← Book details Ciwon So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 134

Sashe 4

Ciwon So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta fada kuka na daf da subuce mata.
ou're so selfish, ke ce kika lalata komai and because of that i lose her forever
liyu tashi ka fita daga falon nan, i don't want to see you in my side please leave
Ya kalli Ammy sai yayi murmushi ya mike tsaye.
ow...

Daga haka be sake cewa komai ba ya juya ya nufi kofar da ya shigo ya bude ta slowly ya fita.

Dr Zainab ta bishi da kallo hawaye na sauko mata.
mmy Abiey yana da gaskiya, ya rasa soyayyar mahaifi, kuma ya rasa wanda ya fi so fiye da kowa a duniya, he deserved Happiness, kuma yana da damar da zai tsane ni, da ace ban biye tsoro da son zuciya na aikata abun da Deen ya umarce ni da shi ba, da yanzu Abiey be shiga cikin wannan halin ba, kuma da yanzu be dora min laifi ba, duk cikin yan'uwa babu wanda Abiey ya shaku da ita kamar ni, kuma a haka na zama silar rasa farincikinsa
i daina biye shi Ciwon So ne yake damunsa, ta ya zaki salwantar da rayuwar mijinki uban yayanki saboda shi?

Ki ma daina saka wannan a ranki
Kujerar da Abiey ya tashi Dr ta nufa ta zauna tana hawaye jikinta gaba daya yayi sanyi.

Abiey na fita falon cikin motarsa ya shiga ya yi reversed kamin ya isa gate mai aikin kula da gate din ya bude masa, sai ya fisgi motar ya hau titi kamar wanda baya son ransa.

Driving yake hawaye na cika idonsa suna saukowa tun yana daurewa har sai da ya kai ga dukan sitiyarin motar da karfin tsiya kamar zai raba shi biyu.
miss you Zahra i miss you so much....

Tafiyar minti ashirin da wani abu ya nade hanyar da gudun motarsa ya isa gidan Mommy Uwani cikin minti goma sha biyu.

Sau daya ya danna horn aka bude masa gate ya shiga ya faka harabar gidan sai kuma ya samu kansa da kasa bude motar ya fito, ya ji kamar zaman motar zai fi yi masa dadi fiye da shiga cikin gidan ma, kwantar da kujerar motar yayi ya jingina ya kwanta ba tare daya kashe motar ba ya lumshe idonsa ya rungume hannayensa.

After like 30min ya ji ana kwankwasa glass din motar, hakan ya saka shi bude ido, sai ya yi arba da Yasmin step sister din Dr Zainab ta uku, sai dai ita bata iya ganinsa kasancewar motarsa mai bakin glass ce.

Tashi ya yi zaune ya bude motar sai ta matsa gefe ya fito.
ommy ta ce na duba ka ko lafiya?

A maimakon ya amsa mata sai kawai ya rumgumeta ya lumshe ido.

Kamar wanda ta mutu haka komai nata ya tsaya cak with shock kamin numfashinta ya dawo jikinta a hankali.

Kasa motsawa ta yi duk da kasancewar a compound din gidan suke, tana gudun wani ya gansu domin ba halinta ba ne, shi ma kuma na halinsa ba ne, be taba gwada yi mata haka ba ko a mafarki.
biey do you need someone to talk to?

Ya daga mata kai da sauri.
kay...

Bari mu shiga cikin gida sai ka sha ruwa mu yi magana ka ji?

Ya kara rumgumeta.
lease let me hug you
Ya furta calmly har lokacin idonsa a rufe suke.

ZAHRA POV.

Bayan na sha cornflakes din daya siyo min, na kwanta saman kujera shi kuma ya fita tsakar madaidacin gidanmu ya fara gyara kayan miyar da zai dora mana jalof din da su, tun ina jin motsinsa da yadda yake kai da kawo har bachi ya sace ni, daman ni da bachi kamar 5&6 ne, indai zan ci na koshi sai kuma bachi duk inda na samu kuma yinsa nake tun ina karama har zuwa yanzu da nake da da shekara ashirin da daya.

Ina farkawa na gan a lullube ni an dora kaina saman filo, na san ba kowa zai min wannan ba sai abokin shigata aljanna wato Deen mijina masoyina.

Cikin shagwaba da na saba na dan juya kaina kadan na kalleshi yana zaune tsakiyar falonmu yana goge tufafin daya wanke min jiya.
abe na kin farka?

Na dan mitsintsinka ido kamar wata yar baby ta turo baki gaba ba tare da amin komai ba sai dan tsabar shagwaba da na saba da ita tun ina karama har zuwa yanzu.
bincin ya yi?
o acici mala'ikun tauna, bari na zo na rika ki ki wanke bakin sai mu ci abincin tare daman ke nake jiran ki farka
Yana fadar hakan ya nufo inda nake cike da so da kauna ya ya rika ni na tashi zaune kana ya mikar da ni tsaye yana gyara min dauren zanen dake kokarin subuce min, daman can ni raguwace aiki ko na daukar tsintsiya ne bana so balle kuma yanzu da nake dauke da cikin wata bakwai.

Tare muka shiga bandakin dake bedroom dina, shi yayi fitsari ni ma na yi na wanke bakina da fuskata sannan ya rika hannuna kamar ance masa koyon tafiya nake.
aka a hankali
Ya fada yana kallon yadda nake takawa har muka isa a inda muka saba zama mu ci abincin.

