← Book details Ciwon So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 134

Sashe 9

Ciwon So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ban taba jin tashin hankali irin na wannan ba, ko a lokacin da aka fasa aurena na farko ban shiga tashin hankali irin wanda nake jin kaina a yanzu ba, balle kuma ace na rasa mijina?
ubhanallahi A'uzubillah ba zan taba rasa Deen ba
Wani bangare na zuciyata mafi alheri yana kore bangaren da ke min wani bakin sashe da ban taba kawowa a raina ba, kamar an yaye min komai a zuciyata haka na ji na daga kaina na saka talkamina da kuzarina na fara takawa ina jin Hajiya na kirana amman ban amsa ta ba, domin na san ba zai wuce tace min na dawo na karya ba.

A titi na na samu Bahijja tsaye ta tsayar da wani mai napep tana magana da shi ban ce mata komai ba na shiga Napep din.
alam zoo road
Juyowa ya yi ya kalleni sai Bahijja ta ce.
aman ita ce matar da zaka dauka
kay Hajiya kudinki 400 ne
uje Malam
Na fada ina jin kamar na tashi sama.
llah ya tsare
Bahijja ta fada, sai na kalleta na dauke ido na maida gurin titin, iyakar kokarin da na yi na kar zuciyata ya ayyana min wani mugun abu ne, sai dai hawaye kam duk kokarina ban iya tare su ba.

Har kusa da kofar gida ya aje ni na fito na ciro kudinsa na mika masa, sai a lokacin na tuna da na manta wayata a gidan Hajiya, naira dari ya bani canji kasancewar dari biyar na mika masa.

Na juya da sauri na karasa kofar gidan ina tabawa sai na jita a rufe, kwankwasa na yi da karfi, ba a amsa min ba kuma ban ji motsin komai ba, a take hankalina ya kara tashi, na sake dukan kofar da karfi sannan na ji amsa.
aye?

Zahra bata nan
Muryarsa da na ji sai tausayinsa da kaunarsa suka kara kama zuciyata, a take idanuwana suka cika da hawaye, wannan karon a hankali na buga kofar.
ahra bata nan waye wai?

A maimakon na amsa masa sai na sake buga kofar, ina jin takun tafiyarsa har zuwa bakin kofar kamin ya bude na jingina da kofar ina jin wani kalar abu na motsa min a zuciyata.
ahra...

Ya furta da mamaki yana kallona kamar yadda nima nake masa wani irin kallo da bana jin na taba masa irinsa a rayuwata, da sauri ya kamo hannuna ya shigo da ni cikin gidan ya sannan ya leka waje ya dawo yana duba lafiyata.
iya faru?

Miyasa kike kuka?

Miya same ki?

Sai na kasa amsa masa sai kallonsa nake hawaye kam sai suka samu muhallin da suka dade suna nema a fuskata, hannanyensa ya saka ya share min hawayen sannan ya juya ya shiga falon be dade ba ya fito rike da wayarsa kamin ya karaso kusa da ni ya fara magana.
iya aka yi ma Zahra?

Miya same ta?

Sai kuma ya yi shiru da alama amsa take ba shi.
aba Hajiya, kuma shi ne aka barta ta zo ita kadai?

Inda wani abu ya same ta fa?

Ya sauke wayar sannan ya karaso kusa da ni, sai na kama hannayenta biyu na rika hannunsa daya na mai bakina na sumbanta.
amuwarka kullum akan Zahra ne Deen, kullum tunaninka nawa ne
Rumgumoni ya yi jikinsa sai na fashe da kuka.
iyasa ka boye min Deen?

Miyasa
aki iya yin kuka a yanzu ai
iyasa ka boye min?

Na tambaya cikin kuka.
aboda damuwa zaki shiga Zahra
Ya amsa da muryar dake nuna hawaye yake.
ow are you feeling now?
etter
Na amsa min yana dago ni jikinsa ya cire katon hijab din sannan ya hade goshina da na shi ya lumshe ido.
love you Deen, zamu samu mafita da yardar Allah zaka warke, duniyar da kake mafarkin zamu gina zamu ginata mu cika gidanmu da yaya dukan abun da muke fata zai tabbata Inshallah
eah Inshallah
Ya furta hawaye na sauko masa, sannan ya kai hannayensa ya rike fuskata ya sumbanci bakina.
o zauna na shirya miki wani abu ki ci, Hajiya ta ce baki ci komai ba
ana jin zan ciya cin komai Deen, ka je dai ka shirya zamu tafi asibiti
Murmushi na gani a fuskarsa sai ya rumgume ni.
ey da kudin da zamu bata a asibiti ai kara mu siye kayan jariri da shi
aboda me?

Idan kai lafiyarka bata da muhimmanci a gurinka ni tana da a gurina
ikitoci sun ce sai na kashe kudi da yawa Zahra kuma babu su
amu yi su, zamu nemo Deen zamu samu da yardar Allah
Dago ni yayi daga kirjinsa yana dariya ya saka yatsansa ya share min hawayena.
iliyoyi ake magana fa, and ....
amu samu Deen ka yarda da ni, zamu samu kuma zaka samu lafiya zaka warke, zamu cigaba da rayuwarmu kamar yadda muka saba
Hannuna ya kama ya nufi cikin falon da ni, sai da ya zaunar da ni sannan ya dawo ya dauki jakar da na bari da Hijab ya shigo da su.
ll this while kana zuwa asibiti Deen?

