← Book details Ciwon So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 112 OF 134

Sashe 112

Ciwon So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mama ta ce
ikan da mamaki, mun yi zaton daga Abiey sai Sauban ne suka san gaskiya
oh da ni aka shirya komai, Ammy da Mai Martaba ne kawai ba su sani ba, amman babu abun da Abiey zai yi da ba zai fada min ko ya nemi shawarata ba, ba dan ni da kanen mahaifin Sauban da aka tura ba su yarda sun je ba
mman a matsayin ki na babba be kamata ki aimata wannan abun ba, saboda gudun matsala?

Musamman gurin Mai Martaba
a ni aka lalata auren Abiey da Zahra na farko, domin Deen yayi garkuwa da mijina ne har cikin gidana, kuma na rasa hujjar da zan gabatar da shi a gaban kotu har sai bayan da komai ya faru, sun shigo a cikin gidan dauke da bindigogi sanye da mask a fukokinsu ta yadda bana iya tantance ko daya a cikinsu, sai dai na gane cewar shi din ne bayan an daura aurenki da shi, tun kamin su bar gidan sun gargade ni cewar kar na karna kuskura na fadawa police domin rayuwar mijina suke so ba tawa kuma ba dukiyar da muka tara ba, kowa yayi magana a cikin mutanen da suka yi magana ban da mutum daya wanda nake kyautata zaton shi ne Deen, tun a ranar suka ba ni umarni na yi duk abun da zan iya a fasa aurenki da Abiey, idan ba haka wanda ya dauke mijina zai kashe shi sannan ya akashe kansa, sun yi min rantsuwar dake nuna ba da wasa suke ba, lokacin idona ya rufe musamman da aka dauki kwana biyu babu kira babu wani bayani daga jami'an tsaro cewar an gano inda mijina yake, gashi lokacin da suka ba ni umarni ya rage kwana uku a daura auren Zahra da Abiey, na rasa yadda zan bullowa lamarin ina ta sauraren ko za su kirani amman ba su kira ba, hankalin Ammy da na yan'uwan mijina ya tashi balle kuma ni da nake matarsa, a lokacin ina ganin kamar ransa yana hannuna ne, domin aikata abun da aka umarce ni zai ceto rayuwarsa, akasin haka kuma zan rasa shi, amman Abiey ya kasa fahimta ta saboda kaunar da yake miki ta rufe masa ido da baya iya hangen komai sai ke, be aminta na aikata ba, bayan mun shirya komai na fada masa sai yace ko da haka ta faru zai aureki, a nan Ammy ta shata masa line ta ce idan har ya zabi auren Zahra akan rasa rayuwar yar'uwarsa, to sai ta masa baki, a dole ya hakura dake sai dai ni yake ta dorawa laifin, bayan mijina ya fito aka daura aurenki da Deen sai muka fahimci shi ya aikata wannan abun, da na tambaye mijina a ina ya aje shi sai yace sun kai shi a ciki daji ne, kuma tabbas da ban aikata abun da suka bukata ba da kashe shi za su yi da gaske, sai dai yace da za a dawo dashi cikin gari bayan an daura aurenki sai da aka rufe masa fuska kamar yadda aka yi masa a lokacin da za a shiga da shi dajin, a tsawon zaman da yayi a dajin be ga fuskokinsu ba kuma be ji muryar wani da zai iya ganewa, haka kuma ba su bar masa wata alama da zai fahimci komai ba, even camera tsaro dake wajen gidanmu ta dauki motarsu ne kawai da bata da number kuma aka gagara gano shi har sai dai mao faruwa ta faru, bayan komai ya laba na ce zan saka shi a kotu sai Abiey ya hana domin ba mu da wata cikakkciyar shaida a lokacin, sai dai muna da kudin da za mu iya sakawa a daureshi ko da shi ne da gaskiyar a haka dai Abiey ya hana saboda kar a tashi hankalinki, tun daga lokacin na gane kaunar dake tsakaninku daga Allah take, yan mata da yawa su kan so namiji saboda kudi ko wani abun da yake da shi, sai dai ke ban ga haka daga gareki ba, shi ma auren da kika yi be saka kaunarki fita daga ransa ba, sai ma karuwa da ta yi, saboda muka samu rashin fahimta da shi, a yanzu kuma na samu hanyar da zan gyara wacan barnan da na yi, me zai hana na yi haka?

Idan ban taimaka masa a yan
zu ya samu abun da yake so ba?

Da wane ido zan kalleshi?

Ke ma kuma na san kin dauke kai daga gareshi ne kawai saboda an shata muku layi, ya fada min idan ya fito fili ya nuna yana sonki abu ne mai wahala ki amince masa, saboda kin nuna masa ya bi umarnin Ammy da Mai Martaba, shiyasa muka bullo miko da wannan hanyar
12/28/22, 11:06 - Buhainat: Tun da ta fara maganar bata tsaya ba har sai da ta kai aya, ni kuma na dago na kalleta hawaye wasu na bin wasu.
mman hakan zai kara lalata alakarsa da Mai Martaba ne kawai, wata kila sanadin haka Ammy ta kara tsanata?
e miye laifinki a ciki Zahra?

