← Book details Ta Fita Zakka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 103 OF 193

Sashe 103

Ta Fita Zakka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A wardrope din ta saka kayan kamar yadda yace,ba komai acikinsa sai Rigar barci Daya da Jallabiya guda Biyu Saman Madubi kuma sai Tararuka Amina ta matsar da su gefe ta saka kayanta aranta tana fadin ita yar Saudi bata ijiye kayanta anan ba kenan..?
Har da littafan makarantar ta da takalmi da jakar Cikin wardrope ta Nausa su ta hada da ghanas din duka ta Tura kada dai yazo ya gani kafin ta gama bayanta ya kage ta koma ta zauna bakin gado tana Tuna Hamida afili ta Furta"Allah sarki Hamida kin sha Fadamin watarana baki tare dani zan tuna dake..Sai gashi Kaddaran data Rabani dake ko kwana Daya ban yi Cikinta ba na Tunaki hamida..!
Sai hawaye ta tabbata da Hamida na nan tare da ita duka wannan aikin ita zatayi Kan gadon ta koma ta Dunkule tana kukanta na fama sai da taji sanyi ya isheta ne sannan ta tuna batayi sallar mangriba da isha"i ba..dole ta mike ta koma Tiolet din ta Dauro alwala tazo ta Daidai ci gabas tayi sallarta tana idarwa ta kwanta nan Saman Cafet din tana Tunanin rayuwarta a wannan gidan,Sai kuma ta fara kuka kewar yaya ta isheta Sai kuma ta ji mutuwarta ta dawo mata Sabuwa sai kuma ta tuna da mamanmu da su Hamida sai kuka wiwi har barci ya kwasheta tana kuka bata sani ba.
Da safe tana tashi da filet da kofunan taci karo tana idar da sallar asuba ta makara sai da gari ya waye ta tashi ta Dauke duka harda goron ruwa ta fara Tunanin in da zata kai domin in wannan dan bala"in yazo ya gani kashinta ai bushe.
Yanke shawaran fita tayi ta kai kitchen daman ya sa mata sabon suna wai kazama ai in yaga wannan sai ya kara kiranta da Hujja..
Koda ta fito shuru falon ba kowa sai da ta leka ta tabbatar da ba kowa sannan ta fara Tafiya Sadaf Sadaf zuwa Kitchen ai tasan hanyar tunda sun taba zuwa.
Tana shiga kitchen din nan ma ba kowa sai dai tas kitchen din ba Datti kamar ba"a girki a wajen saman Cabinet din kitchen ta ijiye kayan hannunta ta juyo kenan zata fito suka kusa cin karo da Sakina data ganta sai da gabanta ya fadi ta ja baya tana Zare ido.
Sakina Dake sanye da Riga da wando na plazo ta kalli Amina Daga sama har kasa cikin kaskasci kafin tace"Me ya kawo ki kitchen dina..?
Amina ta kalleta taso tace ne bata sani ba ammh kuma bata da wannan karfin gwiwan yanzu ta kanta take yi yasa batace mata komai ba ta raba ta gefenta zata fita ran sakina ya baci ta Finciki hijabinta ta Dawo da ita baya ta Shake mata wuyan Hijabi tana Fadin"Ke don ubanki ni nake miki mgana kina sha min kamshi..?
Tafada tana Zare mata ido Amina ta kalleta ammh ta kasa mgana aranta Tana Tunanin Sakina tazo Lokacin da Bazata iya maida mata martani ba..Ammh ta bari wanchan mara imanin ya tafi wlh bata zagi Aba a banza ba sai ta rama mai.
Ido ta dago karaf suka hada ido da Danmallam dake tsaye daga falo yana kallonsu yana sanye da Jallabiya baka da Hula Cashaba ce a hannunsa kamar Dawowarsa kenan daga masallaci.
Amina tana ganinsa sai da gabanta ya fadi da sauri tace"Kiyi hakuri abu na kawo..!
