← Book details Ciwon So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 71 OF 134

Sashe 71

Ciwon So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kallona yake yana zagaye fuskata da idonshi can ya sauke gurin bakina yana kallon lips dina.
ada min ya kuke kare da Abiey?

Ina son sani abubuwa akanki, saboda ina son zuciyata kara natsuwa da ke
Na ware hannuna ina tabawa sai idonshi ya koma gurin tsiraran yatsun hannuna.
-Gudu muka rika yi ina ta kiranshi amman be juyo ba kuma ba tsaya min ba har sai da ya ji na fara kuka, na fadi a gurin ina ta kiran Babana da Mama sannan Abiey ya dawo ya kama hannuna yace
i tashi mu gudu mana, bana tunanin a nigeria muke fa, duba wannan dajin babu kowa babu haske, kuma tafiyar da na yi be wuce daga nan zuwa can ba ina nemanki sai hango ki na yi a tare da matar nan amman duba gudun da muke amman har yanzu ba mu kai gurin mutane ban ga alamar titi ba
Kuka na fara yi domin na gaji sosai.
i ba zan iya gudi ba na gaji da yawa
aka zaki daure waya ce ki kawo mu nan, tun da nake a rayuwata ban taba shiga hatsari irin wannan
i kai ka kawo mu kai ka yi min dinki da baka dinka min wannan lace din ba da yanzu ina can gida ina bachina, amman kai ka dinka min ka kuma ka kawo nan
aifin ki ke kika ji maganar iyaye ki ai, da kin ji maganarsu da duk haka be faru ba
o waya ce na bijire musu ba kai ba, kai ka dinka min kaya kuma ka dauko ni ka kawo gurin bikin aljana Allah ka dai ya sani gaskiya wata kila kai ma aljanin ne
mman da na kawo ki ai na ce ki tashi mu tafi kika ki ko?

Kuma da kin fada min cewar Mamanki ta hana ki zuwa ba zan yarda na kawo ki ba, gashi nan abun da kika ja mana ai
Na fisge hannuna.
biey mu ga kafarka
Tsaki yayi ya mike tsaye ya fara tafiya, sai na saka kuka ina ihu idan na yi ihun sai murta ta amsa amo, da sauri ya dawo ya fara kokarin rufe min baki.
i yi shiru Zahra karki ja mana wata matsalar haba, kina jin yadda muryarki take amsawa kin san ba a duniyar mutane muke ba
an yarda da kai ba, mu ga kafanka
Ya daga wandonshi da sauri ya haska kafar da wayarshi, farar fata na gani irin ta mutane amman ban gansu ba har sai da na kai hannu na taba, ban ji gashi irin wanda na ji a gurin wacan yarinyar Aljanar mai kafafuwan doki ba, hakan kuma be kara gamsar da
ni ba sai da na dankara mashi kwanta har sai da yayi kara.
iye haka?
abbatarwa na yi, yanzu me zan fadawa Mama?

Kuma na san Deen sai ya kusa kashe ni idan na koma gidan
Na fada cikin kuka ina tuna irin azabar da Deen yake ba ni idan ya ga na tsaya da wani balle kuma ace na bi namiji na shiga motarshi.

Ya sake kama hannuna.
i hakuri ta so mu tafi
Na mike tsaye muka cigaba da tafiya cikin tsoro yana rike da hannuna gam.
arki juya, ba a son tafiya ana juyawa
Da dukan alama shi ma tsoron be gama fita cikinshi ba, idan ba haka ba taya zai ce min wai kar na waige ba a son waige idan ana tafiya.

Kyalkyalewa na yi da dariya sai yayi saurin sakin hannuna.
ahra ke ce?

