Sashe 17
Ta Fita Zakka Part 1 Complete Hausa Novel · about 10 min read
Amina bata bi ta kan Hamida da Hanne dake mata Dariya ba Har suna Tafawa tayi kwafa batayi mgana ba ganin ta isa Gaban Famfo tana wanke Kafa yasa Hanne tace"Amina wai nufinki bazaki wanka ba..?
Cikin Masifa Amina ta Juyo tana Fadin"Eh din bazan yi ba jikij ki ko nawa..Ban son munafunci Hanne ki Kyaleni..!
Hanne tace"Daga mgana..?Tsiya Dake bakisan gaskiya..!
Hamida ta leko Daga Cikin Dakimsu tana Fadin"Kice dai batasan abun arziki ba..!
Amina Ta Hura hanci kafin tace"Ba"asani ba din..Hamida da Hanne bana som munafunci kowa yayi harkarsa Fakat..!
Basu kara ma tanka ta Hanne Dakin ta shige suna mgana da Hamida tana Fadamata Malam yau baya nan yaje Jigawa Saukar Al"qur'ani da wata Makaranta ta gayyaceshi sai ga Amina ta shigo Tana Hura Hanci jira take amata mgana ta Fara jidalisai ta ga Tataga sun yi banzada ita suna Cigaba da Hirarsu.
Tsab Hamida ta Shirya ta saka Hijabinta da Safa Amina ce ta Tsaya sai bata Musu Lokaci take Hanne tace"Amina don Allah kiyi sauri..Dakyar fa Baba ya barmu..Kuma kinsan in muka Dade hukuncinmu..!
Amina ta cika Bakinta da iska kafin tace"kunga nifa bana son ana Damuna..In kunga bazaku iya jira ba Kuyi gaba ban ce Dole wata Cikin ku ta Jirani ba Atoh..!
Tafada Lokaci Daya tana Bude Dirowarta ta kaya Baki ta Washe ganin Hamida ta gyara mata Cikin Shakiyanci tace"Hamidas..Kaimijinki Wlh ya More da gyara baki da kiyiwa...wlh irinku masu yima Kishiya wanki da guga harda Uwar miji..!
Ta karishe Fada tana Tsintsira Dariya Hamida tayi tsaki kafin tace"Kina da mtsala Amina..!
Amina tace"Nafi gidan Haya..Tsohowar Mota ma nan taganni ta barni don kwalubanta..!
Amina ce fa sai ta gama bata musu Lokaci kuma amata mgana tace an Dameta in baza"a jirata ba ayi gaba..
Saida ta gajida mgana kana ta shirya sai da taga Hanne ta kusa sannan ta Sauya kaya zuwa Doguwar riga tama mata kadan Gwiwan kafarta a waje ta kuma Sanya Hijabi ko kasa bai kaimata ba.
Hamida ta kalleta Kafin tace"Amina kalli kwarimki a waje..Ki saka Safa mana..!
Amina tace"Wlh bazan saka ba..Ke haka Kurum ana Fama da Zafin nan..Nifa bana son Zuhudu bazan kashe kaina ba. ke dai bakin saka ba. to miyr na Damuwa sai na saka..?
Hamida tace"Kafarki fa awaje..Kinsan fa bai kamata ba..!
Amina ta Tsaya Lokaci Daya tana Fadi "Kafata a waje take..A"a kice Tsirara nayi ba kafata a waje ba..Hamida kin fara isata acikin gidan in ban kwabe ba nace na fasa zuwa kucr ba sunana Amina ba..!
Da Sauri Hanne tace"Yi hakuri..Don Muje.Wlh in muka bata Lokaci Hajiya zatace mu barshi su Ya shamsu suje.!
Tsaki Amina Taja tayi gaba tana Fadin"Dilla yo Laifina ne..?baga wacce ta wani Dameni da mganar banza ba nan..Niwlh na tsani iyayi hamida kuma Halimta kenan Shigen Neman suna da son Nuna tafi kowa son Allah..!
Hamida ta kalli Hanne zatayi mgana ta Rufe mata baki tana Fadin"Don Allah ki kyaleta..Kinsan Halin Jidalin Amina bataki a fasa tafiyar na ba ta Zauna tana sauke mana Rashin Mutumta..!
