← Book details Ciwon So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 134

Sashe 1

Ciwon So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Root Entry
WordDocument
0Table
Data
Normal
CIWON - SO
_Alhamdulillah Maa Shaa Allah, ga ni tafe dauke da wani sabon labari mai suna CIWON SO hausawa suka ce mai wuyar magani...

Wannan karon na ce bari na gwada labarin soyayya na ga ko zan iya
ku yi addu'ah kar na baku kunya, kun san na fi kwarin gurin saka tashin hankali da kuka best on reality, but i will try my best na ga na baku abun da kuke so da yardar Allah
*Ni Khadeeja Candy ina gaishe da masoya a duk inda suke ina muku son so
annan nasarar da na samu ba tawa ba ce ni kadai, nasara ce gaba daya ta club dinmu a bisa kokarin da coach dinmu yake yi.

Na gode
Anty Amarya ta yi murmushi zuciyarta fes tana kallon yadda danta yake jerawa yan jarida da suka tsare shi da tambayoyi amsoshinsu.

Ta ko wane gefe daukarsa hoto suke kamar za su cinye shi, coach dinsa na zaune daga dama, sai kuma shugaban kungiyarsu dake zaune a hannunsa na hadu dukansu fararen fata ne ban da danta.

A hankali ta dauke kai daga kallon katuwar plasma ta kalli agogon GMT dake tsaye a yawantacen falon da aka kawata da kayan alatu kamar ba za a mutu ba.

Unkurin tashi tai wanda hakan yayi daidai da shigowar kira a iPhone din dake hannunta.

Sai da ta kara fadada fuskarta da murmushi sannan ta amsa kiran ta kai wayar a kunnenta.
nty An tashi lafiya?
lhamdulillah
biey yana gida tare da ke?
anzu zan tashe shi
aba Anty tsakani da Allah baku kyautawa, ace ya kai har wannan lokacin yana bachi?

Na tabbatar da aurensa ake Sauban ba zai kwana a ko'ina ba sai tare da shi, idan ma ya kwana wani gurin ba zai kai yanzu ba ace baya kusa da Abiey
arfe daya na dare ya sauko garin nan jiya, kuma kin san yana tare da gajiya, amman yanzu zan tashe shi
hiyasa ai ya kwana a gurinki, ya san da a gidana ne be isa yayi wannan bachin ba
Ammy ta fada cike da rashin jindadin da ya bayyana a fuskarta.

Doc Zainab dake zaune gefenta ta tabe baki.
ina kara tsawaita zancen ne kawai Ammy, the more you talk the more Anty zata bar shi ya kara samun bachi, sai a daura auren ma a gaba tace ta manta bata tashe shi ba
Duk abun da Doc Zainab take fada Anty Amarya tana jinta domin tana zaune ne daf da Ammy.

Murmushi kawai Anty tai ta kashe wayar ta mike tsaye ta nufi upstairs.

Kofar farko ta fara turawa a hankali ta shiga dakin dake cike da sanyin ac, duhu ne ta ko'ina kamar ba safiya ba, wutar dakin Anty ta fara kunnawa, haske ya cika ko'ina na dakin.

Can bakin gado ta hango danta kwance ya yi ruf da ciki idonsa a rufe.

Karasa tai kusa da shi tana kallon kyakkyawar fuskarsa, hannu ta kai ta taba gashin kansa a hankali.

A take ya bude fararen idanuwansa dake nuna alamar ba bachi yake ba ya kalleta.

Ta dan wara ido still murmushinta na shimfide a fuskarta.
a bachi kake ba?

Ya maida idon ya rufe yana amsa mata.
a kasa bachi
a yi zaton kana bachi ne, shiyasa ban tashe ka ba, yau fa auren Sauban ko ka manta?

Ya dago ya kalleta.
o saboda shi na dawo jiya remember?

Amman yau ina jin kamar ba zan je ba
Anty ta saka hannunta a yalwataccen gashin kansa tana shafawa a hankali.
anar yau, rana ce mai muhimmanci a rayuwar Sauban, rana ce da ba lallai ne ya sake maimaita irinta ba, a matsayinka na amininsa ya kamata ka kasance tare da shi
Anty ta fada sannan ta mike tsaye ta nufi closet dinsa ta bude, wata tsadadden gizner ta dauko ta dora masa saman gado.
ari na shiga bangaren mai Martaba na samo maka hula mai kyau, tun da kai ka watsar da al'adarka ta saka kayan hausawa, but make sure kamin na dawo ka shirya, Narjis zata kawo maka breakfast yanzu
Ya sauko da kafafuwansa kasa yana girgiza kai.
o Anty ba zan iya cin komai ba a yanzu
iya ma da ka dawo baka ci komai ba, yanzu kuma ka ce ba zaka karya ba?

Abiey shin ba kai ka fada min komai zai wuce ba?

Ya sauke kansa kasa yana murmushin dake nuna tsantsar bakinciki da damuwa a tare da shi.
omai zai wuce Anty, komai zai zama labari, amman hakan ba yana nufin kaunar Zahra ta fita daga zuciyata ba, son Zahra ya aure ni kuma na auro Anty, ina rayuwa ne kawai saboda sonta yana raye a tare da ni, daga lokacin da kaunarta zata bar jinina, a lokacin ne zan nisanta da rayuwa, na yarda komai zai wuce amman ban da son Zahra
Ya mike tsaye ya nufi windows din dakin ya bude curtains din da suka tare glass door dake dakin, wanda hakan ya bawa rana damar hasko ilahirin dakinsa.

