← Book details Ta Fita Zakka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 90 OF 193

Sashe 90

Ta Fita Zakka Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Ta karishe Fada cikin wani yanayi Lokaci Daya tana komawa ta zauna gefen gado tana jijjiga kafa kamar ta Rufe Sakina da Duka haka take ji.
Sakina ta fashe da kuka kishi da Bakincikinta sun cika mata Kirji Cikin Wani yanayi tace"Haba Anty wannan yarinyar fa..?Wlh bazan iya jure zaman waje daya da ita ba..Dama zaki rokar min Umar ne ya amimce ya koma da ni Madina shikenan sai na Biki mu tafi..!
Anty Amarya ta mata kallon Tara saura kwata kafin ta mike tana Fadin"Kinga in zaki tafi ki zo mu tafi..In bazaki jeba shikenan mu koma mu nade hannu mu zama yan kallo..Wahalarmu tatashi a Tutar babu..!
Anty bata kara bi ta kanta ba ta Fice Daga Dakin kada ta cigaba da zama Sakina ta cikamata ido ta kaimata Duka Tana zaune afalo tana jiran taga Sakina zata fito ko kuwa kasa Zata watsa mata a ido sai gata ta fito Idanuwanan sun kumbura saboda kuka Anty Amarya tayi Mirmishin Nasara kafin ta Mike tana Fadin"Muje na maidake..Karaya ba Halin Madina bane..Ita Nasara insha Allahu Tamu ce Sakina..Kafin su kaita zasu tarar dake agidan Mijinki..Ita ai aro muka bata nan da wani Lokaci zata zama tarihi..!
Sakina sai taji ta samu natsuwa Daki Anty Amarya ta koma ta Dauko wayarta ta Karamar jakarta ta saka Sakina gaba suka fice daga gidan ba wanda ya gansu,Mallam kuma shashensa a kulle kila ya fita adaidaita suka samu suka hau zuwa kofar arewa..!
Buga get din sukayi megadi yazo ya Bude musu bayan yaga sune,Sakina na kan gaba Anty na bayanta suka Shiga Falon gidan da sallama ba kowa Tsit kamar ba Mutum acikin gidan
Anty Amarya tabi Falon da kallo kafin ta kalli Sakina tace"Naji gidan tsit..Ko ya fita ne..?
Sakina ta zare mayafin Jikinta tana Fadin"Bana jin ya fita..ga motarsa chan a haraban gida..a dakinsa na barosa koda na fito Dazun..!
Anty Amarya ta samu Daya Daga Cikin kujerun falon ta zauna tana Fadin"Shiga kicemai nazo ina son mgana dashi..!
Sakina ba Musu ta Nufi Dakinsa Knooking ta farayi taji gyaran Muryansa kafin ta Tura kai ta shiga Dakin komai nashi Baki da Fari ne makeken gado da wardrope sai Cafet sai Madubi,Yana kwance kan gado yayi kwwnciyar Ringigine yana kallon p.o.p din Rufin Dakin yayi matashi da Hannayensa bai da Riga Dogon Wando ne baki ajikinsa Gabadaya Kirjinsa yana waje inda Gashi suka kwanta Luf.
Idanuwansa suna Rufene kamar mai barci sanda ta shigo Dakin yana jinta ammh bai Motsa ba saboda Halin Dayake ciki baya Bukatar hayaniyar kowa akansa yana jin sanda ta Fita bai yi kokarin hanata ba saboda ba shi da kwarin gwiwan Daukan kokenta na banza shi kanshi inda zai yi kukan Dayaji Dadi Ransa gabadaya a jagule yake tsammanin abunda bakayi Tsammani ba baida Dadi sam.
Gefensa ta zauna tana Fadin"Habibi Anty na Falo tana son mgana Dakai..!
Kamar bazai yi mgana ba ta kafeshi da ido tana kallomsa yadda taga kamar yadan Fada mata a fuskarsa da Wuyansa.
Ji kawai tayi yace"Karata kika mata sakina..?
Yafada cikin Sanyim muryansa kamar koyaushe,Da sauri tace"A..a..!
"A"a ko Eh..!
Ya fada Lokaci Daya yana Bude Idanuwansa kuma ya tashi Zaune yana kallonta sai taji ta Daburce ta kasa kallonsa idonta na kasa tana wasa da Zoben hannunta.
Bai kara ce mata komai ba ya Zuro Santala santalan kafafunsa suka nutse saman Italian Cafet din Dake Dakin ya Mike Tsaye yana Fadin"Kije gani nan zuwa..!
Ba Musu ta mike ta fice Daman ta Kosa ta Fita Kwarjininsa yafi na koyaushe bata so ya Tsareta da wannan kallonsa da yake sakawa ka kasamai gaddama ko Karya.
Wajen Anty Amarya ta koma tana Fadin"Gashi nan zuwa Anty Don Allah kiyimai mganar tafiyata..!
Anty zatayi mgana kenan Kamshin Turaransa ya sanar da su zuwansa Falon suka Dago suna kallonsa atare Jallabiya ya sanyo saman wando jikinsa Fara Tas da ita,Anty Amarya ta kalli Sakina tana fadin"Koma kasa ki zauna mara kunya..!
Ba musu ta sulale a kasa shima saman Cafet din ya zauna yana gaisheta ta amsa tana kallonsa ganin yadda yanayinsa yayi wani iri duk da daman bamai gane yanayinsa koda yaushe haka yake.
Kansa na kasa Anty Amarya tace"Ina gida dazu sai ga Sakina tazomin da kuka..ni Hankalima ma har ya tashi na Zata matsala kuka samu..Sai Daga baya take Fadamin wai ka Fadamata Amina Zata tare yau shine tazomin tana min kuka kaji wani Sakarci Umar..?
Kansa na kasa shidai bai ce mata komai ba Sakina ce ta Dago tana kallonta ta Rakata da Harara kafin ta Dauke kanta ta maida kan Umar tana Fadin"Tana fadamin haka ban yi mata da wasa ba nayi mata Fata Fata..Nace wannan ai Sakarci ne..Mallam ya Fadamana da Safe zemcen Tarewar kuma in banda abun Sakina Amina ai kanwa take gareta keda zaki kwantar da Hankalinki ki jata ajiki ki Riketa amana kamar yadda kike rike Sarood ai kece babba Kece zaki samar da zaman Lafiya agidan Mijinki ammh baki dunga wannan Sakarcin ba..Gatanan Dukanta ne kadai ban yi ba sai ta fara kuka tana bani Hakuri nace bani zata bama Hakuri ba sai zata zo ta baka hakuri nace mata me zai dameta ai bata tashi Hankalinta Lokacin auranka da Sarood ba sai kan Amina ta gida ku zaku hade kai ma a matsayinku na yan gida Daya haba Sakina..
In kaji yadda na dinga mata fada sai kace na Sauraramata ta gane kuskusranta Daman kishi ne na hallitar mata ya Rufemata ido..Shine data gayamin bakasan ta fito ba na Daukota kafa da kafa nazo baka Hakuri..Dom Allah Umar kayi hakuri ka kuma Cigaba da Hakuri Nauyi ne ya karu a Kanka sai ka kara Hakuri kasan mu mata sai a hankali Wani Lokaci ana taromu ne muna karkacewa..!
Ta karishe fada tana yar Dariya kansa na kasa yana Sauraranta aransa kuma Dariya kawai yake yi wai ta mata Fada Sakinar ce zatayi ma Fada daman baisan yadda batason damuwarta bane sai dai ko ba domin Sakina ba Anty Amarya Matar Uba take garesa zai bata girmanta yasa ya jinjina kai yana Fadin"Bakomai Anty komai ya wuce..!
Anty Tace"Yauwa nagode..Allah ya Zaunar daku lafiya ya kade Fitina..!
Da ameen ya amsa kasa kasa Sakina ke Zungurin kafarta yasa ta gyara Zama tana fadin"Sannan naji wata mgana Umar..Sakina tace min kace baza ta bika ba madina ba yanzu..?

