← Book details Ciwon So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 88 OF 134

Sashe 88

Ciwon So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kowa tsoron amsar da za'a bashi yake yi, jim kadan ta dawo masu da wayar ta mika masu muryarta na rawa sosai ta ce" Ku je ku daura alwallah, kowa ya gabatar da abinda ya iya wa mahaifinku, Allah ya bashi lafiya"
Adawiya mai saurin kuka ce ta shiga yi tana matsowa kusa da Aunty Amarya ta ce" Aunty, ya rasu ne Aban?"
Idannuwanta da suke dauke da kwallah ta dora a saman fuskar Adawiyar a sanyaye ta girgiza kanta ta ce" Bai rasu ba, ama bashi da lafiya, su Hajia ba gobe zasu juyo ba, dole sai sun sake kwana dan a ga yadda hali zai bada, ku dai ku rike carbi Allah ya tashi kafadunsa"
Da wannan ta salame su ta juya nata dakin ta karasa saman salayarta ta zauna
A hankali ta sada kanta waje daya, sai kuma ta fashe da kuka, kuka mai tsatsanin gaske tana jin tamkar zuciyarta zata bar gangar jikinta......., Innalilahi wa inna ilaihi raj'une ga abinda suke fada mata.....ga abinda maman Abul ke fada mata da kuma maman Furera, .....a lokacin da suke tunanin itace ta tsiga tsakaninsu da mijinsu ba zuwa ba zowa gan lamarin aurataya sai suka sakota a gaba da yan habaice habaice kamar haka :sukan ce mata ta fa yi aniya a dakan da take saka shi ya bata koda cikin y'a mace daya ne, dan idan tana da hankali zata kula Docter dai shekaru karta ja suke ita kuma a cikinsu itace yarinya futul itace ba d'a ba jika tsakaninta da shi, ta kuma sani sarai cewa wannan gida da ake ciki gida ne da yake malakin MARSHAL, gidan docter wanda suka taso suka dawo wannan ko rabin rabin wannam bai kai ba duda shima gida ne na masu kudi gaskiya, sai dai a lokacin da ya fito ya ringa dauka gaba daya ya raja'a ya maka ginnin nan bulo da bulo hawa da hawa wajajen shakatawa kala daban daban wajen karatun islamiya kai babu ce kawai babu ya zuba mahaifinsa da makarabansa dan karra samun jin dadin rayuwa, ta fa sani idan har Docter ya mutu a lokacin da bata da d'a ba jika tsakaninta da shi tana cikin matsala, dan kuwa cimilin takaba ne kawai zata iya samu, gwara gwara su idan aka dan duduba ta yiwu da yan motoci da gonaki haka jefi jefi sai gidajen nan nasa uku wa'inda ake haya a cikinsu baki daya, idan aka raba ta yiwu su samu matsugunni , ita kam sai dai a koma rayuwar da........watau rayuwa a bakin titi ana neman na abinci , ana bara ana karuwa ................

Wadinnan kalamai su suka fi daga mata hankali, dan ta san wace rayuwa ce ta baro ta bakin titin, lalle bara kam ta yita ama kuma karuwancin bata taba yi bama, sai dai ta fuskanci kalubale da tashin hankali daga wasu mazan azalumai masu son wulakantar da mace, wa'inda idan suka ganki a halin kaka naka yi baban burinsu su ribanceki su idasa wulakantar da darajarki a banza a wofi dan baki da yadda zaki yi........., Magangannu mararsa dadi da sauransu, shi yasa tunda ta samu kilacewar nan sai ta sake kilace kanta, abu biyu kawai ke fitr da ita koyon girki a lokacin da take amarya, sai kuma islamiya....summa tana samun abinda ta samu ta dawo ta kilace kanta, bata da kawa, bata da abokin shawara sama da Docter, bata iya sakin karinta ta yi hira da kowama in ba shi din ba....................