Ina jin haka na san tsoro yake ji sai dariyar ta kara taho min.
an taba ganin namiji mai tsoro ba irinka, ashe ma kai matsora ci ne
t's not funny Zahra baki da hankali ashe, now i understand why ake dukanki a gidanku taya zaki fara mana dariya muna cikin wannan halin
aka ka wuce ni fiuuuuuu kamar iska
Na nuna yadda yake gudun ina cigaba da dariya, sai gashi shi ma yana dariyar, tafiya muka cigaba da yi har muka gaji muka samu gindin wani ice muka zauna ni da shi, sai ya jinginar da wayar tsakiyar mu nan tsoron ya sake dawo min.
a kira waya mana ka fadawa Babanka ko Ammy, ni tsoro nake ji
etwork din ya dauke ai, da tun kamin ki fada na kira
anzu ya zamu yi?
aya sani kin janyo mu kin kawo a nan, Allah yasa idan kika koma gida ayi miki shegen doka
ai ma Allah yasa idan ka koma Babanka yayi maka shegen duka
Ya kalleni.
a ace Babana zai doke ni ko ya hukunta idan na yi masa laifi da zan fi kowa farinciki da jindadin haka
aboda?
aboda mahaifina ba kamar mahaifinki ba ne, ni nawa mahaifin babu ruwanshi da ni, idan na ci ko ban ci ba, ba damuwarshi ba ne idan wani abun zai same na fadi na mutu ma ba zai damu ba
a masa laifi ne?
an masa laifin komai ba domin na tashi ban san wani abu soyayyar mahaifi ba, ko riga daya be taba siya min na saka ba, a gidan Ammy na bude ido ita ce uwata ita ce ubana, ita take hukunta ni idan na yi laifi kuma ita take cilasta min zuwa gidan mahaifina daga ita sai matarshi ta uku Anty Amarya ita ma tana so na sosai kuma tana nuna min kulawa tana neman duk wata hanya da zata shirya tsakanina da mahaifina
ada kuka yi?
a mu yi fada ba Zahra, ko da na bude ido haka na samu kaina cikin tsanar mahaifina ban san dalili ba, amman abun nan yana min ciwo sosai, amman kin yi dace ba kamar ni ba Babanki yana son ki
a fini sa'a domin kai ka ga mahaifinka, ni kuma ban san nawa uban ba, Mama ta fada min tun ina ciki ya rasu ban taba ganinshi ba sai a hoto, sai abokin shi na sani wanda shi yake auren Mama ta a yanzu
Kamin na karasa maganar hawaye regen regen sauko min yake, domin ni ma ina da wannan tabon na rashin sanin mahaifin ko sau daya ban taba jin muryarshi ba, balle na yi rayuwa da shi.
llah ya mishi Rahma
meen
Na share hawayen sai ya rika kaina yana kokarin kwantar da ni kan kafadarshi na buge masa hannu.
ai wai miyasa kake taba ni be kamata ba fa, ni dai ba yar iska ba ce
i kuma dan iska ne ga iskanci nan rubuce a goshina, daga taimako, ai gashi nan kin jefa mu cikin wannan halin
i nima bana son taimakonka daga yau, ba ni ba kai daman ba san haka za a fada min a gida, kuma zan fada musu cewar sace ni ka yi?
a aka yi na sace ki?

Ai babu wanda ya gan ni gidanku kuma ban san hanyar gidanku ba
Ina ganin ya mike tsaye ni ma na tashi sai ya dauki wayarsa ya matsa daga kusa da ni, binsa na yi da saurina.
in ce ba ni ba ke
Ban sake ce masa komai ban kuma daina binsa ba, har muka samu wani fili muka zauna a guri ni dai kamin wani lokaci bachi yayi gaba da ni, ban farka sai da safe ina bude ido na zabura na tashi zaune ina waige waige can na hango shi zaune yana ta daga waya sama da alama network yake nema, da sauri na tashi na karasa inda yake zaune.
a kira gida ne?
etwork din ne sai ya kawo ya dauke gurin nan ba network daman ke na ke jiran ki farka mu tafi
Na waiga ina kallon ko'ina na dajin, irin dajin nan ne mai kama da tsohuwar gona idan an cire amfanin gonar babu komai a ciki sai haki da ciyayi.
biey a ina ka kawo ni?
a za'ayi na sani?

Ki kabe kanki akwai kasa
Na kabe dogon gashina da ya gama hautsinewa saboda wahala dankwalin da mayafin ma ban san inda suke ba daga ni sai doguwar rigar lace din da aka dinka min jiya, kama hanya muka yi muna ta tafiya cikina sai kukan yunwa yake min ga gajiya, daker da tsudin goshi muka fara hango mutane, kamin mu karasa gurinsu na yi kuka har Abiey ya gaji da ba ni hakuri ya saka min ido.

Mutanen kauyen mutane masu karamci da son mutane sosai sai da suka fara ba mu abinci da ruwa, Abiey yayi fir shi ba zai ci ba, ni kan na zauna kamar a gidan mu na kwashi tuwona na ci na koshi ba wani kyama na sha ruwa sannan suka ba mu guri muka yi na yi sallah, bayan na gama na dawo kusa da shi na zauna.
biey ka je ka yi sallah?
a yi sallah tun a inda muka kwana na yi taimama a gurin na yi sallah, yanzu kuma na kira Ammy na fada mata muna garin Bagar (Fake name)
a aka yi ka san sunan garin?
utanen garin suka fada min, kuma na yi browsing na gani
o yanzu tafiya zamu yi?
a a nan zamu jira su har su zo
mman dan Allah idan mun koma gida ka je gidan mu kace musu sace ni ka yi ka ji?

Ya wara ido yana dariya.
a saka kaina a bala'i kenan?

Ya aka yi ma muka zo nan?

Ko ina motata?
aya sani, ashe kenan wannan yarinyar da muka bi tafiyar da ta yi da ni har mun iso nan kenan?
Chapter 71 · 0% Book details