Center carpet ya shimfida mana na zauna sannan ya fita waje ya shiga kitchen ya dauko mana abincin daya dafa.

A plate daya ya zuba mana spoon ma daya ne, kofin ruwanmu ma daya ne, daman can indai zamu ci abincin a tare to bana bata hannuna shi zai min komai da hannunsa idan kuma spoon ne daya zamu yi amfani da shi.

Sai da ya fara ba ni ina ci sannan shi ma ya soma ci, ba karya mijina gwanine ta kowane fanni, ga kyau ga tsabta ga soyayyar ga iya mu'alama ga kuma iya girki.

Dadin abincin ya saka na fara masa santi.
een idan muka yi kudi ka gina mana katon gida
i dole, kin ga sai mu shuka shimkafa, mai, magi, da kifi, kayan miya da komai da mun tashi girka jalof sai dai kawai mu diba mu girka
Ya fada yana min kallon zolaya, aiko sai dariya ta ce min salamu alaikum, har sai da abincin ya sarke ni, da sauri ya dauko ruwa ya bani na sha kadan sannan ya cigaba da ba ni abincin.
dan na yi katon gida, duk sai kin cika min shi da yaya, ki yi ta haihuwa kamar kaza
Na turo baki gaba.
ab Wallahi ba zan iya ba, sai dai ka auro wata, daman maza da sun yi kudi sai aure
Ya aje spoon din hannunsa ya kama hannuna ya rike yana kallon cikin idona da wani irin tsantsar kauna da soyayya marar algus.
na son ki Zahra, ina mik
i wani irin so da wani dan'adam be taba miki irinsa ba, ina miki wani irin so da bana son kallon mata saboda na taya ki tsare kaina, kullum kece nake tunanin yadda zan faranta miki me zan yi na burge ki, Alhamdulillah na fi karfin abun da zan ci yau da kullum amman da zan yi arziki na fi kowa kudi a duniya, ko wace kaddara tawa sai na saka mata sunanki, Wallahi Zahra na miki alkawari ba zan taba miki kishiya ba, ina nufin ko da a zuciyata ne wata rana ta kyasa min son wata mace ba zan taba bari ba, balle har na hada ku a karkashin inuwa daya har abada Zahra, Ciwon Sonki ya riga ya so ke ni kuma ba zan taba warkewa ba
Idona ya cika da tausayinsa ba tausayi na rasa ni ko wani abun ba, sai dan yadda kaunata take dawainiya da shi, ni kaina ina masa son da bana jin akwai mace da take yi ma mijinta irinsa.
een wani lokacin tsoro kake ba ni, kana min wasu kalamai kamar ba na hankali ba
Na fada a shagwabe ina turi baki hawayen har ya sauko min.

Murmushi yayi ya tashi daga inda yake ya dawo kusa da ni ya zauna ya ja ni jikinsa ya rumgume ya dora hannunsa saman cikina.
na son ki Zahra ke ce rayuwata...

Page 1 to 10 ne free, na kai page 10 na gama free pages In'Shaa Allah, if you want to subscribe pay 500 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith bank
Sai ku turo shaidar biyan ta wannan number 08036126660 zan saka ku paid group In'Shaa Allah.

Yan nijar kuma za ku biya ta wannan number +22790165991 sai ku turo shaidar biyan ta line na 08036126660.

Thank you.
10/1/22, 21:58 - Buhainat: https://www.wattpad.com/story/240284722?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_reading&wp_page=reading&wp_uname=KhadeejaCandy&wp_originator=Cq%2BoU%2FS0Yt8EYG4ZuWXIrcPLtvMV3Yp1Xa0ZiS9AC0SgFQFRtl%2Beh5SiD11fLE%2FaNoz5iaTQIGz%2FuSuAvbcJBa4hsJzESJfsDBE7wl1CdXGgHAhOSK0sQqZ5%2BLHD0JLJ
CIWON - SO
By Khadeeja Candy
ZAHRA POV.

Bayan mun gama cin abinci ya kwashe kayan sannan ya gyara gurin, kana ya dawo ya rika ni na tashi na koma dakin na zauna, shi kuma ya fita falon domin karasa gogarsa.
will be there Zahra
Yana rufe bakin ya shigo dakin ya zauna kusa da ni.
e kike so?
ayarka zan yi game
Be ce min komai ba ya tashi ya fita falon ya dauko wayar ya miko min sannan ya koma ya cigaba da gugar.

Daman na san password din wayarsa kamar yadda ya san nawa, duk abun da nake so ina yi da wayarsa haka shi ma yana daukar tawa yayi bukatarsa.

Kai tsaye na cire password din na shiga cikin wayar na danna game din da nake so na soma yi.

A lalace na bata awa daya da rabi ina game din ina hamma abun ka da raguwa nan da nan bachi ya sace ni.

Ana daf da kiran sallah magariba na farka kaina yayi matukar nauyi alamar bachin na ishe ni har na wuce ka'ida.

As usual ina farkawa na ga Deen ya lullube ni da blanket daman ya saba idan ina bachi sai ya gyara min bachin ya lullube ni, wayarsa kuma na rumgume a kirjina that's means be fita da wayarsa ba, wata kila yana gudun na farka ne shiyasa be daga hannuna ya dauki wayar ba.

Mika na fara yi sannan na tashi na shiga bandaki na yi alwala na fito na gabatar da sallah la'asar ina zaune ina lazimi har aka gabatar da sallah magariba.
Chapter 4 · 0% Book details