← Book details Ta Fita Zakka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 191 OF 193

Sashe 191

Ta Fita Zakka Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

agefenta ita taimaka mata ta saka mata Belt sannan ta rike mata Aba Dake hannunta.. Amina jikinta sai rawa take yi yau gata ajirgi duk bata cikin natsuwarta addu"a kan har ta shiga bayi sai da tayi matar dake gefenta nata mata Dariya saboda ganin yadda take yi sai da Tambayeta ammh bata taba shiga Jirgi ba tace eh tayi Dariya tace kodaga gani to maatar ne ma yasa ta Saki jikinta ba kamar Farko ba suna ta Fira nan tasan sunan matar Surayyah a Nageria take itama aiki yakai mijinta madina suka koma yanzu ma tazo ganin gida ne su yan Abuja ne suna ta Hira da Amina duk da ta Girmeta itama ta Fadamata wajen Mijinta zataje sai santin su Aba take tana jin Dadin ta samu yar"uwa a Nageria..! Sai Dare suka sauka a jidda Danmallam Daman tun tasowarta ya Sani yana Jidda shi da Sarood da Sakina suna jiran Saukan Amina Saboda ya gayamusu sai ko ga Amina ita da Surayyah wacce ke rike da Aba ita kuma mallam na Hannunta .! Sakina baki ta saki tana kallon yadda Amina ta koma Cikin Abaya baka tayi Rolling jan gyale Takalmin kafarta ja ne da Jakarta ga yaranta sai dai kace Masha Allah Danmallam ya nufeta Ya karbi Jakarta lokaci da mallam yana mata maraba har da Rumgomta sannan suka gaisa da Surayyah Amina ta Fadamai irin taimakonta da tayi a jirgi ya mata godiya itama Mijinta yazo Daukanta har suka gaisa da Ya Danmallam sai ma suka ga sun san juna suna Haduwa wajen karatu a masallacin cikin madina suka gaisa cikin girmamawa basu rabu ba sai da Surayya ta karbi Lambar wayar Amina da alkwarin zata zo har gida sannan ta shiga mota suka wuce ita mijinta, Amima kuma ta saki Fuska suka gaisa da su Sarood har da rumguma Sakina kuwa Amina sama sama ta amsa mata ko Hannun Datake bata,ta kauda kanta bata karbi Musabahanta ba,Motar Haya suka shiga zuwa Madina Danmallam na rike da Aba Sarood ta kankame Mallam itama cikinta har yayi girma Sakina na gefe kamar maraniya mamaki ya kamata jin yadda Amina da Sarood ke Hira Cikin Larbaci..! Gidan su Sakina suka fara zuwa Sai da Amina tayi sallah taci abinci sannan suka Dumguma zuwa gidanta ta iske komai an gyara har kayanta da suka Rigata isowa Data tambayi Danmallam yace mata Sakina ce Sarood suka zo suka gyara bata kara mgana ba nan suka barsu ya rakasu suka Hau mota suka koma gidansu Yau dai ga Amina amadina Duk Gajiyan da ta kwaso na Tafiya Sai Da Danmallan ya Famshe sai washegari ya barta ta Fara barcin gajiya sannan shi ya Kira chan Nageria ya Fada musu saukanta .! Saboda ita bai riga ya siya mata Layin nan ba,Amina kamar bugagiya wajen Sati tana Hutawa sannan ta Fara Fita ita da Danmallam gidansu Abu Kattab suka fara zuwa ta wuni mami Sara nada Kirki sannan Amina taga inda Sarood ta Dauko rashin Hayaniya har suka bar gidan Su Aba na hannunta tana wahala dasu Daga Ranar Amina bata zauna ba suna Fita Cikin gari yana nuna mata wurare Amina tayi kuka data ganta a msallacin ma"aiki Bata taba Zaton haka ba,Sannan sun raba kwana yana kwana Biyu gidansu Sakina ita yana mata kwana Daya Sai dai tana Wahalan Renk ita kadai ta Saba yakaka ta Saba mata duk sai ta Sangarce. Ammh yanzu Reno kadai ya isheta sai in yana nan yake tayata Reno Sai Daga baya ne ya siya mata layin chan ta saka suna mgana da yan'uwanta Amina daman kusanta da son yawo ballatana an samu garin Madina tuni tasan ko"ina Ballatana ma da Surraya ta Kirata tazo gidanta ta wuni itama Ranar Danmallam ya kaita ta wuni Amina ta sami Sake tunda Danmallam bai mata shamaki da Fita ba Saboda wani Lokacin baya kusa ko yana cikin makaranta waya kawai Amina take mai tace zataje masallaci Kusan koda yaushe nan take sallar mangariba da Isha"i kafin kace me Fatar ta Goge ta zama kamar bakar Balarabiya atamfa sai tana Gida in zata fita kuma Jallabiya ce Ita da kyawawan yaranta gwanin ban sha"aawa..! Watan Amina Daya da zuwa Madina Sarood ta Haifi Yar mace kyakyawa a gida ta Haihu sai daga baya sukaje asibiti aka Dubata Yarinya kamar tace sak kamar yar larabawa,Amina tana zuwa kullum saboda suna dan dasawa da Sarood Tsakaninta da Sakina kuma sama sama ne ko" ya"yanta sai a bayan idonta take Dauka In Amina na wajen bata bari Har Danmallam yaso yayi mgana Sanin Jidalin Amina yasa bai mata mgana ba..!
Chapter 191 · 0% Book details