← Book details Ta Fita Zakka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 177 OF 193

Sashe 177

Ta Fita Zakka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai da Hajiya ta saka baki sannan su Ya Aisha suka Tafi da su Amina gidan su ya Jafar saboda su Shirya Sa"adatu kuma Mallan ya kira Jidda yace Sa"adatu ta Dawo gida ko batasan yau za"a Daura mata aure bane..?
Ba Dadewa suka Dawo ita da Sadiya fuska duk ta Kode saboda kuka gidan su ya Jafar suka wuce tunda chan zasu shirya kafin Daurin auran.
Anan ne su ya Aisha ke jin Labarin Sakina cikinta ya zube sannan tana chan ana mata karin jini bata san inda kanta yake ba.
Sadiya ke maida musu zencen tana kuka su ya Abida na Faman bata baki Amina kuma na tare da su Hanne ita yanzu tama Daina kukan Hamida ce sai Ahankali ita da Hanne suna ta faman bata Baki ammh Taki sakin jikinta gashi ana Daura aure za'a tafi Dasu mallam yace bamai Daga wannan auran.
Baba Mallam da Aba tun safe suka fita ba wanda yasan inda suka je sun dai yi mgana da Hajiya kafin su fita Sannan har yan bazanga da bakin gusai suka iso maza basu dawo ba sai wajen 12,da rabi na rana suka Dawo Shima Baki akayi daga maiduguri wani kawun su Hajiya sai D'ansa guda Daya wanda ko Hajiya bata san da zuwansu ba.
Ashe Labarin abunda mamanmu ta aika yaje kunnen su kawu Salisu matan sun kirasu sun Fada musu komai,Kawu Salisu sai Fada yake yi yanaCema Aba ya saki Balaraba taje duniyace Mallam ne ma ke basa bakin kan mganar Aba dai bai ce koma ba ai ko bai ce balaraba ta bar mai gida ba in Tana da kunya basai ma ta jira yace ba zata san inda Dare yayi mata.
Zuwa Lokacin Yan Daurin aure sun fara Zuwa Mutanen Yola ne suka fara zuwa da Mata guda biyu suka zo aka kai su Shashen Hajiya sai yan Zaria suma sun Iso da mace Daya.
Na gombe ne karshen isowa su kan maza ne kadai suka iso banda mace ko Daya.
Amaran nachan gidan ya Jafar an samu sun yi wanka sun saka wani Less din da Mallam ya Dinka musu mai Fari da Golden sai Hijabansu mai ruwan kasa Itama Amina ta shirya Cikin leshinta mai Tsada da ya Aisha ta Dinka mata iri daya da ita har da Yakaka sai dai ita Bubu tayi saboda Cikin jikinta kowa ka gani ba walwala ido Duk ya kumbura.
Su ya Zulaihat sun zo da Safe suka Hade dasu Hamida da Amina suna ta kuka dasu ya Jadwa suna ta basu Hakuri su kuma suna cema musu ba Laifinsu bane sai da ya Aisha tace zata Kira Hajiya sannan suka sarara.
Misalin karfe Daya da wani abu na Rana Kofar gidan mallam ya Cika ba matsaka Tsinke su ya Danmallam sai Lokacin suka iso Cikin shigarsu ta alfarma haka ma su Ya Jafar mallam ma da Sabuwar shadda da rawani haka ma Aba kowa dai yayi kokarin Boye abunda ke ransa har da su Nazeem kuwa.
Alokacin kuma Hajiya Uwani ta san da abunda ya faru da yar"uwarta Batula sai ta rude kuka kamar zata Haukace bata tsaya neman kowa ba ta Hada kayanta Ko Umaima bata Tsaya bi ta kanta ba,ta ma bar Shashen nata tana Shashen Hajiya ta shiga Cikin yan Biki ita kadai ce batasan me ya faru ba mutane sun yi yawa yasa har ta fito ta tari abun hawa ta hau zuwa Tasha ba wanda ya lura da ita ammh Nazeem ya ganta sai dai bai nuna ya ganta ba yana Tunanin abunda ya Dace da ita kenan ya Dauka ta neman ma kanta mafita ne kafin mallam ya koreta.
Anty Amarya kuma tana Shashenta ko kare bata kara gani ba,kaf Danginta suna asibiti wajen sakina su jidda kuma suna Tare da Sa"adatu domin cire mata Damuwar dake damunta duk da suma karfin Hali ne Mamanmu kuwa Sai da ta raina kanta Har Daki yan Gusai suka Bita suka mata tsofin Allah Tsine shiyasa ta kasa Fitowa Tayi kuka har ta bama uku Lada yan"uwanta sun Tsine mata kamar me sun ce ana Gama Biki yau gobe zasu koma sannan sun ga karfin Halinta Data iya Takowa gidan Sa"idu..
Ita kuma tana Tunanin ina Zata..?
Bata da inda zataje a karbeta Ta riga tayi ma rayuwarta mummunan Tabon da har Abada bazai goge ba.
Karfe Biyu aka Dauran auran su Hanne,Na Aba aka fara Daurawa da Hadiza Babbar Diyar kanwar Hajiya Yagana Datayi aure mijinta ya rasu bata kuma taba Haihuwa ba..!
Hadizan ma da ita aka zo Biki Suma kansu basu sani ba sai da aka Daura shi ya kawo kawun Hajiya Tun Daran Jiya mallam ya kirasa yamai bayani Tun Safe kuma suka Biyo Jirgi Daman a Bauchi yake da zama shi da iyalansa. !
Daurin auran daya bama kowa mamaki Hajiya kam Bakinta yaki rufuwa Mallam a koda yaushe Tunaninsa mai kyau ne