Dole Hamida tayi shuru suka Fice Kitchen suka fara shiga suka ma Mamanmu Sallama Amina ta Bude Tukwinyar girkin tana Fadin"La Mamanmu Zogale kike Dafawa..!
Tana Dariya tace"Zulaihat na Rage ma aiki..Dambun Zogale zatayi inta Dawo Saboda Aba dinku..!
Amina tace"Wayyo Mamanmu..A ijiyemin mai yawa don Allah..!
Hanne ta Harareta tana Fadin"Ke kadai.?kina da son kai mu fa ba mutane bane ko..,?
Amina ta juya ido tana Rumgume Mamanmu ta baya tana Fadin"Saboda ni kadai ce Diyar Mamanmu ko Mamanmu..?
Mamanmu na Dariya tace"Kwarai kuma baki da na biyu a wajena..Kuje zan Dibar muku da yawa saboda Diyata..!
Fita sukayi Amina nayi musu gwalo Dakin Yaya suka shiga suka mata sallama Amina kin shiga tayi Daga waje ta tsaya suka fito Kafin su Rankaya zuwa gidansu Hanne din Shashen Hajiya suka shiga sai Fada take musu rana tayi.
Hanne tace"hajiya Amina fa ta bata mana Lokaci..!
Hajiya tace"ku kuka sani..In Malan dai ya Dawo bazaku je ba..Tun Dazu Na kira Idi na jiranku zai kai ku kuma zai Tsaya ya Dauko ku..Kuna da yawa..Kagaki ga Mamah ga Hamida da Sa"a kuyi hanzari share share da goge kunji ko..?bana son Malam ya Dawo baku dawo ba Dagani har ku ranmu sai ya baci..!
Hanne tace"To Ina key din gidam Hajiya..!
Hajiya tace"Na duba na wajena ban gani ba..Kuje shashen Amarya ku amsa wajenta tana dashi..!
Amina saita koma ta Zauna tana Fadin"in kun amso ku gayamin..!
Hajiya tace"In baki je ba..Tafi Haraba wajen Mota Idi na man na jiranku..!
Ba Musu ta mike suka fice Tare su suka Wuce Shashen Anty Amarya ita kumata koma Haraban gidan Inda Idi ke Cikin mota kirar Siana yana Jiransu.
Tafi minto goma da Fitowa sai gasu sun Fito Sa"adatu ce abaya tana wani Bude Hanci Hannunta Leda ne babba komiye aciki oho..?Sai key din gidan tana wani Kadawa Amina Kallo Daya ta mata ta Kauda kai itama Shiga Motar sukayi bayan sun gaisa Idi kamar yadda Tarbiyansu take..
Kai Tsaye daganan bai Diresu ko"ina ba Sai Kofar Arewa,inda gidan Ya Dan Mallam yake.
Tundaga Wajen gidan suka saki suna kallon Wannan Tsaruwa kamar a Turai akwai megadin Dake Tsaran Gidan wani Buzu ne,bai ko jin Hausa sosai,Idi megadi yayi Hon ya Bude musu suka Sulala Ciki tun da suka Fito sukayi ta kallon gidan ba wani Babba bame sai dai ya Tsaru matuka Gashi gabadaya Haraban gidan yana Shimdide da Marbels mai Santsi Kalan Ruwan kasa mai Duhun Get din Gidan Fari ne Fentin gidan kuma Ciki da wajensa Mai ruwan pich ne mai kyau da kyalli.
Sa"adatu ce agaba ita adole masu gida Amina ta tabe baki ita Sakarcin Hanne ta gani ita wazai je gidan Ya Jafar yamata wannan Ikon bata ci uban Mutum ba.
Sai da suka Shiga Falon suka san Waje basu ga komai ba Duk da gidan ya Dade a Rufe ammh kuma babu abunda ya Sauya wani Sanyin Dadi ne ya Daki Hancinsu sai da Amina ta Lumshe Manyan Idanuwamta tana kare ma Falon kallo.
Komai Baki da Fari ne duk yadda akayi Mai gidan yana son Kalan sosai.
