← Book details Ciwon So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 134

Sashe 19

Ciwon So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ko su lalata masa rayuwa?
mmy da dai kin yi hakuri kin saurara na wani lokaci bana tunanin Mai Martaba zai yi haka saboda ya musgunawa Abiey...
a Hajiya Zuwaira ni ba irinki bace da zan sakewa kishiyoyi dama suna yadda suke so, ba zan bari a raina min da ba, ni na haifi abina ni an san wahala da zafin abuna, babu abun da muke nema gurin Mai Martaba kin sani, ko yau Mai Martaba ya fadi ya mutu zan iya ciyarda iyalansa har kashen rayuwarsu, bana bukatar komai daga gurinsa balle kuma abokan zamanki, dan haka bana tsoron kowa a cikinsu, ke dai da kika ga zaki iya zama a raina ki, a raina yayanki sai ki yi ta tsoronsu
Anty Amarya ta yi murmushi.
a tsoro ba ne, mahakurci mawadaci wata rana sai labari, su ma da suke ganin sune da gida ba a haka za a dauwama ba
oh ki zauna nan kina tsoronsu, shiga ki sanar masa ina son magana da shi
Anty Amarya ta yi murmushi mai sauti ta nufi kofar da zata sadata da bangaren Mai Martaba, Abiey dai kansa na kasa be daga kai ya kalli Ammy ba, kuma be saka bakinsa ba.

Ammy na tsaye har Anty Amarya ta fito ta yi masa iso suka sake shiga gurin a tare.

Har turakar Mai Martaba Anty Amarya ta shiga da Ammy saboda Mai Martaba ya bata umarnin haka.

Ammy na shigowa dakin Anty Amarya ta juya ta fice, sai Mai Martaba ya dago kansa a hankali ya kalli Ammy dake sanye da buba ta farin lace da farin mayafi jakarta rataye a hannu.
a ji ance ka saka wa dana masu tsoro saboda me?

Ta aika masa tambayar kai tsaye abun da ba a taba masa ba, kuma babu wanda yake masa haka ya zauna lafiya sai tsohuwar matarsa uwar dansa.
ambayarka na ke, ko wadacan isassun matan na ka ne suka kawo shawara?

To Dana be so
Uffan Mai Martaba be ce mata ba, sai kallonta yake da duban mai wuyar fassara, domin babu alamun fushi ko bacin rai a tare da shi, kallo ne irin na wanda ido suka yi marmarin gani da kuma burgewa.
ana ba mashaye ba ne, balle ka ce maye yake, ba manemin mata ba ne balle ka ce zai lalata maka sunan zuri'a, to ba shi dogarawa na meye?

Daurin zane na baya ga walle?

Kai da ka gama kwance masa zane a kasuwa sai kuma ka dawo gida ka ce zaka daura masa?

Ai duniya ta gama sani kuma ka riga ka nunawa kowa Aliyu ba shi da uba...
biey ba shege ba ne...

Mai Martaba ya fada a tsanake yana taron numfashinta tun gabanin ta karasa furucinta.
o miye ya rage?

Tun na haife shi ka taba saka hannu ka dauke shi?

Ko ka taba tambayar lafiyarsa, da na bar gidanka ka taba aikawa a dubo lafiyarsa?

Ko ka taba taba siyen tufafin naira biyar ka aika masa?

Sai yanzu?

Ka ce zaka juya shi yadda kake so?

Saboda ka auro Matar kwarai ta dawo tana neman cilasta muku alaka kai da shi?

Aa ba zan yarda ba babu wanda ta haifa min Aliyu a cikin matanka dan haka babu wanda zata bada shawarar yadda zai yi rayuwa, ni ce uwar
ana ni ce ubansa
ar gobe....

Baki da...

Uban diyan da ya fini...

Mai Martaba ya fada a rarrabe irin ta masu isa da Martaba da basa furta magana mai tsawo a jere, yana kallon cikin idon Ammy cike da jin zafin furincin da shi kansa ya san ba karya ta fada ba.

Sai ta girgiza masa kai.
i uban yayana ya mutu, bayan shi kuma ban san wani uban yaya ba, domin Aliyu a gurina shege ne ba shi da uba
Take Mai Martaba ya mike tsaye ya nuna ta da yatsa cikin bacin rai.
akinki kar ya sake furta sunan Abiey idan ba zaki iya kiransa da lakaninsa ba, karki sake kiran sunan Mahaifina
Ammy ta gyara tsayuwarta irin na daman jiranka nake, domin da ganganci take nanata sunan bayan kuma ta san Abiey ya ci sunan tsohon Sarki ne.
ai yake sunan mahaifinka, ni kuma sunan
ana ne
Tana furta haka ta juya ta fice daga dakin fuuu kamar an turata.

Bacin marar misaltuwa ya taru a zuciyar Mai Martaba tun da yake a rayuwarsa baya jin an taba masa cin mutunci irin na yau da Ammy ta yi masa ba tare da tsoron komai ba, babu abun da ya tsana a duniya kamar a ambaci sunan mahaifinsa, komai zaka aikata a duniyar nan idan ka ci sunan mahaifinsa zai daga maka kafa kuma zai girmamaka, yana daya daga cikin dalilin daya saka ya hana ko wace mace a cikin matansa sakawa danta ko yarta sunan iyayensa sai Abiey da shi ya rada masa sunan da kansa, a wani lokacin can kamin duniyar soyayyarsu ta ma'aurata ta rikide zuwa kiyayyah.