Wannan zulumin ya hannata barci, kira kuwa ta yiwa Mamah ya fi a irga har sai da Maman ta kashe wayarta dan gaba dayansu ta sanarwa ama Aunty amarya ta gaza zama waje daya , karshema haka asuba ta risketa garin Allah ya waye tana cikin hali na kuncin zuciya da tashin hankali, har suka fito suka tafi wajen karatun da aka yi kiran kowa aka hadu ana sauke Alkur'ani da sadaka.....jikin Docter kam ya kiya sai fatan samun lafiya ko wace iri ce, hankalin iyalansa gaba daya a tashe yake, basu taba yin wuni tare ba dai a wannan lokacin, abinci zubawa ake ana kaiwa cen bangaren na docter domin a cen suke iyalan nasa baki daya, hankali du ba a jiki ba, babu mai hararar kowa, kowa yana cikin zulumi
A hankali yayansa na nesa suka fara matsowa sanadiyar kiran da suka ringa samu da iyayensu
Mazan ne, da matan masu aure, daidaiku ne basu samu zuwa ba dan mazajensu sun ce su bari ya dawo mana mutumen da ba rasuwa ya yi ba zasu ringa zuwa sunna dagawa junna hankali, aduarsu yake da bukata fiye da komai
A irin wannan hali ahalin gidan Docter suka dauki kwana biyu bayan kiran Mamah sunna cikin hali na zulumi, sunna karatu ba ji ba gani da sauke Alkur'ani, ana sadaka ta launin abinci kala kala da ta suturu da ta kudi, sosai suka ninka alkhairansu , wanda hakan ya zamto baban abu mai daraja, domin har a masalacin Docter abinda ake yi kennan, ana cikin roka masa gafarar ubangijinsa domin su Marshal ya fito masu karara ya sanar masu ne Docter na bukatar addu'a, dan tunda ya shige halin comar nan bai kuma sannin inda kansa yake ba
Tun karfe hudu da rabi Amir ke kai kawo a baban tsakar gidan yana sanye da jalabiya fara hannunsa rike da carbi, idannuwansa sun gaza daina zubar da hawayen da suke tarawa yana kai kawo yana ankare da dukkan wani motsin dake kai kawo sanadiyar abinda ya same su iya mazan suka ji banda matan da suke falon Abah yanzu yake sa ran gannin sun bude dan ya sanar masu domin baya so su ji daga bakin wani
Alamun an fara kukunna wutacen falon ya saka shi sake sauke wani hawayen mai zafin gaske, a hankali ya karasa ya dan dakata dan ya basu damar kimtsa kansu, dan tashi daga barci ai ba kowa ke yi tsaf tsaf a nutse ba
Ya dauki minti kusan goma a tsayen nan ya shiga bubugawa a hankali sannan ya dakata
Ba'a jima ba aka tambayi wanene, dan du sai suka tsayar da abinda suke yi na shirye shiryen daura alwallah da hawa saman salaya, shake falon yake da iyayensu da
ansu a haka ya shigo yana dan cicira ido ya rasa inda zai fara nufa dan a gaskiya bashi da wannan courage din a yanzu a gabansu
Uman Abul ne take saukowa daga saman Abah hankalinta a kan abinda yake faruwa
Jiki babu karfi ta karaso tana fadin" Lafiya du kuka yi tsaye kunna kallonsa?

Yayansu lafiya dai ko wani ne ya aikata laifi?"
A hankali ya ja numfashi ya sada kansa, muryarsa a sanyaye ya ce" Aa, babu wanda ya aikata wani abu, shigowa na yi na sanar maku cewa, yau mun tashi da kyautar Ubangiji"
Da sauri ta sake kureshi da ido, lokaci daya kuma Aunty Amarya dake tsaye saman salaya ta silale ta zauna tana tataro kafafuwanta ta dora gwuiwoyin hannayenta sannan ta kai tafukan wajen kanta tana yamutsar kan nata bskinta ya kasa furta komai
Mahaifiyar Furera ce ta ringa ambaton innalilahi wa inna ilaihi raj'une, domin yannayinsa zai sanar masu kyautar ubangijin me take nufi
"Kana nufin Docter ya rasu?" Maman Abul ta fada muryarta na wani irin rawa, hajan ya sa yan matan da yayunsu masu auren barkewa da kuka kowa na rungumar wanda ya fi kusa da shi, shi kuma ya karaso jikinsa tamkar an zare laka ya zauna a saman kujera a sanyaye ya ce" Allah ya amshi ran Abah, karfe uku na dare da wasu yan mintuna"
A hankali itama ta bi ayarin matansa dake kuka da ya'yansa, muryarta a matukar jigace tana kallon Amir ta ce" Shikenan Amir Abah ya rasu?

Wayo Allah mun shiga uku mun lalace, innalilahi wa inna ilaihi raj'une innalilahi wa inna ilaihi raj'une, dama tafiyarsa ba ta dawowa bace?"
"Amir yanzu shikenan a akwati za'a sako gawar Docter a kawo a wuce da shi makwontai mu ko ganninsa ba zamu yi ba?, Shikenan mun rasa uban y'ayanmu ya tafi da kaffafuwansa a dawo mana da gawarsa a cikin sanduki?

Menene zai saka mu samun nutsuwar zuciya bayan bamu ga gawarsa ba?, Menene zai sanyayar mana da zuciyarmu?

Shi yasa yake gudun fita wajen nan, fin karfin Docter aka yi aka fitar da shi waje, gayacen ya rasu za'a kunkuma mana shi a cikin samduki a kawo a wuce da shi a turnutse a kabari ba tare da mun yi ban kwana ba?" Maman furera ta fada tana hawaye hankalinta du ba a jikinta ba
Murya a sanyaye Aunty amarya bayan ta bi yan matan da kallo du sun warwatsu kowa yana neman inda zai saka ransa ta ce" A nasihar Abah, yace du inda ransa ya fita a birne shi a nan, kasa ta kai shi"
A zabure Maman Abul ta dubeta ta ce" Kina nufin ba za'a kawo mana uban y'ayanmu kasarsa garinsa inda aka san darajarsa aka san mutincinsa a birne shi ba?, Ai ba zai taba yiwuwa ba, in dan tashi ne ai shi komaima ya yi yadda ba zai wahalar da dan gwal din ba!, Dole a kawo mana mijinmu a birne a garin da muke ko dan ya samu kyakyawar ziyara da addu'a ta kirki "
Uhum, wasa farin girki, Amir sai ya rasa bakin magana , ya ringa bin wani gagarumin rikici da tashin hankali da yake gani a gaban idannuwansa wanda Mahaifinsa ya tafi ya bari, ama ya bar wa da shi?

Innalilahi wa inna ilaihi raj'une abinda yake kallo a yanzu ya karra daga masa hankali da shiga tashin hankali da tonon asiri irin na mutuwa, wai wadinnan ahalin da Docter ya bari wa ya barawa, ya Allah, wannan lamari ya sake gigita shi, ya sake saka shi shiga a hali na tarin tunanin shin yaya zasu yi?
Chapter 88 · 0% Book details