Sannan Duka kujerun da Dining an Rufesu da Fararan kyallle,Sai Cafet duk an Nadesu waje Daya Komai dai yana Muhallimsa ammh an Killacesa Daman gidan bayan wani Lokaci su Ya Shamsi na zuwa suna gyarawa sannan Sai Karshen Shekara yake zuwq da ita iyalin nasa,ammh yakan zo a shekara su Uku zuwa Hudu kuma agidansa yake sauka.
Falo ne Babba sai Bedroom guda uku sai Kichen guda Biyu Sa"adatu ita ta Bude bedroom din guda Biyu Bata Bude Dayan ba ta Dago tana kallon Su Hanne Lokaci Daya tana Fadin"Bari na Bude muku kitchen ku fara da Chan kafin mu zo Falo..Ni zan gyara Bedroom din Anty Sakina..!
Bawai neman Shawaransu take ba Umarni ne take basu Hanne ko ajikinta ta taka ta mika hannu Tana Fadin"Bani key din na Bude Kitchen din..ki gyara chan din Saboda aikin yayi mana Sauri.Ko kuma Hamida ta shuga Dayam ta gyara ni da Amina mu gyaro Kitchen din ko ya kika gani..?
Da Sauri Sa"adatu tace"A"a ku gyara chan gabadaya in kun gama ga Falo.ni zan gyara Duka bedroom ai guda Biyu ne Dayan na Yaya Dan Malam ne kuma Key na wajen sa u ya Jafar..!
Hanne bata kara mgana ba ta karbi key din ta Bude kitchen din ta Juya tana cema su Amina"Bismillah..!
Hamida tabi bayanta Amina kuwa sai da ta gama Tabe baki kana ta Bisu Ciki Sa"adatu kuma ta shige Ciki abunta.
Amina baki ta saki da Hanci tana kallon Tsaruwa da Haduwar Kitchen din Shima Fari nr da baki gabadaya Cabinet din kitchen din Fari da Baki ne Hatta Tairs din Dake Kitchen din ma Fari ne yana kyali Kamar ana Gyarssa ba wani Datti sai kuran da baza"a rasa ba tunda komai na amfanin Girki suna cikin Kwalayensu ne Fridge ma ba komai aciki sai ruwa da Lemo,Hamida na Duba Kitchen din tace"Gidan ma ba wani Datti..!
Hanne na Kokarin Bude Store tace"Ai Dayake su ya shamsu na zuwa suna gyarawa..Sannan Anty Sakina gaskiya akwai Tsabta kafin su tafi sai Hada komai nata ta adana..!
Ba wanda yace wani abu har ta Bude Store din Gabadaya kayan abinci ne Dankam aciki Hamida ta Leka tana Fadin"Hanne kayan abincin su basa Lalacewa..?
Hanne tace"Suna Lalacewa mana..kamar fa wannan kwananan aka Zubasu ai kafin su koma suna Kyautar da komai kafin su koma..!
Hamida ta gyada kai tana Fadin"Ham..!
Amina dai na gede batace komai ba sai Kalle kalle takeyi basu bi ta kansa ba suka Fara goge Da kakkabe tunda sun ga tsiyaya da Moper anan Kichen din da Towel din gogen Kichen Amina na gefe ko Hamnu bata saka ba Domin Taga abun akwai rainin Wayau aciki.
Hamida ne ta juya tana kallinta kafin tace"To ke Amina tunda mun kama nan ko zaki je ji kama Gyaran Falon ne..?
Amina ta tabe baki kafin tace"Ni daman nace muku zan yi wani aiki ne..?ke hanne wai nan ba gidan yayanki bane..?
Hanne bata gane Tambayan ba tace"Bangane ba..?
Amina tace"to gani nayi ta zabi Aiki mai Sauki ku ta hadoki da gyaran Kura..ji yadda take bada Umarni kamar gidansu..In tana takama matar gidan yayartace..Ai kema mai gidan ne Yayanki kin fita iko dashi..!
