← Book details Ciwon So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 134

Sashe 25

Ciwon So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai da na fara taka entrance din na ji zuciyata ta yi min wani irin nauyi kamar ba tawa ba, yawu na hade yafi a kirga sannan na cika kafar da nake jin ta yi min nauyi sosai na doshi kofar, sai kuma na samu kaina da matse hannu na rumtse ido ina jin kamar idan na bude wani mugun abu zan gani, kamar na juyo na dawo sai na ji ba zan iya ba.
nnalillahi Wa'inna Ilaihirraji'un
Shi ne abun da na furta sannan na bude ido ina jin kamar na dan samu kwarin guiwa na kai hannu na murda kofar falon na nasa kafata sai na arba da abun da na fi tsana, idonsa ya sauka a cikin nawa a take mug din dake hannunsa ya subuce ya fadi kasa, kallo daya na yi masa na dauke kaina domin bakin maciji zai fi min sha'awar kallo fiye da Abiey.

Kamar wanda aka dasa haka na tsaya rike da kofar ni ban shigo ba ni ban koma ba har sai da Yasmin ta kira sunana.
ahra
Na kalleta sai dai ban amsa mata ba na shigo cikin falon na tsaya, Yasmin ta karaso kusa ni, ni kuma na kasa furta komai kuma na kasa juya na fita, a lokacin ne sai kuma ya koma min kamar mafarki.
aman...daman....

Sai na kasa furta komai, hawaye suka wanke min fuska.

Da sauri Abiey ya juya ya ba ni baya, sai na kalleshi tun daga sama har kasa acan na dauka yaudara ce kawai yanzu kuma na fahimci akwai tsanata a tare da shi, daman ai zama a samu domin matsayina da nashi ba daya ba Deen ma ya sha fada min haka.
aman na zo nan ne saboda Mijina
Na fada ina sauke kaina kasa hawaye suka hanani ganin komai.

Yasmin ta dafa ni.
iya faru?

Dafa ni da ta yi sai na samu gwarin guiwar karanto mata abun da ke tafe da ni kamar daman can a gurinta na kawo kukana.
ana asibiti, hantar ce ta samu matsala likitoci sun ce sai mun kawo miliyan bakwai sannan za a masa magani, na buga duk inda ya kamata na buga, yan'uwansa sun yi iya kokarinsu, iyayensa ma amman gaba daya abun da muka hada be wuce miliyan uku da wani abu ba, taimako muke nema saboda likitoci sun ce idan ya wuce sati samu iya rasa shi
ubhanallahi
Yasmin ta fada, sai dai abun da Abiey ya juyo ya fuskance ni ya furta ya kusan saka ni suma a tsaye.
ho are you?

Ba ni kadai ba, ko Yasmin na lura ba kamin kaduwa ta yi da fucinsa ba.
ahra ce fa
Yasmin ta fada.
ahra who?

She should introduce himself
Na daga kai na kalleshi da wani irin duba na kaskanci.
ahra...

Aminu...

Umar....

Mrs Zaharadeen...
ai aka ce miki kudin da muka tara na taimako ne?

What make you think that we can help you?
es you can't...

Soyayya da kokarin ceto rayuwar mijina ya saka na manta wani irin mutum ne kai, kana da gaskiya ko kowa ya kare min a duniyar nan be kamata na zo neman taimako a gurinka ba, am such a fool, da wawanci ka yi amfani ka cutar da ni, yanzu kuma wawanci ya sake kawo ni gurinka
Na karasa ina murmushin takaici da bakinciki sannan na juya sai kuma na juyo.
utarwa da min ban yafe maka ba, kuma ba zan taba yafe maka ba, yadda ka so ka kunyata ni ka saka ni a bakinciki Allah ya kungiyata ya hana ka farinciki Aliyu, azzalumi macuci mayaudari
A fusace na fice daga falon ina tafiya kamar zan fadi, zuciyata kuma na ce min gani nan fadowa kasa saboda bakinciki, ina jin Almu yana min magana ban saurare shi ba na fice da sauri hanya na hade min, ban taba bakinciki aikata wani abu ba kamar yadda na yi bakinciki tako kafata a cikin gidansu Abiey a yau.

ABIEY POV.
aya zan taimaki mutunmen da ya nisanta ni da ke?

Taya zan taimaki mutumen da ya saka kika kallo a matsayi macuci, ta zan iya taimaka wanda ya saka kika manta da soyayyata a zuciyarki?

Ya fada a zuci kamin ya furta.
can't
Ya juya ya isa dinning ya dora hannayensa kan kujerar dinning din ya kifa kansa, sai kuma ya dago kai ya daga kujerar ya buga a dinning, a take dinner din da yake na glass ya watse tare da abincin da yake kai.

Da gudu Yasmin ta haye upstairs.
his is the first time da Zahra ta zo nemam taimako a gurina na kasa taimaka mata, ta zo nan ne saboda tana jin tana da gata a gurin, but she end up called me macuci azzulumi, all because of Deen, ba zan iya taimaka mutumen da ya raba ni da rayuwata ba
Ya furta kamar wani mahaukaci ya nufi kitchen da gudu ya dauki wayarsa ya shiga kiran Sauban, ringing biyu uku Sauban yayi picking.
ello
auban ka zo gida gurin Ammy yanzu ina son ganinka akwai matsala
Yana fadar hakan be tsaya jiran abun da Sauban din zai ce ba ya kashe wayar ya jigina da kitchen kamin ya isa fito kamar marar lafiya ya nufi sofa ya zauna ya dafe kansa.