Sakina zatayi mgana kenan taji Muryansa daga bayanta yana Fadin"Saketa Sakina..!
Sai Lokacin ta juyo tana kallonsa sannan ta saketa ammh sai da ta Murje mata kafa da takalmin Dake kafarta Amina taji azaba ammh bata nuna ba Da sauri  ta fice Daga kitchen din kamar ta kifa ko barayinsa bata kallah ba ta koma Dakin datake tana shiga ta Dafe kirji tana Sauke Numfashi kamar wata mara galihu haka ta koma saman cafet ta zauna tayi Tagumi bata son hawa gadon ne bata saba da irin shi ba sannan ta saba kwana cikin mutane,akwai watarana ma da ita da Hamida suke kwana agado daya hamida tayi ta mitan ta matseta ammh Amina ta mata Burus wai ga inda Rayuwa ta kawota ita kadai kamar mara galihu.
Tunda ta shigo Dakin bata kara jin motsin su ba sai chan rana Sakina ta shigo Lokacin har barci ya fara Fizganta koda ta Bude ido sai taga ta Dungurar mata da Filet din abinci tayi Tsaki ta fice Daman yunwar Amina take ji domin tayi alkawarin daina zama da yunwa in ta mutu Danmallam da matarsa basu da asara.
Data gama da Filet din ta fita takai kitchen bata ga sakina ba yasa ta Tsaya ta Bude Fridge ta Dauki ruwa ta sha ta Koshi ta koma Daki da Daddare ma Sakinar ta kawomata Fuskar nan tata kamar Hadari saboda hadewa,Ta ballama Amina Harara Dake zaune taba kallonta sai da ta fita taji Dariya ya kamata aranta tace bani kadai yake ma Mugunta ba harda matar tasa tasan badomin shi ba Bata isa Sakina ma ta kalleta ba..
Kamar ta sani tun abunda tace mai jiya da Daddare ya dinga Daure mata shiyasa sai ta ganshi sai ta zuba abincin ta kaima Amina tana cika tana batsewa shi dai ko kara bi ta kan Sakina bai yi ballatana Amina,ita kuma Sakina Dadinta Daya ganin Aminar da ita da banza duk daya a wajen Umar sannan suna waya da Anty Amarya tana fadamata komai ita tace tarika bama Amina abinci ba komai suke da nasara..
Washegari tun safe Umar ya fita kan mganar Visa dinsa kano yaje tunda ta chan zasu tashi sai dare ya dawo an samu Visar nan da kwana Hudu zasu tashi,Farinciki ya ishesa sai kuma aranar yaje chan Gida bayan tafiyarsa da Amina sun hadu da Aba yayi ta mai fadan kada ya saurarama Amina in tayi mai wani abu yayi mganinta kada ya Ragamata shidai bai ce komai ba.
Taya ya zai biyema Aba ya taba Amina hajiya ko mallam su ji labari ai sai su Tsine mai ya samu dai ya lallaba ya kara gaba ba"a gansa ba ballatana ace wani abu.
Tare da mallam sukayi sallar isha"i Daganan ya shiga cikin gida ya gaida matan mahaifinsa,Shashen Hajiya ne na karshe,ya shiga tana zaune afalo tana gyaran farcenta ya zauna nesa da ita a kasa suka gaisa tana tambayansa Amina yace tana lafiya.
Shuru na wani Lokaci kafin ya muskuta yana fadin"Hajiya na samu Visa ina ga nan da kwana hudu zan tafi..!
Hajiya ta Dago tana kallonsa kafin tace"Allah ya kaimu..Allah kuma ya Tsare..!
Kansa na kasa ya amsa da Ameen kafin Hajiya tace"Yanzu ba da ita Sakinar zaka koma ba kenan..?
Kai Tsaye yace"Eh Hajiya..!