Mai Martaba irin mutanen nan da basa wasa da sunan iyayen balle abun da ya shafe su.

A fusace Ammy ta iso falon, sai ta samu Abiey zaune shi kadai yana latsa waya.
ashi muje
Ya dago ya kalleta.
ewa yayi na bar masa gidansa?
a ce maka dai ka taso muje
just want to know so that na bar masa gidan har abada
Furucinsa na karshe ya saka Ammy zubar da makamanta ta matso kusa da danta da ya mike tsaye fuskarsa na nuna ransa a bace yake ta soma masa magana cikin sanyayayiyar murya.
liyu ba a fushi da iyaye, no matter what Mai Martaba zai maka mahaifinka ne ko ka
i ko ka so, and ba zaka tana iya shiga aljanna ba idan babu yardar
aya daga cikinmu, ya alla ni ko shi, matukar kana son ka yi albarka dole na ka bi mahaifinka, so ka saka wannan a zuciyarka ba zaka taba fushi da mahaifinka ba zaka tana rabuwa da shi ba har sai idan mai rabawa ce ta raba, but for now he need some space ka san bana son abun da zai bata maka rai Autana?

Zo mu je
Ta karasa tana kai hannunta ta rika hannunsa su nufi kofar fita falon, duk abun da ke faruwa akan idon Anty Amarya dake tsaye upstairs tana kallonsu cike da burgewa, sai dai bata nuna tana ganinsu saboda ta bawa Ammy damar natsar da danta da kuma fada masa gaskiya irin ta uwa ta gari.

Ammy na fitowa daga falon Anty Amarya ta kusa cin karo da Mama Lami dake kokarin shigowa falon rike da bandir din kudi a hannunta, da alama wani ya labarta mata cewar an ga shigowar tsohuwar matar sarki a gidan, domin ba kasafai kake ganinta gurin Anty Amarya ba sai irin wannan ta samu, kasancewar kowa da bangarensa kuma da masu yi masa hidima ga kuma yayansu, sai dai idan Ammy ta zo gidan da kanta take zuwa gurinta ta gaisa da ita ko kuma ta fakewa da ta zo gurin Anty, idan ba haka ba ko kusa da part din Anty Amarya bata bi, Anty Amarya dai ce take biye da su kullum kamar yarsu.
a Maa Shaa Allah, Hajiya Umaima yau a gidan na mu
i ce, ai kin san idan aka gan ni a gidan nan
ana Aliyu aka ta
aba dai Hajiya ai ba a cin gira kusa da ido, ko ba komai an mun ci ki a sakaya sunan Abiey, kuma yan iya magana sun ce ka ki naka duniya ta so shi
o ni na so
ana, ki buga tambura ki yi shela ki ce duniya ta ki Aliyu
Murmushi Mama Lami ta yi tana kallon Abiey da tuni ya kai gurin motarsa domin basa shan inuwa
aya da Mama Lami duk cikin mata mahaifinsa ya fi tsanarta kara ma Hajiya Kilishi yana daga mata kafa sosai, amman Mama Lami ko Anty Amarya ta cilasta shi gaisheta ji yake kamar tace ya cire ranshi ya bata.

Dauke kai ta yi ta tura kofar dakin Anty ta shiga tana dariya, Anty na ganinta ta karasa sauko da take suna gaisawa.
ai ni Umaima tana ba ni mamaki, ka bar gida amman kishi baka bar shi ba?

Ko gani take kamar ni na kashe mata aure da Mai Martaba ne?

A duk lokacin da zan hadu da ita magana sai wance ta manta?

Anty Amarya dai bata ce komai ba bayan murmushin da ta yi ta mika hannu ta karbi kudin da Mama Lami take mika mata.
ar ribar da aka samu ce ta watan daya shige Mai Martaba ya bada yace a raba, shi na na dan debo miki ke da su Aisha
oh mun gode Allah ya saka da alheri ya karawa yi ma arziki albarka
Ta fada bayan ta karbi kudin, Amin ma wuyar fitowa take a bakin Mama Lami idan isar ta tashi haka tasa kai ta fice ba tare da ta amsa addu'ar da Anty ta yi ba.

Sai da ta fice sannan Anty ta girgiza kai.
hmm wasu mata na mulki, wato har an kawo an raba ban sani ba sai da aka debo aka sammana, akwai Allah ba a nan zamu dawwama ba Lami
Ta fada tana jin wani kololon bakinciki na taso mata, haka suke mata sun maida ita ba kowan kowa ba a gidan, tana cikin gidan sai a yanke hukunci ayi komai bata sani ba, yaya biyu ma da Allah ya
bata sai sun ga dama Mai Martaba yake musu abu, kuma abun da duk suka ce haka za'ayi musamman ma Mama Lami, Anty Amarya kam da ita ta banza duk daya a gidan aikinta kawai ranar girkinta ta yi girki ta shiga ta kula da mijinta, amman komai na shi bata sani ba kuma ba a iya yanke hukunci tsakaninsa da shi sai abun da abokan zamanta suka yanke.

ZAHRA POV.

Bayan sun kwantar min da shi a saman gado suka fice suna masa addu'ar samun sauki, ni kam ban da aikin hawaye babu abun da nake, na kai hannu na taba shi na dauke na tambaye shi me ke masa ciwo amman be amsa min ba, sai runtse ido yake alamar yana jin azabar ciwo.
Chapter 19 · 0% Book details