After like 20min direban Ammy ya faka motarta kusa da entrance din shiga falon sannan ya fita ya zagaya ya bude mata ta fito, ta nufi kofar shiga falonta rike da jakarta.
ubhanallahi
Shine abun da ta fara furtawa a lokacin da ta shigo falon ta yi arba da dinning dinta da aka fasa, ga kuma Abiey dafe kai.

Abiey ya dago ya kalleta idonsa cike da hawaye.
mmy a yau na ga Zahra a cikin damuwar da na kasa yi mata magani, na ga Zahra tana zubar da hawayen da na gagara tsayar mata da su, a yau Zahra ta roki alfarma sa na kasa yi mata...

Ammy ta karaso cikin falon tana kallonsa thinking ko dai
anta ya fara ganin ghost...
10/1/22, 22:03 - Buhainat: *
CIWON - SO
By Khadeeja Candy
annan abun ya zama hauka, tun kana yin abu da hankali har ya kai yanzu ka fara fita hayyacinka, wane irin so ne wannan?

Ji yadda kake kokarin maida kanka mahaukaci saboda kawai wata can da bata san kana yi ba
Ammy ta rufe da fada domin a ganinta abun ya wuce gona da iri, amaimakon yayi magana sai ya soke kansa kasa ya rumtse ido.

Fadan da Ammy ta yi ya saka Yasmin saukowa jikinta a sanyaye domin ta tsorata sosai da yanayin Abiey.

Ammy ta nuna shi da yatsa.
nd this should be the last time da zaka kara ambatar sunan Zahra ko wani abun da ya shafe ta a gidan nan?

Enough is enough na gaji, ban san abun da yake damunka ba
Sai ya dago ya kalleta cikin wani irin yanayi mai wahalar fassarawa.
iwon so ne Ammy, kaddarata ce wannan
Ya mike tsaye wanda hakan yayi daidai da faka motar Sauban a harabar gidan, sai kawai ya nufi hanyar fita daga falon Ammy ta bishi da kallo har ya bude kofar ya fita, sannan ta maida dubanta gurin Yasmin.
ina nan yayi wannan haukar?

I think sai mun tashi tsaye Abiey ya fara tabuwa, wai yanzu yake fada min yau ya ga hawaye a idon Zahra bla bla..
a gaske Ammy Zahra ta zo nan
Ammy ta kalleta da sauri.
a gaske?

Kim ganta da idonki?

Me ta zo yi?

Ita da wa ta zo?

Yasmin ya shimfadawa Ammy abun da ya faru, ba karamin mamaki da tausayin Zahra ne ya kamata ba.
ubhanallahi
Ta furta sannan ta mike tsaye da sauri ta nufi kofar falon ta bude ta fita, sai ta samu Abiey tsaye a balcony din tare da Sauban.
liyu da gaske Zahra ta zo nan ashe
i ma yanzu yake fada min abun da ya faru, and i could believe what he did to her
Sauban ya amsa mata shi kanshi mamakin abun da Abiey yayi yake.

Abiey ya kalleshi yana murmushin takaici.
hat do you expect?

Kana ganin zan iya taimakon mutumen daya raba ni da rayuwata?

Mutunen da ya kashe ni da raina?
a akansa zaka yi saboda Zahra zaka yi?
eah idan har zan yi saboda ita to ita kadai zan yi ma, ko zan iya taimako kowa a duniyar nan ban da wannan mashayin Sauban i can't
Ammy ta sake kallonsa da mamaki.
annan ba halinka ba ne
uniya ce take koyawa mutum wani abu da ba halinsa ba, Ammy don't you think amana ce take bibiyarsa?

Yaushe zuciyarki ta manta abun da ya faru?

Duk wani hali da nake ciki da damuwa saboda shi ne, abun bakinciki har yanzu Zahra kallona take a matsayin macuci saboda ya bata komai
Ammy ta yi kasa da kanta tana tuna lokacin da abubuwa suka rinchabe, lamarin da be yi ma kowa dadi ba.

Sauban ya dafa shi.
eah kana da gaskiya Abiey, amman ina son ka sani Zahra ba ita ce autar mata ba
gurin Zahra ce autar mata, and i called a nan ne saboda na san Zahra zata iya zuwa neman taimako a gurinka, ko makiyina bana son ya taimakawa Deen, balle wani na kusa da ni har ke Ammy
Ya juyo yana kallon Ammy.
aman can ko zan yi saboda Zahra zan yi, but since ka ce kar ayi i won't hurt you
Ammy ta fada sannan ta sauke ajiyar zuciya ta juya ta koma cikin falon.

Sauban ma ajiyar zuciya ya sauke ya saka hannayensa aljihu.
llah yasa kar ka zo kana nadama
Zaunawa Abiey yayi a daya daga cikin kujerun da suke gurin.
a rasa abun da zan yi, so yana da zafi Sauban, Ciwon so yafi ko wane irin ciwo cutarwa da azabatar da mai shi, you got lucky you marry your first love babu wani tashin hankali
Ya furta yana kawarda fuskarsa hawaye na cika idonsa, sai ya saka babban yatsansa ya goge, babu abun da idonsa suke masa gizo sai hawayen da ya gani a fuskar Zahra, da kuma cikin dake jikinta.
na fatar abun nan ba zai cutar da abun da yake cikinta ba
s she pregnant?
Chapter 25 · 0% Book details