Anty ta juya a sanyaye ta fice,
bakinsa ya cika da iska ya soma busarwa a hankali.

Sannan ya juya ya shiga bathroom dinsa, kamar wanda ake aka cilasta haka yayi wanka ya fito ya nufi dressing mirror.

Tsayawa yayi kallon kansa yana murmushi,
ahra kin tuna?

A irin wannan ranar ni ango ne, ina sanye da fararen kaya, ke kuma kina a dayan dakin ana miki kwalliya, kin kira ni a waya kika tambaye ni, wane kalar kaya ka saka Abiey, sai na fada miki fararen kaya na saka, gashi ma ana fesa min turare, kika yi min dariyarki mai dadin sauraro kika ce i can't wait to see you Angona!...
biey
ana...

Ya juyo da sauri yana kallon Anty dake rike da sabuwar hullar Mai Martaba.
ahra ta dade da mutuwa, ka saka wannan a ranka, ka bude zuciyarta gaskiya ta shiga ka karbe ta
Wasu hawaye ma su zafi sun sauko masa.
ahra tana raye Anty, tana nan tare da ni...!

Ya saka hannunsa yana nuna sautin zuciyarsa.

Sunkuyawa tai a hankali ta aje masa hular sannan ta sake kallon kyakkyawar fuskarsa da hawaye ke zarya, ta juya ta fice ba tare da ta sake ce masa komai ba.

Tana tura kofar dakin ta nufo downstairs tana saukowa a hankali hawaye ya soma taruwa a idonta.
llah ya sassautawa yaron nan, ka kawo masa dauki
Cikin rashin jindadi ta sauko downstairs ta nufi dinning.

Narjis dake aikin hada ma yayanta breakfast ta kalli yar'uwarta Aisha sannan ta kalli Mahaifiyarta.
nty....

Anty Amarya ta kalleta cike da damuwa.

Aisha ta yi sauri aje wayar hannunta ta taso ta nufo Anty cike da kulawa.
iya faru Anty
biey ko?

Narjis ta tambaya sai Anty ta daga mata kai hawaye na sauko mata.
an taba ganin wani mutum da zuciyata take matukar tausayinsa kamar Abiey ba, duk lokacin da wani abu zai same shi no matter how little it's, abun nan sai ya cige ni
Taja kujera ta zauna sannan ta kalli Aisha.
da ina ganin kamar hankalinsa ya kwanta komai ya wuce, amman dawowar nan da ya yi, tsakanin jiya zuwa yau, gaba daya ya canja kamar yana kokarin fita hayyacinsa ma, domin a yanzu har magana yake da kansa abun da be saba ba
nty, ina jin kamar auren da Sauban zai yi ne, ya saka shi shiga wannan yanayin dole zai tuna da ita
Narjis ta fada tana daukar breakfast din, sai Aisha ta mika mata hannu ta karba.
awo bari na kai masa
Ba musu Narjis ta sakar mata, ta ja kujera kusa da ta Anty Amarya ta zauna.

A hankali Aisha ta tura kofar dakin ta shiga sai ya juyo yana gyara rigar shaddar dake jikinsa.

Tsaye ta yi tana jiran ya karasa sannan ta shigo, kallonta yake yana murmushi gaba daya Zahra yake gani ba kanwarsa Aisha ba, yana tuna lokacin da ta taba shigowa dakinsa ta same shi yana kokarin saka aninin rigarsa ta suit sai ta tsaya tana kallon kirjinsa, sai da ta gama kallonsa har ya daga mata gira daya, sannan ta juya da ta yi ihu tana fadin Subhanallahi na yi mugun gani ta fita dakin da sauri...

Murmushi yai mai sauti ya juya ma Aisha baya hakan ya saka ta kira sunanshi.
biey...

Ya juyo da sauri wanda hakan yayi daidai ta dawowar hayyacinsa, arba da ya yi da Aisha ya saka shi daga kanshi sama ya busar da iskar bakinsa sannan ya sauke kan ya kalli Kanwarta.
biey...

Ya nufi gefen gadonsa ya zauna, sai ta nufi wani karamin tebur ta dora, sannan ta dawo kusa da shi ta zauna.
biey yawan tunanin da kake, shi ke jefaka cikin damuwa, damuwarka kuma tana shakar mu
Ya kalleta yana hade yawun bakinsa.
a kasa mantawa da Zahra ne
A take idon aisha ya cika da kwalla.
ukanmu mun kasa mantawa da ita, Zahra mace ce mai far'a mai son mutane babu ruwanta kowa nata ne, Zahra bata da matsala da kowa, tana da ban dariya, wautarta sakarcinta shagwabar ta duka abun burgewa ne, babu wanda zai zauna da ita yace baya son ta, balle kuma kai da so ya shata layi a tsakaninku, ba abu ne mai sauki ba mun sani, amman Abiey ana sassautawa rayuwa saboda a samu natsuwa da sukuni, ko dan saboda mu da Mai Martaba ka tausaya mana, Abiey kai fa Baban mutum ne, dan kwallon kwando da babu na ukunsa a halin yanzu, idan ka shiga wani hali zai taba career ka, kuma wasu za su ji dadi mu kuma mu shiga damuwa har ayi mana dariya...
Chapter 1 · 0% Book details