji lafiyar yaron nan, idan har ya tabbata nonon mahaifiyarsa yake so to dole za a rika ba shi shi domin shi ne rufin asirinmu
an taba ganin jaririn da aka haifa ace idan an bashi nono ko madara yana saka shi ciwon ciki ba sai wannan, waya sani ko wani abu ta yi masa lokacin da ka bar mata shi mutane fa sai Allah zata iya ba shi wani abu ko ta shafa masa
Dr Hamid yayi shiru yana nazari.
ai yiyuwa amman bana tunanin haka
i kam ko da nononta ya ba shi lafiya ba zan yarda ta cigaba da ba shi nono ba
aki iya rasa shi, domin dole ne a dakatar da bashi wannan nonon da madara idan kuma baya cin komai kin san ba zai rayu ba, sannan kin ji yanzu mijinki yana maganar fitar da shi waje, idan kika yi sake aka zurfafa bincike za a iya Mijinki zai iya gano cewar ba
ansa ba ne saboda blood type din yaron nan ba irin na mijinki ba ne, ya kamata ki yi taka tsantsan domin ba ke kadai ce a cikin matsala ba har da ni
Ta daga kanta sama ta sauke ajiyar zuciya.
10/10/22, 19:32 - Buhainat: Ciwon so
10/20/22, 08:02 - Buhainat: Ya saka dayan hannunsa ya dauki daya daga cikin tawul din dake nade a durowar ya goge fuskarsa zuwa kansa, sannan ya fito dayan hannunsa rike da wayar dake jone a kunnensa.
dan ma abun da kake fada haka ne, ai ba wannan hanyar ya kamata ta biyo ba
ata da wata hanyar ne sai wannan a yanayin yadda Yasmin take da kunya da zata iya fitowa kai tsaye ta nuna maka ba, wannan ce kawai damarta kuma kai da kanka ka samar mata ita
an yi dan nasan zai kawo min matsala na, da ace na san Yasmin zata min haka da zan saka sunanta a ciki ba, kuma wannan abun ma ai
rashin kunya ne, zata raba min hankali biyu ni kuma ina son tunani ya tsaya akan Zahra ne kawai
ole ne ka yi taka tsantsan kuma la bi Yasmin a hankali domin idan ka ce zaka mata jan ido zata iya bata lamarin
un kusan kawai a haka ai, matukar ba ta yi abun da na roke ta
mman Abiey kasan zaka iya hadawa biyu?

Ga Zahra ga Yasmin?
onono kasan mata basa son kishiya and i think Zahra tana daga ciki, ko da ma ace tana so ni a karan kaina ba zan iya hada soyayyarta da wata ba
Ya fada yana kallon kanshi a madubi.
ut ka san minenen?

Ni Wallahi at first na dauka kana da feelings akan Yasmin ne
Guntun murmushi yayi.
ani lokacin tana min yanayi da Zahra ta hanyar magana da mu'amala amman hakan ba shi ke nufin ina son Yasmin ba
uddy i hope Zahra zata fahimci wannan soyayyar da kake mata ba tare da ka wahala ba
i ma fatana kenan, sai dai kasan turawa sun ce what come easy won't last and what last won't come easy, Deen ya riga ya bata komai wai lasan mugun nan har cewa yayi ta masa alkawarin ba zata auri wani namijin ba bayan mutuwarsa?
hat!?

Da gaske?

Kai a ina ka ji wannan maganar?
ayarta take fada min
ayarta fa ka ce?

Taya?
es na na je asibiti saboda na yi magana da Dr akan Yasmin sai na samu Zahra a aibitin, ta kusan bata awa hudu ko biyar a gurin tana jiran wani likitada karshe da ya fito ma sai ya rufe ta da fada ita kuma ta fara masa kuka, ban san abun da take nema a gurinsa ba amman dai na fahimci akwai damuwa a tare da ita sosai, a talk to her bata saurareni ba, that's why na je kai tsaye gurin Yayarta at that time na shirya fuskantar duk wani lokaci da yayarta zata min damuwarta ce ta dame ni, na karanci damuwa a idonta sai dai ba lallai ne ta ba ni damar yaye mata damuwar cikin sauki ba, haka yasa na tafi gidan Yayarta na saka aka min sallama da mijinta na fara magana da shi sannan na min izinin ganin matarsa, na zauna na gaisa da ita the first da ya fara fitowa bakinta wai ban ji kunya
ba na zo gurinta bayan duk abun da na yi?

Ya juya ya ba madubin baya.
a ce mata me?
a shimfida mata duk abun da ya faru, kuma na jidadin yadda ta fahimta daman sai da na fara fahimtar da mijinta, a lokacin ne take fada min cewa yace ta masa alkawarin ba zata auri kowa ba bayan ransa, and ya cigaba da mu'amalarta after likitoci sun ce ya kebe kansa, ina mamakin wane irin so yake mata ne?