Kana ciwo amman baka taba nuna min
aboda gudun irin wannan damuwar
Na aje numfashi da karfi irin na wanda kuka ya ci shi sosai.
anzu da ciwon ya kai wani mataki sai dai kawai na farka na ga ka mutu?

Na tsaya jiran mutuwa kai da Hajiya?

To ni na yi yaya?

Yayi shiru yana kallona hawaye sai sauko min suke.
obena tana cikin rayuwarka Deen, idan har zan rasa ka to ina rokon Allah ya dauki rayuwata kamin mutuwarka, ba zan iya rasa ka ba Deen
Wani irin kuka ne ya ci karfina, da sauri ya zo kusa da ni ya zauna ya jani jikinsa ya rumgume yana hawaye.
arki tadawa kanki wani ciwon, kin san kina da ciki kar wani abun ya same ki
Na dago kaina na kalleshi da idanuwana da suka yi ja, fuskata har ta kumbura.
a zame min inuwa a lokacin da wasu suka saka ni a rana, ka yi min rumfa ka rumgume ni a lokacin da wani ya yaudare ni, ka yi min masauki a lokacin da wani ya watsar da ni, ka rufa min asiri a ranar da Abiey ya so ya kunyata ni ni da iyayena, Deen kai ne fitilar haska rayuwata, shim taya kake tunanin zan iya rayuwa idan babu kai?

Miyasa ba zaka tausaya min ka taimaka min gurin neman lafiyarka ba?

Zan iya jure rasa komai Deen amman ban da mijina, na maka alkawari sai na samo kudin nan ko ta halin yaya, zamu nemo kudi Deen kuma zaka warke i promise
Ya sumbanci tsakiyar goshina har sai da na ji sanyin lips dinsa na lumshe ido, hawayen da suke masa zuba suka sauko min saman fuska suka hade da nawa suka sauko min sai na saka hannayena na tare ina jin kamar ba zan iya barin hawayen mijina su zuba a kasa ba.
on't mention his name again...
ar a bada
Na furta idanuwana a lumshe.
ari na samo miki wani abu ki ci
Ina jin lokacin da yake kokarin dagawa sai na rike rigarsa.
umgume ni Deen
Dawowa yayi ya zauna ya rumgume tsam a kirjinsa, sai na ji kamar na saka wuka na fasa kirjinsa na shiga na zauna daidai saitin zuciyarsa.
a isa haka Zahra Mom Zahra
Ya furta min da muryar zolaya sai na yi dariya mai sauti na bude ido na dago ina kallon kyakkyawar fuskarsa, na kai yatsuna cikin nasa ka kwantar da kaina kirjinsa ina jin yadda
umin jikinsa ke ratsa jikina.

ABIEY POV.

Babban dakin taro ne da kama shi sai wanda ya ci ya sha kuma ya tsaya da kafafuwansa, adon da ka yi a holl din abun kallo ne balle kuma yanzu da kwararrun masu decorations suka gyara shi.

Ango Sauban da Amaryarsa Nuratu a muhalinsu da aka yi ma ado na musamman, bukin da ya hada manyan mutane kuma irinsa na farko a iyalin Alhaji Sani Asusu mahaifin Sauba, kusan duk wanda ke gurin fuskarsa da sake take kowa yana farinciki amman ban da Abiey da ya kasa zama a inda ya kamata ya zauna ma, balle har ya sake yayi walwala, sai dai jifa jifa yake sakarwa Sauban murmushi musamman da aka je gurin yi ma amarya da ango niki, sai dai hakan be hana abokinsa fahimtar damuwarsa ba, kana ango kasan yana cikin farinciki but deep down inside his heart yana matukar tausayin abokinsa, domin ya san wannan ranar zata tunawa da Abiey da ranar da aka fasa aurensa ne.

Kusan duk wanda yayi ma ango riki yayi masa wasa sai ya zolayi Abiey domin duk wanda ya san Sauban yo dole ya san Abiey idan kuma ka san Abiey dole ka san Sauba kamar alif da lam haka suke, wasu su ce sauran shi wasu kuma su ce Sauban ya masa wayo ya bar shi, iyakar karfin halin da yake na murmushi ne wanda ya tsaya iya saman fatar bakinsa.

Ana musu hotuna ya fadawa Sauban zai tafi gida ya kwanta domin ba zai iya tsayawa karasa bikin da shi ba.
dan ka je gida tunani zaka rika yi Abiey kara ka zauna a nan cikin mutane
o please
kay Allah ya sauwake
Ya furta sannan ya dago daga gurin ango ya sauko kasan stairs din ya nufi hanyar fita ba tare da ya kula kowa ba, yana fitowa ya ji an kira shi.
biey
Sai ya juyo a hankali ya kalli mai kiran na shi.
afeena...

Ya furta with surprise, ta karaso kusa da shi tana murmushi.
in zo ashe
e zai hana na zo?

Auren Sauban ake fa!

Jerawa suka yi tare suna tafiya zuwa gurin motarsa dake fake.
ow are you Feeling now Abiey?

Ya sauke ajiyar zuciya secretly ya hade yawun bakinsa.
lhamdulillah
a Zahra take?

Wani irin dauke wuta yayi na dakiko sannan ya amsa mata, cikin wani irin yanayi da ita ma kanta ta fahimci furta sunan Zahra ya taba shi.
a yi aure tana rayuwa da mijinta cikin farinciki and that's all the matters
ar yanzu tana kallonka a matsayin wanda ya ci amanarta ya yaudareta?

Ya kalleta yana dan murmushin takaici.
hy wouldn't she?
Chapter 9 · 0% Book details