← Book details Ciwon So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 108 OF 134

Sashe 108

Ciwon So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wata rana na shirya da kaina na tafi sabon gidansu Abiey, domin a ganina ba komai ba ne na shiga gidan Ammy a yanzu, ban samu Abiey a gidan ba, Ammy ma na same a cikin wani yanayi dake nuna kuka ta yi, tana ta kawar da fuska kar na kalleta amman hakan be hana ni fahimtar tana cikin damuwa ba, na ritsara a dakinta na tsareta da tambayar damuwarta sai ta ki fada min ni kuma na saka kuka domin ganinta a cikin wannan halin ya daga min hankali sosai ina kallon Ammy kamar uwar da ta haife ni, idan ba uwarka ba a gidan wa zaka je kayi yadda kake so ka hau gado ka kwanta ka ci abun da ranka yake so ba za a ce maka komai ba ko a nuna maka yar fuska.

Bayan na sha kuka na koshi Ammy ta kama hannuna tana dariya.
aba Autana ta zo mana
o Ammy me ke damunki?

Idan baki fada min ba zan daina kuka ba ko da na tafi gida, saboda zan rika tunanin kina da wata matsala ne
Sai ta zaunar da ni kusa da ita wasu hawayen na taruwa a idonta.
na da matsala Zahra, matsalar da bata da magani, amman ina jin kamar na samu magani a lokacin da na same ki, saboda hankalin Aliyu yanzu yana gareki, kullum ba shi da magana sai ta ki, Zahra ina son ki zame masa cikakkiyar yar halak karki butulce masa, akwai mata da yawa da suka fi komai ba amman idonsa be sauka akan kowa ba sai ke, kuma zuciyarsa bata natsu da ko wace mace ba sai ke
a miki alkawari Ammy ba zan taba cin amanar Abiey ba
ahra na aikata wani abu, wanda shi ya saka ni kuka a yau kuma yake saka ni kuka a ko wane dare, zan fada miki wannan ne saboda ina son kamar yadda nake son Aliyu ban taba fadawa kowa wannan sirrin ba, amman abu ne da ya dade yana cina kuma ina fatar ba zaki fadawa kowa ba, ke ma zan sanar da ke ne saboda ki kara natsuwa da
ana kuma ki tausayawa masa
A take hankalina ya tashi domin na san duk wani abu da zai saka uba zubar da hawaye a kowane dare ba karamin abu ba ne.
a miki alkawari babu wanda zai ji Ammy
Sai da ta share hawayenta ta sake kama hannayena ta rike sannan ta ce.
ahra karki taba yarda ki mu'amalanci wani da aurenki, kara ki yi shi a waje ko kuma bayan mutuwar aure ba a aure ba, maza basa yafe irin wannan kuma basa mantawa, kuma wannan abun yana shafar yayan da mace zata haifa, ni da Momy wato abokiyar zamana a gidan mahaifin Zainab mun sake aure bayan rasuwar mijinmu, sai dai ni na rigata auren saboda na fita kurciya da kyau, kuma ni na yi sa'ar aurene saboda tsohon manemina ne na aura, ya nuna min so irin wanda Aliyu yake kokarin nuna miki a yanzu, har ta kai baya iya adalci a tsakanina da sauran matansa, wannan ya haddasa fitina kuma zazzafan kishin da ya saka sai da aka ware ni dabam, domin ni ina yaki da bakina ne da anyi min sai na yi magana bana shiru, amman Wallahi ban san hanyar zuwa gidan ko wane boka ba, a lokacin kuma sai hankalinsu ya kara tashi suna ganin kamar zan kara dauke masa hankali ne, sanadin haka sai suka shiga bin bokaye suna kokarin raba ni da mijina, sai kuma suka yi nasara Mai Martaba ya juya min baya irin Juyowar da idan na rabe shi sai ya rika jin warina, idan ya taba ni sai yace jin yake kamar ya taba itace, har tambayar yake miya samu jikinki haka ni kuma ban san miye ba, da abun ya fara yawa sai ya daina zuwa gidana sai dai aiko min da duk wani abun bukata da kuma sakon gaisuwa, bayan ya kaurace min sai na fahimci ina da cikin Aliyu, wanda yace min idan na haife shi sunan mahaifinsa za a saka masa duk kuwa da kasancewar ya hana ko wace mace saka sunan Abban sa amman ni soyayya ta saka ya karya wannan alkawarin da ya dauka.

Wata rana kamar an turo shi sai ya shigo gidan fuska babu annuri ban masa laifin komai
ba,a nan na samu damar sanar masa halin da nake cikin ina ganin kamar samun cikin zai kawar da komai a tsakaninmu ya dawo da zaman lafiyarmu, sai dai a lokacin da na sanar da shi ina dauke da cikin sai ya kasa farinciki a aka danna jindadinsa akan cikin ya gagara nuna min murnarsa, sai Allah ya raba lafiya kawai yace min, a ranar na yi kukan na yi bakinciki sosai, a dayan bangaren kuma na yi farinciki da kyautar da Allah yayi mine.