Ke da aka yaudara aka aura?

Idan akwai mai laifi to ni da Abiey da Sauban ne, ki cire wannan a ranki, kuma karki takurawa kanki da neman sai Abiey ya rabu da ke ina da tabbacin idan haka ta faru, to zamu rasa shi ne a lokaci daya, ko a yanzu kadan ya rage mu rasa shi domin damuwar dake ransa ta haifar masa da babbar matsala, wata kila warkewarsa na daga cikin samunki, shiyasa ni ma na jajirce har haka ta faru...
r ki daina yi min wannan fatan, da yardar Allah ba zan sake zama matar takaba, ba zan sake binne mijina ba sai dai shi ya binne ni
Murmushi ta yi ta kwantar da kaina jikin kafadarta.
i kaina ban jidadin yadda abubuwa suka faru ba, amman wani lokaci ya kamata mu yarda da kaddara mu bar zukata su yi aikinsu, Allah yasa Ammy ta fahimci haka
meen Mama
Ta daga ni ta mike tsaye.
an tafi wata kila ba zan samu dawowa ba, sai dai na same ki a gida
a gode sosai Dr mun yi magana da Mr Bashir, ya sassauta min fiye da yadda na yi zato kuma hakan ya faru me ta dalilin bayanin da kika masa kamin na dora masa da nawa
Ta dawo ta zauna tana kallona da mamaki.
a miki magana kenan?

Na daga mata kai ina jin tausayinsa a raina.
ayi kuma ya roki ni abun da da ace ba da Abiey aka daura auren nan ba, da na amince masa ko dan Amir, domin ya fito min a sigar da ban yi zato ba, ya nuna min natsuwarsa da hankali, daga ni har matarsa da Dr Hamid ba mu kyauta ba, amman ya kasa natsu be yanke hukunci a cikin fushi ba, na dade ban ga wani mutum mai hankali da kwantar da kai ya aiwatar da wani abu ba kamar shi
aman can na sa ran haka, domin be dauki abun da zafi ba, kuma daman idan har zai yi tunani haka ya fi dacewa domin idan yace zai hukuntaki ko matarsa duniya zata kalleshi a matsayin marar tausayi da tunani, kuma har wanda be san abun da ya faru ba zai sani, hakan kuma ba zai goge komai daga zuciyarsa ba haka ma daga abun da suka aikata, tabbas Mr Bashir mutum ne, na jidadin abin da yayi, Allah ya dubi zuciyarsa ya ba shi haihuwar da yake nema
meen
Ni da Mama muka amsa, bata dade da tafiya ba, yan'uwa Mamata suka shigo duba ni.
12/28/22, 11:06 - Buhainat: ABIEY POV.

A hanya yayi sallah Magariba sannan ya shigo cikin gidan, kallo daya zaka yi masa ka fahimci yana cikin farinciki, da kuzarinsa ya shiga dakin Ammy ya zauna gefen gadonta har sai da ta sallame sallah sannan ya dawo kusa da ita ya zauna.

Ta kalleshi da duba na mamaki
liyu ya kake yau kamar wanda aka yi ma bushara...?

Na sumbanci kumatunta yana murmushi.
a cika wani buri nawa ne da na dade ina zuwan jiransa, Alhamdulillah ko a yanzu na mutu zan tafi cikin farinciki
Ya kwantar da kansa jikin Ammy a shagwabe ya fara magana.
mmy na miki wani katon laifi da ba lallai ne ki yafe min da wuri ba, kuma be zama lallai zuciyarki ta karbi abun da wuri ba, amman dai ke zaki taya ni yakinsa a gurin Mai Martaba har na yi nasara ko kuma shi yayi nasara a kaina wanda bana fatar haka
Carjin dake hannun Ammy ta aje ta juyo da kyau ta kalleshi cike da fargaba.
an fahimta ba, fito fili ka fada min abun da ka aikata
ai kin min alkawarin ba za ki yi fushi da ni ba
dan har kasan abun da zai saka raina ya bace ne miyasa zaka aikata tun farko?

Ya gyara zamansa ya sauke kai kasa with serious face ya ce.
mmy kin san yadda nake matukar son Zahra
Ammy ta daga masa hannu.
an Allah karka fada min ka aikata wani abu akanta, ba kusa ba ba kuma nesa ba na shata line tsakaninka da yarinyar nan
aba Ammy wannan ba halinki ba ne, kuma kin fi kowa son abun da nake so
h amman haka ba zai saka na so abun da zai cutar da kai ba
Ya kwanta saman jikinta.
a ina Zahra ta zama cutarwa a gareni Ammy?

Yarinyar da ke da kanki kika shiga kika fita wajen ganin an mallaka min ita?
da can ko Aliyu?

Ba a yanzu ba, da Mai Martaba ya zaba maka matar da zaka aura, kuma yarinyar babu kalar wulakanci da bata yi maka ba bata yi ma yan'uwanka ba
Ta janye jikinta ta matsa baya cikin bacin rai tace.
saya ma wai me ka aikata?
Chapter 112 · 0% Book details