Hanne tace"Sai me..?ni ina komai ne Saboda Allah da Ya Dan Malam ba Saboda wata Sa"adatu ba..Kema don Allah kidaina mgana in baki yi ba ki koma Falo ki zauna nidai muyi mu gama Lafiya mu tafi gida..!
Hamida tace"Ni ban ma ga abun mgana ba Wlh..!
Amina ta ballara mata Harara tana Fadin"Ai bazaki gani ba..!
Daganan ta yi ficewarta Falo ta koma ta Haye gan Dining ta zauna tana Kada kafa Domin daman chan batayi yi niyyar ko Tafa wani abu ba Sa"adatun tazo tayi duka mana.
Tana nan zaune Sa"adatu ta fito Daga Dayan Bedroom din suka kalli juna kafin kowa ya Kauda kansa Dayan ta shiga shima ta gyara kafin nan su Hanne sun gama da kitchen din suka Dawo gabadayansu suna gyaran Falon Sai alokacin Amina ta saka Hannu ta yaye abunda aka Lulluben Dining din ta Goge suma Kujerun sun yaye komai sun goge Dayake Sa"adatu tazo da Klin da Turaran Wuta mai kanshi na Tsinke da na Bunner Dayake akwai Wuta suka jona suka Turara gidan.
Ba inda basu share sun goge shi ba Ko"ina yayi tas yana tashin Kamshi Cikin Awa Biyu suka Idar da komai Sai da sukayi salla suka yi shirin Tafiya Alwarma a Sink din Kitchen sukayi ga yunwa sai dai suka sha Ruwa da Lemo Amina ko Ruwa bata sha ba Sallah kadai ta yarda tayi.
Karfe 2:30pm na rana suka Dawo Daganan Amina da Hamida gida suka wuce basu koma gidan Baba Malam ba.
Koda suka koma su ya Zulahait sun Dawo daga makaranta sun gama Jarabawa Ya Jafar tayi ma waya yaje ya Daukosu Tunda Idi baya nan Daman kuma Dokar Malan ce ya Hana su Hawa adaidaita,Ita da Ya Sadiya da Ya Aisha da ya Ikram da Ya Shamsu sune suke Jarabawar Neco su Ya Zeenatu sai da ya maida su Amina yaje ya Daukosu.
Amina tunda suka Dawo ba wanda yaji wata mgana Daga bakinta Da Daddare bayan sun gama Karati tana jin Hamida nata bama su ya Zeenatu da su Mamanmu Labarin gidan Suna Zaune abaranda suna shan iska ba Wuta kuma Gen yaki tashi sai mai gyara yazo.
Amina na daga Cikin Dakinsu kwance taji Sanda Hamida ke fadin Tsarin gidan Mamanmu na gefe tana Fadin"Ai bama Sakinar ba shi kanshi Dan Malam din dan gayu ne na karshe..Mun je gidan ai tun sanda aka gama ginashi sannan mun ga Hoton ginin a waya Daya Turo ma Aba dinku..!
Kowa saiTofa albarkacin bakinsa yake yi har Yaya ma tana Saka baki Amina na jinsu aranta tana mamakin yadda Yaya take Ji da Dawowar Dan Malan koda yake taji fa ance Dan Dakinta ne har waya suna yi da ita.
Aba yau ya Dade wajen Baba Malan Amina ta fara barci Sama sama taji Shigowarsa kuma tana ji yana tambayanta yaga kowa bai ganta ba Mamanmu ke fadamai inda mukaje Tunda muka Dawo nake kwance nagaji.
Bai ce komai ba,ya wuce Dakinsa Yaya ke da Aba Aranar ita take ta kai da kawon kai mai abinci da abubuwan Dayake so su kuma su Mamanmu na Tsakar gida suna cigaba da Hirar gidan Ya Danmalam sannan suka koma Hirar Biki da kuma Labarin Sati na sama Baba Malan yace za"a jere kamar yadda aka saba daman ba"a kawo Lefe sai dai kayi shi ka sakashi Cikin Dakin Amarya intazo tagani kayan Fitar Biki Daga na Amaran har na Sauran yan gida Baba Mallan ke yin komai Hajiya babba ita keda jagaba kan Komai Tare da Sahalenwan Baba Sa"idu.