← Book details Ciwon So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 134

Sashe 11

Ciwon So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jiya da aka kawo shi rangi rangi rai a hannun Allah yau kuma ya samu lafiya ya fara tijara
Anty ta kalli Sauban dake maganar tana dariya.
ada masa dai sai an zo duba marar lafiya sai a ga gado wayam babu kowa a kai?

Likitoci sai su ce ina mai jinyacin ai ko?
mmy zata fada musu na tafi gida idan sun zo
Ammy ta kalli Abiey.
aboda ga Ammyn mahaukata ko?

Sai na zauna gadin gadon asibiti har likitocin su zo?

Duk suka saka dariya ban da Abiey da yayi murmushi tunawa da haka ta taba faruwa da shi da Zahra.

Sauban ma ya mike tsaye ya ce.
mmy za ku iya tafiya ai, sai ki fadawa Dr a waya in ya so kamin taje aiki sai ta je can gida ta duba shi
an gida gurin Mai Martaba ba, tare zamu wuce
Juyowa Abiey yayi ya kalleta kamar yayi magana sai kuma wata zuciyar ta hana shi, saboda ba ya son ya yi wani furuci da zai saka ran Anty ko Ammy ya bace.

A tare suka fito da Anty Amarya Narjis tana rike da hannunsa Aisha kuma tana gefen Narjis, Sauban na baya tare da Ammy da waya ke makalle a kunnenta tana fadawa Momy Uwani abun da ya faru.

Mota daya Sauban ya shiga da Ammy sai da ya fara sauke ta gida sannan ya wuce nasa gidan.

Abiey da Anty Amarya da yayanta biyu kuma direba ya sauke su a Masarautar Mai Martaba Sarkin Kano Abubakar Aliyu Jauro Na Uku, ko da wasa Abiey be kalli bangaren su Mama Lami da Hajiya Kilishi ba, daman can gaisuwa ma sai Anty ta yi kamar tana yi sannan ya gaishesu, idan kuwa wata lurar ta saka shi zuwa bangarensu ji yake kamar yana saman kaya da karmami minti biyar ba zai iya yi a falon kowancce a cikinsu ba.

Idan ma ka ganshi a bangarensu to cilastawar Anty ce, domin shi har mantawa yake da yana da wasu matan uban ko yan'uwan da suka hada uba daya, bayan yayan Anty Amarya Aisha da Narjis, kusan idan ka tambaye shi ma sai yace wai maka be san sunan wasu ba.

Yana shigowa cikin falon kai tsaye ya nufi upstairs zuwa dakinsa, wanka ne abun da ya fara yi ya jika ko'ina na jikinsa da turare kala kala masu matukar tsada da kamshi na tashin hankali, sannan ya sauko kasa zuwa dinning.

A zahiri idan ka kalleshi sai ka yi zaton babu damuwa ko bakinciki a tare da shi, bayan kuma su ne suka hade masa kai suka yi kaura a zuciyarsa da ruhinsa, sai dai imani da yardar da kaddara ya hana fuskarsa bayyanar da hakan sai dan abun da ba a rasa ba, ko kuma idan ta dauro.

Kujera yaja ya zauna, shi kadai a dinning kuma shi kadai a iyalahirin kafon falon da baka jin karar komai sai anye air conditioner dake tsaye, warmers din ya bude sai da ya gama kalle abun da aka shirya a gidan na karyawa sannan ya dauki karamin plate ya zuba soyayen dankali da ya hada ruwan tea, ya soma karyawa daman shi ne favorite food nasa, sai da ya gama karyawa sannan ya saka hannunsa aljihu sai ya ji babu wayarsa, runtse ido yayi ya bude ya tashi a dolenss ya nufi upstairs, yana shiga ya samu wayar tana vibration.

Safeena ya gani a rubuce saman screen din wayar, dan murmushi ya yi sannan ya kai hannu ya dauka ya nufi inda iPod's dinsa suke ya dauko expensive one yayi connection sannan ya sake kiranta.
ey Safeena
i Handsome
Jimmm yayi kamar ba zai ce komai ba, he is just breath without saying anything, every act, every word, every move is reminding him Zahra, haka take kiransa idan ya ce Hey Pretty sai ta ce Hello Handsome.
a jikinka?

Safeena ta katse masa tunani.
lhamdulillah
ana asibiti?
na gida
aman na san da wahala ka iya zama asibiti ai kai da baka son jinya
Ya shafa kansa ya nufi katon dressing mirror dake tsaye yana kallon kyakkyawar surarsa da kwarzantaka da haifa irin ta zakin namiji.
an iya aje wayar
Ya furta jin ta yi shiru bata ce komai ba.
eah why not get well soon please
pray so
Ya sauke wayar ya saka ta aljihunsa ya nufi inda keys din motarsa suke ya dauko new one na sabuwar motar da ya siya last couple months.

Cike da kuzari yake saukowa stairs din agogon GMT dake falon ya soma bada sanarwar 10am, kallon agogon yayi ya dauke kai ya nufi kofa.
biey...

Ya juyo da sauri ya kalli Anty dake fitowa ta kofar baya.
na zaka je?

