← Book details Ta Fita Zakka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 170 OF 193

Sashe 170

Ta Fita Zakka Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

"kada ki kara tabani malama..!

sakina ta katseta cikin karaji da sai da anty amarya ta fadi kasa jidda da sadiya suka karisa suka riketa jidda ta kalli sakina cikin bacin rai tana fadin"sakina lafiyan ki kuwa..?
kada zafin kishi ya saka ki rasa natsuwarki mana..!
sakina ta dago jajayen idanuwanta ta balla mata harara kafin tayi mgana anty amarya tayi saurin kwace jikinta cikin nasu jidda tana fadin"yau za"ayi walkiya kowa zai bayyana..na rantse da allah ni madina bazan karbi faduwa ni kadai ba..sai dai mu yi faduwar guzuma..!
tafada lokaci daya tana neman balaraba dake falon sai kawai ta tsince ta sum sum zata fice tun da taga abunda ke faruwa tsakanin madina da sakina ta fara kokarin barin falon cikin rawan jiki anty amarya na hangenta ta daka tsalle ta rikota tana fadin"ina zaki kuma..?
munafuka..ai sai ki tsaya kiga yadda wasan zai kare ko dayyaba..?
tafada cikin tsaananin tashin hankali datake ciki da jajayen idanuwanta.
mamanmu ta fara kokarin kwace kanta cikin borin kunya tana fadin"wata dayyaban kuma..?
marliya kada zafin kishin ganin amina da ciki yasa ki fara hauka mana..
ko kafin ta rufe baki anty amarya ta tsinketa da mari mai lafiya sai da kowa afalon ya zaro ido cikin mamaki mamanmu sai da ta duke anty amarya ta bita ta chakumo wuyan riganta cikin karaji take fadin"zaki ga hauka yanzu nan don kutumar ubanki dayyaba..!
lokaci daya ta jawo ta tsakiyar falon kamar kayan wanki ya zulfa ta tare anty amarya tana fadin"meyasa kika mareta kuma kike janta haka..?
anty amarya ta balla mata harara da jajayen idanuwanta tana fadin"matsa ki bani wuri..ai ke mamanmu kika sani balaraba baki san wacece dayyaba..ba yau zaku san aihinin wacece fuskar wannan azzaluman matar..!
sai kowa ya saki baki amina na zaune tayi dariya jin dadi sai hawaye afili ta furta"komai yazo karshe..!
hamida ta kalleta cikin wani yanayi tana fadin"me..ya ke faruwa..?
sai amina ta kasa ce mata komai tsausayi suke bata yau zasu yi kwanan bakinciki in suka gano wacece ainihin mamansu.
anty amarya ta yarfar da mamanmu nan tsakiyar falon hajiya goggo husai ta mike tana fadin"ke marliya meye haka kuke yi kamar wasu yara..?
anty amarya ta cire dankwalinta taci damara tana zaran ido ta nuna mamanmu dake kifta ido ta rasa mafita tace"wannan zaku tambaya abunda ya faru..domin tasan komai..nima shi nake tambayanta yanzu..dayyaba ni zaki munafunta..?
ni zaki yaudara ki ha"inceni..?
wlh na yi rantsuwan
ko kaffara bazan yi ba kinsan inda amina take da halin datake ciki gani kikayi burinki ya cika kin kashe yaya..sannan kin samu sa"idu yadda kike fata shine yasa kika juyamin baya..?
to wlh kin yi kuskure ni madina fitilar sharri ce ko ba kalanzir sai na kai safe yadda ta bare dani da uban kowa sai ta bare yau..!
tafada cikin karaji da ihu kamar wata mahaukaciya daidai lokacin da su mallam sukayi sallama suka shigo falon bayan sa kaf zaratan ya"yansa ne kama daga ya danmallam nazir ,nasir,nazeem,jafar uzairu,shamsu akilu da zubairu, da aba aliyu abokin ya danmallam atare suka bayyana acikin falon sai kuma waje ya dau shuru kallo ya koma wajensu mallam.
hajiya na ganinsu ta murmusa kafin tace"yauwa ku kariso..yau abun dake boye ne zai fito fili..anyi walkiya za"a ga kowa sannan an dade ana ruwa kasa na shanyewa...!
kai tsaye ta maida kallonta kan anty amarya da ko ganin su mallam bata damu ba burinta kawai gayyar ta watse cikin wata murya tace"marliya naj kin fadi wata mgana da sunan hadiza..?
me kike so ki fada ne..?
anty amarya ta kalli mamanmu wacce ta ke kallonta cikin zaro ido jikinta na rawa ta tuma gaban madina ta rike kafarta tana fadin"madina don girma allah ki rufamin asiri..wlh na rantse da wanda raina ke hannunsa bansan komai kan cikin amina ba..!
anty amarya ta saka kafa ta ture mamanmu ta fadi gefe cikin taruwan hawaye tace"wlh baki isa ba balaraba..ai ke kwalba ce uwar sharri..qur"ani kadai zaki fadamin na yarda dake..!
yadda kasuwar ta bare dani ban ci riba ba kema yau sai ta bare dake dayyaba..!
tafada lokaci daya ta maida kallonta kan su hajiya tana fadin"hajiya..mallam sa"idu ina ya"yan yaya su jadwa..?
tafada tana binsu da kallo cikin son suji me take son fada suka tsura mata ido ta juya tana kallon mamanmu dake kuka tana rokonta kada ta fada ta juya mata baya ta kalli idon aba tace"kunga wannan matar ba matar kwarai bace..shekarun data kwashe tana zaune daku duk na cutarwarce..muguwa ce azzaluma ni duk mugunta na ban taba kisa ba..ammh kunga wannan..?
to tayi kisan kai ta kashe rai har lahira..!