Daga nasa sai na Hamida sai na Sa"adatu na hanne ne na karshe Bayan an Daura auran aka shiga taya juna Murna ya jafar yayi mamaki Lokacin Daya ga wanda Hanne ta aura har ya bashi Hannu sukayi musabaha bai daina mamaki ba.
Har sai da shi yace mai""Ya jafar Allah ya Rubuta Amina ba matata bace..Hannatu ce matata..,!
Ya jafar ya jinjina kai aransa yana kara yima Allah kirari.
Su Danmallam suna cikin jama"a suna ta Faman gaisawa da mutane Bakinsa har Kunne shi da Aliyu,da Nazir nan kasan ransa Halin da Amina take Ciki yake so ya sani Sakina kuma bata gabansa bai san Halin Datake Ciki ba Sannan basu kirasa ba shima bai nemi kowa ba.
Suna cikin gaisawa da Mutanan ne ya Hango Amina suna tafe ita da Zafira Amina ta saka Hijabi mai Ruwan Sararin Samaniya kalan leshinta da Takalminta mai Saukakan Tudu tana Tafiya cikinta yana gaba da ita Saboda Girmansa har suka shige gidan mallam
Ayadda Danmallam yaga Fuskarta ta Kumbura ne yasa Hankalinsa ya tashi yaja Hannun Aliyu suka bi bayansu Baya son yaga Amina na cikin Damuwa,suna shiga kuma haraban gidan yan bazanga suka taresa ana ta gaisawa yasa basu samu karisa cikin gidan da wuri ba.
Amina kuma daman Ya Aisha ne tace Hajiya na kiranta, taso ta jira su taho dasu Hanne suna Sauya kaya yasa tace Zafira ta rakota su suna chan ko Mganar auran Aba din ma basu sani ba sai bayan tahowarta sannan Anty Fadila take fadamusu itama Mijinta ne ya kirata ya Fadamata.
Amina har ta shiga Shashen Hajiya ta zama abar kallo da Sha"awa suna shiga Falon cike da jama"a.
Da Hajiya suka ci karo da ta fito Daga Dakinta Taci gayunta itama bakinta Har kunne Amina suna gaisawa da yan Falon yawancin yan"uwan Hajiya ne taga dai ana nuna tw ita bata san me ya faru ba.
Yakaka ce Amina ta Hango zaune itama ta sha gayunta ta karisa suka gaisa Yakaka na fadin"wasu baki ne suka zo suna son ganinki..Hajiya ta saka aka kiraki..!
Hajiya ta kariso wajensu zatayi mgana kenan sai ga wata Farar mata gajera ta fito Daga Dakin Hajiya bayan ta wata mata ce itama suna yanayi sai da tana dan tsawo ita.
Hajiya na ganinsu ta juya tana Fadin"Yauwa Nenne ga ma Aminar nan ta kariso..!
Ta fada tana riko Hannun Amina har gaban matar da Amina ta kasa Dauke Ido a kanta.
Wacce aka kira da Nenne ta Rike Hannun Amina cikin Fara"arta take Fadin"Allahu akbar Rahina..Kinga Aminar Aminullahi..Allah ya rubuta Ba matar sa bace..Rabo ne rabo ne ya Haddasa abubuwan da sukayi ta Faruwa..!
Wacce aka kira da Rahina tabi Amina da kallo Kafin tace"Ba Shakka yau naga Amina..Aminar da kaf Danginmu ba wanda bai santa ba..Sannu Amina Allah ya raba Lafiya..!
Tafada tana kallonta sai Amina ta kasa mgana ta koma tana Binsu da kallo Hajiya tace"Bafa ta gane ku ba inaga sai kun mata bayani..!
Tafada tana Dariya.
Nenne ta kara rike Hannun Amina Tana Fadin"Amina baki gane ni ba ko..?
Ai nasan baki sanni a Fuska ba sai Muryata..Nice fa NENNE..Nennen Aminu fa..!
Sai alokacin Amina ta Gane ina ta san muryan Ido ta waro kafin tace"Nenne..!
Nenne na Dariya tace"Alkwarin Allah ya Cika Amina..Aminu da bai Sameki ba..Sai Allah ya kaddara yar"uwarki Hannatu ce RABONSA..!
sai amina ta kara zaro ido Cikin mamaki bata samun Damar mgana ba Ya Danmallam da ya Aliyu suka shigo Falon bayan su kuma ya Nazir ne yana Cema yan Falon Tawagan Angon Hannatu zasu shigo su gaida su.
Sai Amina ta juya suka Hada ido da ya Danmallam ya sakar mata ido ita bashi ma take kallo ba Wanda ya shigo ne cikin Farar shadda da babbar Riga shi da wasu maza su uku.
Su ya Danmallam suka basu waje su ka kariso tsakiyar Falon suka Duka suna gaida wadanda ke falon.
Kan Aminu na kasa ne Yaji Nenne na Fadin"Aminu yau dai naga AMINA..yau naga Amina..!
Take fada Hakoranta duka suna Waje..Atare Aminu da Danmallam suka Dago kansu.
Shi Danmallam Wanda aka kira da Aminu yake kallo shi kuma Aminu Nenne ya kallo sai kuma karaf suka Hada ido Hudu da Amina..
Mennarsa da rashinta yasa kadan ya Rage bai Haukaace ba itace agabansa ta Sauya har da Tsohon Ciki ma ajikinta..!

*Janafty*
[11/3, 2:16 PM] Sweet sis: *TFZB2028*

*Ki biya ki karanta cikin Salama kiyi ma girman Allah in baki biya ba kada ki karanta sannan kuma kada ki yada'ashi..Pay N500 via Jamila Umar gtb 0552179550 ko katin waya ta wannan lambar 09069067488*
Chapter 177 · 0% Book details