Ya dan tabe baki kamar mai tunani, can kuma ya daga kafadunsa.
don't know, maybe somewhere else
a shiga ku gaisa da Mai Martaba
Ya sake kallonta irin duban nan na da gaske kike.
a san jiya ka min alkawarin zaka gaisa da shi idan ka dawo, yanzu kuma yana falo yana gaisawa da yan'uwanka, be kamata ka ware kan ka ba
mman Anty ya san ba ni da lafiya?
anin baka da Lafiya zai canja komai ne?

Na fada masa tun jiya
ai Martaba ko yayayansa da matansa babu wanda ya kira ni ko ya zo duba lafiyata
atansa da yayanss ba su sani ba, amman dai shi ya sani, please
kay since kin bukata i can't say mo to you Anty
ood muje
Ta nuna masa kofa, sai yayi murmushi ya wuce gaba ta bi bayansa, dogon corridor ne guda hudu wanda ke sada duka matan Sarki guda uku da dangaren Sarkin, ta yadda wance ke da girki zata shiga kai tsaye ba tare da kowa ya sani ba, domin corridor kowa dabam yake sai idan ya kawo daf da kofar shiga falon Mai Martaba ake iya haduwa da mutum.

Sai da ya cika bakinsa ya iska sannan ya kai hannunsa ya tura kofar falon ya shiga, as usual daya bayan daya ya bi kowa da kallo sannan ya nufi kusa da inda Anty Amarya ta zauna ya zauna, daman a gidan ita ce uwarsa komai yake so ita ce take masa, ko abu aka raba a gidan na Abiey Anty Amarya ake ba ta aje masa, idan kuma wata maganar za a masa ko bukatar wani abu sai an raba ta gurinsa, Abiey wani murdadden mutum ne mai wuyar sha'ani da baya bin ra'ayin kowa sai na kansa, sai dai Anty Amarya ce kadai take iya tankwara shi yayi abun da be tashi ba.

He's not the only son a cikin yayan Mai Martaba amman shi nr da daya tilo da gaba dayan matan sarki guda biyu da yayansu basa kauna, ba kuma shi kadai ne namiji ba balle ace saboda suna da yaya mata ne, no Mama Lami da Hajiya Kilishi duk suna da yaya maza da mata, hasali ma Abiey ne kadai dan da Ammy ta haifa da Mai Martaba kamin su rabu, but he's the only son da Mai Martaba ya tsana kamar mutuwarsa, kuma shi kadai ne dan da Matan Sarkin suka tsana a zuciyarsu ban da Anty Amarya, su ma kuma basa nuna matsa tsanar a fili, musamman idan yana gaban Mai Martaba ko a gaban Anty Amarya sai su nuna kamar ma sun fi kowa damuwa da shi.

Farar Jallabiya ce jikin Mai Martaba irin ta manyan larabawa da yan sarauta suke sakawa, mai matukar tsada da nuna isar mai sakata.

Idonsa sanye da gilashi grandchild dinsa Aymana tana zaune kusa da shi tana wasa da yatsunsa, kamin ya shigo hira suke cikin girmamawa da nishadi, sai dai yana shigowa a take fuskar Mai Martaba ta canja murmushin dake fuskarsa ya gushe, sauran yayansa kowa sai ya natsu domin sun san idan Abiey yana kusa da Mai Martaba kamar haduwar wuta da ruwa ne, dole sai rai ya bace ko da kuwa Abiey be masa laifin komai ba, wani lokacin har su ta kan shafe su.
biey baka gaishe da su Hajiya ba
Anty Amarya ta fada tana kallonsa, sai ya daga kai ya sake kallonsa da idonsa irin na stubborn boy ya maida dubansa gurin Mai Martaba domin yana jin kamar shi ne kawai ya zame masa dole ya gaisar.
arka da Safiya ranka ya dade
Uffan Mai Martaba be ce ba, balle yayi wata alama ta amsa gaisuwar da yayi masa, sai ma daukar wayarsa da yayi yana tabawa cike da kasaita da isa da izza irin ta manyan sarakuna.

Mama Lami ta yi murmushi mai sauki,
dan be gaishe mu ba mu ai sai mu gaishe shi ba wani abu ba ne, ance dukawa wada ba gajiyawa ba ne
Sai Hajiya Kilishi ta tabe baki ta karba mata.
to indan dai duniya kararriya, Allah dai ya kyauta
Anty Amarya ta kallesu tana murmushi domin ta san manufarsu.
u ma dai kuna son abun magana, sai ka ce ba ku san halin
an naku ba, Abiey ai ba magana ta dame shi ba, idan miskilancin nasa ya tashi ko ni da nake uwarsa ba magana yake min ba
Abiey saka hannunsa aljihu ya ciro wayarsa zai fara tabawa, Mai Martaba yayi gyaran murya.
nce faduwa kake, sai a sama maka dogarawa kar kaje ka fadi mugun guri
Mai Martaba ya fada cikin furuci na isa da sarauta.

Abiey ya kalleshi duk da ba shi kadai ne a falon ba ya san da shi yake.
Chapter 11 · 0% Book details