aba cikin rawan baki dana murya yace"wa...ta kashe..?
kafin ta samu bakin mgana daga bayansu sukaji wata murya cikin kuna tace

"yaya ta kashe aba..!

sai kallo ya koma inda akaji mganar sai ga amina ta bayyana a tsakiyar falin gaban anty amarya da mamanmu da ke tsuggune cikin fitar hawaye duka biyu.
gabadaya sai kowa yaji wani sanyin jiki aba sai da ya dafa ya danmallam dake gefensa saboda jirin daya kwashesa anty amarya kuma amina take kallo da mamakin a ina tasan wannan mganar..?
mamanmu kuma kasa kawai tayi dakai yauma tubular sara"i babu tsima babu dubara.
ya jalela da su ya jadwa suman tsaye sukayi ya jafar ne ya iya takowa ya iso gaban amina ganinta da ciki ba shi ne agabansa ba mganar data fada ne abun damuwa..
cikin fitan hayyaci ya kama jijjiga kafadun amina yana fadin"wata yayar ne ta kashe..?
ummanmu..?
ya fada cikin tsawa idanuwansa jajir kawai sai amina ta fashe da kuka ta fada jikin ya jafar tana nuna mamanmu cikin wata murya tana fadin"itace ta kashe mana uwa ya jafar..itace ta rabamu da aba..itace ta rabani da uwata shekaru goma da wani abu bansan dadinta ba..
itace ta maka asiri domin ka lalace sai abun ya dawo kaina.
itace ta hada kai da anty amarya ana zaluntar ya danmallam itace kuma suka ka hada kai domin su ga bayan aurena da ya danmallan da alwashin har abada bazan taba haihuwa ba..
ya jafar wlh wannan matar muguwace kuma azzaluma ce ta dade tana zaluntarmu bamu sani ba..itace ta kashe mana yaya da kunnena naji ta tana fada..!
ta karishe fada numfashinta na sarkewa,ya jafar ya riketa cikin wani yanayi yanayin da baya fatan ya bude ido yaga abunda ke faruwa da gaske ne.
durkushewa amina tayi kasa jafar ya bita ya tallafeta,ya danmallam ya kariso ya riketa yana cire mata hijabi saboda ta samu iska tana ganinsa ta damke hannunta cikin rawan murya tana fadin"itace..ita ta kashe mana yaya..!
malam dake tsaye yace"innalillahi wa"inna ilaihirraju"un..!
sai kowa afalon ya dauka saboda kowa ya rasa abun fadi.
mamanmu na wani irin gunjin kuka tace"kaico na..bansan akwai wannan ranar ba..da ban aikata abunda na aikata ba..don allah ku yafemin..!
gabadaya kallonta kawai ake yi cikin wani yanayi aba kuma zaman dirshan yayi a kasan cafet ya kasa mgana su ya jadwa kuma suna dai tsaye da karfin imani.
hajiya ce ta kalli mamanmu tana fadin"balaraba me hadiza ta miki kika kasheta kika raba ta da wannan duniyar..?
tafada cikin wani yanayin muryanta kamar zatayi kuka ranar da
danmallan yazo mata da wannan mganar bata gasgasta ba har yau tana cikin tantaman balaraba zata iya kasje yaya sai yanzu da komai yake neman bayyana.
mamanmu tana kuka kanta na kasa ta kasa dago kanta saboda kunya balle ta kalli ya"yanta da yayan yaya ga aba ga kunya mutanen dake falon anty amarya kuma na tsaye ta shirya komai ayau sakina ma duk suna gefe banda kuka babu abunda take yi.
amina kuma danmallam jikinsa ya tarairayota ya azata yana ta faman mata fifita da hijabinta sakina na kallonsu tana jin kamar ta mutu saboda bakinciki.
kan mamanmu na kasa ta fara mgana.

"soyayyar sa"idu ce sila..."

*ja*TFZB2026*

*Ki biya ki karanta cikin Salama kiyi ma girman Allah in baki biya ba kada ki karanta sannan kuma kada ki yada'ashi..Pay N500 via Jamila Umar gtb 0552179550 ko katin waya ta wannan lambar 09069067488*

Gabadaya Ilahirin Falon sai da kallo ya koma kan mamanmu cikin mamakin kalamanta,ita kuma kanta ta kara saddawa kasa hawayenta na diga saman cafet din Daya malale falon Hajiya ta cigaba da fadin'"Tabbas kamar yadda na fada da farko Hakane soyayyar Sa"idu ce ta kaini ga komar Nadama dana ke ciki..!
Chapter 170 · 0% Book details