Sai alokacin ya Dago kansa ya Kalli Sakina kafin yace"Eh Anty..Bata fada miki yadda mukayi da ita bane..?
Anty Amarya tace"Ta fadamin nayi ta Fada kamar zan ari baki..Wlh bansani bane dasani ba zata zo ba don Ubanta Sakarci ke Damunta..Don mai garinku bashi Hakuri yanzu agabana..!
Tafada tana Dungurin kan Sakina wacce ta rankwafa tana Fadin"Kayi hakuri..!
Kallonta yake yi bai yi mgana ba yana Rokon Allah kada kafin ya koma Sakina ta Cikashi taga dayan kalansa Taga bacin ransa.
Ganin yayi shuru yasa Anty Amarya tace"Ta baka Hakuri Umar don Allah ka yafemata in ka tashi komawa sai ta Bika ku koma tare..!
Umar ya Dago kansa kafin yace"Anty mi batamin komai bafa..Mgana Dayace na riga na Rantse bazata Bini ba..Nan din Datake so nan zata Zauna Insha Allahu..!
Sakina ta kalli Anty Amarya itama ta kalleta Cikin Takaicinta alamun ta kara Rokonsa tayi mata bata sani ba Duk yana kallonta aransa yace zaki gane baki da wayau ne sakina..!
Anty Amarya tace"Kadai yi hakuri..In ba kudin Visar ne ni zan Biyamata sai ku tafi taren kaji..!
Kai Tsaye yace"Chan din in ta taka ta koma to bada yawuna ba Anty..nima ban rasa kudin da zan Biyamata ba kawai Ra"ayina ne bazata Bini ba..Ita ta sani nayi Rantsuwa kuma akanta bazan yi kaffara ba Wlh anan zata zauna sai sanda naje na dawo..!
Sai dukkansu suka kasa mgana Anty Amarya ta mike tana Fadin"Shikenan gwara kayi mata haka ko zatayi hankali..Ni bari na tafi.Allah ya kyauta..!
Ya mike Tsaye yana fadin"Ameen Anty Idi ne ya kawo ku..?
Anty Amarya tace"A daidaita muka zo..Idi kila sun fita da mallam ne..!
Da Sauri yace"To bari nazo na kaiki gida..!
Da Sauri tace"A"a ka bar shi kawai Nagode..!
Daga haka ta kalli Sakina ta Harareta Kafin ta fice Umar ya fita ya Rakata har waje ta samu adaidaita ya biya mata Drop suka wuce.
Daganan bai koma gidan ba takawa yayi da Kafafunsa zuwa masallacin Dake gaban gidansa Uku da wani abu Lokacin La"asar ta kusa cikin masallacin ya shiga ya zauna yana Faman Tunanin ta ina zai fara zama da yarinyar nan gabadaya Bata dace da Rayuwarsa ba ga Sakina ita kuma kamar wata karamar yarinya ta fara rashin jin mganarsa Lallabatan Dayake yi yasa ta fara Tunanin ya sakar mata ne tarika abunda taga dama..!

*****

8:30pm
Chapter 90 · 0% Book details