Hajiya tace"Ai shikenan ma da nazata da ita zaka koma nayi ma mallam mganar Hamida da hanne su koma chan su taya Amina zama har ku dawo..!
Yana jinta bai ce komai ba tacigaba da Fadib"Ammh tunda ta na nan shikenan..Sai dai kafin ka tafi zaka siya mata ko karamar waya ko Danmallam..?
Kansa na kasa kafin ya Dago yana Fadin"To Hajiya sai a siya mata..!
Hajiya tace"Ya kamata gaskiya tunda kaga itama Sakinar nada wayarta. sannan in ka tafi chan sai ku dinga mgana ta wayar da zaka siya mata hakan zai fi..!
Danmallam dai nasa cewa to ne Domin Gata kan Amina ta fisa gata a wajen su Hajiya.
Shuru ya kara giftawa na wani lokaci kafin tace"yaran nan ma yan"uwanta har yanzu basu saki da kewar Amina ba..Nace zasu je mata cikin Satinan tunda ma zaka tafi bari in ka tafi sai su tafi su mata ko kwana Biyu ne nasan zataji Dadi..!
Dan mallan kansa na kasa aransa yace"Zataji dadi tunda abokan iskancin nata suna kusa da ita..!
A fili kuma bai ce komai ba Hajiya ta shiga Fadamai zata je maidguri Cikin watanan yar yagana zatayi aure ya Dago yana fadin"Hajiya daman tana da wata ya agabanta ne..?Na dauka Suhailu ne kadai autanta..!
Hajiya tace"A"a tana da karamar ta zaituna itace zatayi aure..!
Bai wani damu ba yace"Allah ya kaimu hajiya..Allah ya bada zaman lafiya ke kuma Allah ya kaiki lafiya ya Dawo Dake..!
Ta amsa mai da Ameen kafin tayi mgana Hanne da Hamida sun shigo Falon suna ganin ya Danmallam suka natssu suna gaishesa ya amsa yana kallonsu ganin yadda sukayi wani iri Hajiya ta kalle su tana fadin"Nasha chan zaki yi kwanciyar ki hanne..!
Hanne batayi mgana ba kanta na kasa Hamida ce tace"ni ce zan kwana anan Hajiya..!
Hajiya tace"Shikenan yau dai kun ma Balaraba Yaji..Ita kadai sai jawadu..!
Basu ce komai ba kansu na kasa Hamida ke taba hanne ita kuma taki mgana Hajiya ce ta gansu Dariya tayi kafin tace"Ku sha kuruminku..Karshen sati zaku je kuga Amina..!
Baki suka washe suka hada baki wajen Fadin"Da gaske hajiya..?
Hajiya tace"Yanzu ma muka gama mgana da yayanku..!
Suka wani daka Tsalle suka Rumgume juna wani kallo yayi musu dayasa suka natsu waje daya ganin haka yasa ya mike yayi ma Hajiya sallama ta amsamai tare da cewa"Kace ma Amina su hanne na nan zuwa zasu zo mata da sako tayi hakuri..!
A kasan makoshi ya amsa ma Hajiya kafin ya fice Daga Shashen yana jin ihun yaran bayan ya fita kai ya girgiza kaawai.
Falom Mallam ya koma sukayi sallama shi da Aba ne suna mgana Daganan ya shiga motarsa zuwa gida koda ya koma Sakina ta gama komai taci kwalliya tana jiransa ta tarbesa ta taimakamai yayi wanka ya sauya kaya suka fito saman Dining suna cin abincin sai alokacin ya kalli Sakina yana fadin"Kin kaimata abinci..?
Sakina ta amsa mai da kai,Yaji dadin haka kai tsaye yace"Allah yayi miki albarka..!
Tana Mirmishi mugunta ta amsa mai da Ameen Ameen domin ta gama wasa wukanta jira take ya saka kafa ya Tafi sai Amina tayi nadama wlh.

*********

Washegari..
9:30am.
Chapter 103 · 0% Book details