← Book details Ta Fita Zakka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 193

Sashe 16

Ta Fita Zakka Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Sai da ta gama yanke Farcen nata ta kankare Lokacin Mamanmu ta gama gyaran Zogalen ta shiga kitchen ta Jikata da Ruwa,ta fito kenan Yaya ta kalleta Tana Fadin"Ni ko Mamansu kinsan Dan Malam ko zai dawo Cikin Satin nan..?
Mamanmu ta Tsaya rike da Kugu kafin Tace"Eh naji su Babansa na mganar sannan naji bakin Hajiya dana Shiga wajenta Ranar..,!
Yaya na Fadada Mirmishinta Tace"Yau da asuba ya Kirani mun gaisa ya Fadamin gobe jirgin Asuba zasu taso...Daga Jidda zuwa gata suna gida..!
Mamanmu ta washe baki Tana Fadin"Masha Allah Allah ya kawo su Lafiya naji jiya Babansu na Fadin kayan su har ya iso tun jiya Shi Kadai zai zo ko Harda ita Sakinar..?
Yaya tace"Yace min Har da ita Sakina sannan yace min zai zo da Bakuwa ma..!
Mamanmu ta tsaya rike da Haba tana Fadin"Bakuwa kuma yaya..!
Yaya bata samu Zarafin mgana ba Hanne tayi sallamo Lokaci Daya tana Bayyana atsakar gidan.
Mamanmu da Yaya suka juya kanta Cikin Kulawa sai da ta karisa kan Darduman Yaya ta zauna tana Fadin"Mamanmu yaya sannanku da gida..!
Mamanmu tace"Maraba da Hannatu..Hannatun Aminata..!
Take Fada tana Dariya Hanne ma Dariyan take kanta na kasa ta shiga gaishesu suka amsa mata Yaya ta kalleta Cikin Dogon Hijabinta tana Fadin"Hannatu ya wajen su Hajiya..!
Hanne tace"Kowa lafiya..Tace a gaishemku..!
Suka amsa mata kafin ta mike tana Fadin"Mamanmu su Amina fa..?Daman Hajiya ne tace nazo na Kirasu zamu je chan gidan Ya Dan mallam ne mu yi musu yan gyare gyare kafin su iso..!
Mamanmu tace"Amina na cikin Dakina..Hamida na Dakinsu tama gyara kaya..Amina..Hamida..! Baku ji Zuwan Hanne bane..?
Ta fada tadan Daga Murya Hamida ce ta Fara fitowa tana Fadin"Naji zuwanta Mamanmu ina so na karisane Dirowar Amina kamar Dirowar mara rai mamanmi kaya duk sun Yamutse Wlh Amina kin bani da kazanta..!
Hanne tace"Amina jidalinta bazai barta ma tayi abu mai kyau ba Kina ina ne..?
Amina na jinsu sai da taga Dama ta Fito tana Wani Kallonsu Daya bayan Daya Kafin tace"ina jinku...kawai bana son mgana ne..Ya akayi ne..?
Tafada tana Dafa bangon Dakin Mamanmu.
Hanne tace"ai kinji..Hajiya tace nazo na gayamuku ku shirya muje gidan Ya Dan Malan mu yi musu yan gyare gyare kafin su iso..!
Da Sauri Hamida tace"Kai don Allah..?Bari na gama Yanzu na shirya mu tafi Daman nayi wanka..Amina ce batayi ba..!
Amina ta juya Idanuwanta kafin Tace"Ai ba zuwa ma Zan yi ba..Bar Fadin ma ban yi wanka ba..!
Ba su kadai ba Hatta Yaya sai da ta Dago Tana kallonta Mamanmu bata a wajen tana Kitchen bata jisu ba.
Hanne Tace"Saboda mene...?Hajiya ce fa tace nazo na gaya muku..!
Amina ta mele baki tace"Daman bansan Kakam banki ba Hajiyar datace Dole sai munje..Ke ni fa nagaji ba wani aikin da zan yi ina kannen Matarsa..?su je mana..!
Hanne tace"Wai su Sa"adatu..?to tare zamu tafi da ita fa..!
Amina tace"Ai kaji..Shiyasa ma bazani ba kinsam na Tsani Hada waje da yarinyar nan.balle tana ganin gidan Yayarsu akaje sai ta nemi Budan Hanci ni kuma kinsan Halin Jidalina Kamar Zawo nake bani da Hakuri..!
Hanne tace"ba abunda zai faru..ai ta Daima Shiga shirginki Tunda Sanda Baba mallam ya mata mata mgana..!
Hamida ta Kada kai kafin tace"Kyaleta Hanne in bazataje ba ni zani..Daman in jin Labarin Haduwar gidan nan banta zuwa ba..!
Hanne tace"Nima ban taba zuwa ba..Kinsan Wanshan Dawowar nasu su ya Abida aka tura shima Dakyar..Yau din ma Baba Sa"idu Hajiya tasa ya Kira Baba Malam ya tambayeshi Da yace baxamu je ba sai dai su Ya Shamsu suje su gyara!
Kunsan Baba Mallam baya son muna Fita ko fa gidansu ya Jafar sau daya mika taba zuwa Inajin Hamida..!
Hamida tace"Wlh kuwa shima Lokacin da Anty Shamsiya ke wannan Laulayin ne muka bi su Hajiya Dakyar Shima Daga Cikin gida sai mota Daga Fitowa sai Mota ko dan gari bamu gani ba..!
Sai Lokacin Yaya ta saka baki Ta mike tana Nannade Dardumanta tana Fadi "Sai abarku kuna mata kuma Yawo agari..?ai ina godema Baba Mallam Har gobe ina jinjina ma Hikimarsa..!
Hamida kiyi ki shirya ku tafi..Ku kyar wacce tace bazata je ba..Rashin zuwanta bazai saka afasa komai ba..!
Tafada Ko kallon Barayin Aminan batayi ba Amina da tasan da ita akeyi ta Tura baki kafin tace"Ai ban je ba zani ba..Yasin sai naje nima naga abunda za"ayi Ehe..!
Tafada lokaci Daya tana Juya ido Yaya dai bata ko bi ta kanta ba ta Shige Dakinta Idanuwanta sun kawo kwallah ai akwai wanda Hallayar Amina ke sukan zuciyarta Bayan itace ko Sa"idu bai kaita jin wannan Dacin ba itafa uwace wacce tasan Ciwon abunda ta Haifa Sannan Ita ta kadai tasan aibun mgana da Kullum ake yi akan Amina nasan ita Kadai tasan Ciwon Haifar Zakka cikin Tarin ya"yanka sai dai tana amfani da Nasihar Baba Malam da kullum yake Fada mata Ta rika ma Amina Addu"an Shiriya kada ta sake ta bari ranta ya baci akanta Ballatana watarana ta aibatata Duka basa gyara Tarbiya Sai ma kara Fandarewa Addu"a da Nasiha sune Jagora.
Hawayenta ta Share kafin ta Daga Hannu Sama tana Fadin"Allah ga baiwarka nan Amina kai ka Halliceta kuma Kaddaranka ne kayi ta yadda take..ya Allah ka shiryanta da ita..Ka Natsar da ita..ya Allah kada ta zame mana Zakka watarana..Allah ka Bata wani bawanka da zai shigo Rayuwarta da Alheri ya SauyataWatarana..!
Tafada Lokaci daya tana kallon Sama alokacin Bata sani ba Kaddaran Amina Rubutattane sannan addu"arta an dade da amsata bata sani ba.
Chapter 16 · 0% Book details