Wannan ba so ba ne, sam mun dai gode Allah ya mutu da wuri
Sauban yayi dariya.
a cika zafin kishi Gaskiya
t's not about kishi wannan ba so ba ne kai baka gane ba?

Idan yana sonta ai ba zai mata haka ba
llah ya kyauta yanzu dai you got lucky Yayarta ta saurareka, sauran Mamanta da Zahra, sai dai zaka sha wahala kamin Zahra ta fahimta saboda tana son Deen sosai
ometimes Sauban kana abu kamar baka san waye ni ba, taya zaka bude baki kai tsaye ka fada min Zahra taba son Deen sosai, kamin Zahra ta so Deen wa ta fara so?

I'm her first love duk wanda Zahra zata so bayana yake Wallahi tana son Deen ne by force saboda tana ganin ya taimake ta a lokacin da na gujeta bayan kuma shi ya shirya komai
asy Men...

Yanzu yaushe zamu je mu yi mata gaisuwa?
hi ne matsalar ai amman dai zamu je i will call you back
Ya sauke wayar tare da ajiyar zuciyar da har wani zafi take masa saboda Sauban yace Zahra tana son Deen sosai.

Windows din dakinsa ya nufa ya bude yana hango kasan benen wani iska mai dadi na ratsa shi.
ahra bata taba son Deen sama da ni ba never
Ya karasa furucin da karfi, can kuma ya juyo ya fito dakin zuwa dakin Anty a hankali ya tura kofar dakin ya shiga, Anty dake aikin nade wani farin lace ta kalleshi fuskarta da murmushi.
ngon Zahra na Yasmin
Murmushi ne ya cika fuskarsa sai ya ji kamar Anty ta yaye masa damuwarsa saboda kirarin da ta yi masa.
ngon Zahra din dai ya wadatar
ta Yasmin din ta fasa ne?

Wani guntun murmushi ya yi mai hade da mamaki.
nty ya kike magana kamar ita ce namiji ni ne mace
matsayin da kake a yanzu ai kai ne mace ita ce namiji domin idan har bata ce ta fasa auren ba, kasan Mai Martaba ba zai aminta matsala ta fito daga gurinka ba, kuma zai dauka kana wasa da hankalinsa bayan an je an tambaya aure sai kuma ka ce ba ka son yarinya a yanzu, kar fa ka manta wannan ne karo na farko da Mai Martaba ya nuna damuwarsa akan lamarin ka har ya shiga ciki, aiko ka ga wannan amaryar mai tsada ce
a yi magana da ita tun shekaranjiya kuma na samu Dr ita na mata magana na san zata yi mata magana
auna Abiey
Ya zauna yana kallonta.
ata Dr ko Ammy ko ni ko Momy ba za mu iya canja ra'ayin Yasmin akanka ba matukar tana sonka, amman kai zaka iya canja ra'ayinta ko da kuwa tana sonka
nty na yi magana da ita, kuma ina tunanin ta fahimta in dai ba jan ido take son na yi mata ba
a maganar jan ido ka zaunar da ita ka fahimta da ita cikin hikima ku yi magana ta fahimta ta yadda zata fahimce ka kai ma kuma ka fahimce ta, a tunani zata yi ta amsa maka da to ne kawai amman ba zata taba aikata hakan ba
hikenan zan sake magana da ita, amman shi ne na karshe idan ba ta yi ba zan samu Mai Martaba da kaina na fada masa cewar bana ra'ayinta
arka aikata haka kara dai ka hakura matsalar ta fito daga gurinta
kay...

Anty yaushe zaki je yi ma Zahra gaisuwa?
are da kai ya kamata mu tafi kafata kafarka kai ma ya kamata ka fara motsawa ai, duk dai be dade da rasuwa ba, amman ya kamata ka fara nuna mata kulawa ta san da cewar har yanzu kana kaunarta
Anty ta fada tana murmushi.
amu je tare da ke da su Aisha sai ku shiga ciki ni zan tsaya daga waje, idan ta ga tana ra'ayin gaisawa da ni zata fito
hikenan to ka saka mana rana
llah ya kai mu
Ya amsa da Ameen, sannan ya mike tsaye yana shafa aljihun wandonsa ya fice daga dakin.

Dakinsa ya koma ya dauki one of his car keys sannan ya nufi downstairs ya sauko yana kallon Aisha dake cin salad ya mayar mata da murmushin da ta yi masa sannan ya nufi kofar.
biey ina zaka je?
Chapter 55 · 0% Book details