Na yi bakinciki na kaurace min da yayi ya saka na shiga damuwa sosai har ta kai kanensa da suke uba daya wato Galadima wanda shi kadai yake so na a familyn ya fahimci haka, maganinsu ba tsaya a iya farraku tsakanina da Mai Martaba ba ni ma ya taba tafiyata ya shafi kwakwalwata ya kai bana iya tsayawa na natsu akan wasu abubuwa, ga ciwon kafafuwan da na yi ta neman magani har india na je na kasa samun lafiya.

A cikin Aliyu na wata na biyar zuciya da sheirin shaidan suka debe ni suka na aikata masha'a tare da kanensa da zan iya cewa cilasta ni yayi domin yayi ta lallashina har na amince, ashe ban sani ba wani karin damuwa ce ta fuskanto ni, domin muna a cikin halin da be kamata ba Mai Martaba ya shigo cikin gidan sai dai be shiga inda muke ba sai ya zauna a falo, bayan mun fito muka same shi.

Daga ni har kanensa mutuwa ce kawai ba mu yi ba, amman mun sha kuka na fitar hankali.

Ya saka muka yi masa alkawarin babu wanda zai ji wannan maganar daga ni sai shi sai Allah, saboda idan maganar ta fita zai zama abun magana kuma abun kunya.

Bayan kanenshi ya fita sai ya tambaye ni tsawon yaushe muke tare, na fada masa gaskiya cewar yau ne kawai, amman be yarda ba.
ikinki da ke jikinki zai cigaba da zama a matsayin
ana ko da kuwa ba nawa ba ne, domin jinin
an'uwana jinina ne, kuma babu wanda zai san da wannan maganar, sannan ina son ki sani na sauwake miki ma'ana na sake ki
Cikin tashin hankali na fara bashi hakuri ina kuka ina fada masa cewar cikin dake jikina nasa ne.
dan har zan iya zaman aure da uwar da ta haife ni, to zan sake zaman aure da ke Umaima!

Furuncin da yayi kenan ya banranta kansa da ni, daga lokacin sai na dawo gida gurin iyeyena na zauna, damuwa ta shiga kaina ga kuma sihirin da suka min har ya zama na ina yin abu kamar marar hankali, ana ta nema min magani ana min addu'a cikin iyawar Allah na samu sauki.

Sai Allah ya dauki kaunar Aliyu ya saka min tun yana ciki domin mahaifinsa be taba zuwa duba lafiyata ba bayan ya sake ni, mutane suna ta fadar cewar maganin da suka min ne ya saka ya sake ni kuma ya dauke idona a kaina domin ina fadawa kowa cewar haka nan sidda ya sake ni ba tare da na masa komai ba.

Kamin na haifi Aliyu kanen mahaifinsa yayi hatsarin mota ya rasu, sai ya zamana ni kadai na rayu da wannan bakincikin har zuwa yau.

Bayan na haifi Aliyu Mai Martaba be taba ganin fuskarsa ba be taba aiko masa da komai ba, be taba yi masa komai ba
ana ya girma hannuna yayi wayo na yi masa komai da uwa take yi ma
anta, sai dai kowa ya kalli Aliyu ya san
an Mai Martaba ne domin babu inda ya rago Mai Martaba a kamanin.

A lokacin da Momy ta haifi Yasmin sai muka je barka daga gidanta na dauki
ana na kai shi gidan Mai Martaba, yana kallonsa sai hawaye suka zubo masa, domin be taba saka shi a ido ba sai a ranar.

Sai dai haka be canja tsanar da yake masa ba, be saka ya kula da shi ba, ni kuma ban fasa nunawa
ana shi ne ubansa ba saboda shi ne ubansa din na gaskiya, a kokarinsa na mantawa da ni ya auro mahaifiyarsu Aisha da Narjis, ita kuma ta zo sai ta zama mace mai sanyin hali da son gaskiya, tana ta kokarin sada Aliyu da mahaifinsa sanadin haka har aurenta ya taba mutuwa daga baya aka dawo da ita, amman bata fasa abun da take ba har ta yi nasarar samawa Aliyu
aki a bangarenta ya zamana shi ma zai shiga yayi yadda yake so kamar
an gidan, tun daga lokacin nake matukar kaunar Aliyu kuma nake tausayinsa domin laifina ne ya shafe shi, wata kila har da maganin da abokan zamana suka yi na shiga tsakakaninshi da mahaifinsa amman wannan abun da na aikata shi ma ya shafe shi, ya shafa masa bakin fenti da idan Mai Martaba ya kalleshi yana tuna abin da ya faru.

Da iyayena suka rasu aka raba gidan mu sai na dawo a wannan gidan da tsohon mijina ya bar mine wato na ci gado, na cigaba da kula da kaina da yayana.
Chapter 108 · 0% Book details