← Book details Ta Fita Zakka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 193

Sashe 50

Ta Fita Zakka Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

ce awajenta.. Kallonta yake sai yanzu yake ganin yarintatarta Uwa uwace kuma ai ta wuce wasa duk da alabarin ya Fahimci mamanmu macece ta kwarai ammh bai kai Amina ta Girmamata Fiye da Mahaifiyarta sai dai ba yanzu zai nuna mata haka ba Lokaci bai yi ba sai nan gaba bai sani nan gaba na Tare dana boyayyan Kaddaran kaddaran da bata bashi Dama ya Nuna ma Amina Muhimmancin uwa ba. Ganin Lokaci ya tafi yasa ya kalli Amina yana Fadin"Shida ta kusa..! Lokaci Daya yana Kallon agogon Fatan Dake hannunsa Ido Amina ta Zaro kafin tace"Na dade..kada Mamanmu tajini shuru..! Kai ya gyada kafin yace"Hakane ki tafi..Ki Ari wayar mamanmu kimin Flashing zan kira naga Nombar zamu rika mgana Amina ai zaki min wannan alfarman ko..! Gabanta na Faduwa tace"In aka ganni zan shiga uku wlh..! Yana Dariyan mganarta yace"Zaki boye ai ba wamda zai gani ko..? Saboda ni da Rokon Nenne..! Ya fada yana marairaice mata jin haka yasa ta Daga kai da sauri yayi dan Ihu kafin yace"Nagode..Zan jiraki kinji..! Da kai ta Dagamai kafin ta fara tafiya sai kuma ta juyo tana kallonsa hannu ya Dagamata kafin ta dagamai sai da tace"Yanzu Yolan zaka tafi..! Kai ya girgiza mata kafin yace"A"a kano zan koma Amina daman nan din A hotel nake kwana yau nazo saboda na ganki muna da Shooting gobe in Oscar bai ganni ba ai na Shiga uku Amina..Nura ma in ya fara kirana sai ya Kasheni da raina..! Yadda ya fadi karshen mganar ne yasa ta yin Dariya tana wucewa da Sauri Lokaci Daya taji yana Fadin"Wlh Ina sonki Amina..Ni na sani ina sonki..! Har takai gidansu Hanne Mirmishi bai bar Fuskarta ba kamar almara wani Farimciki take ji yana shiganta Tunasa take da Duka kalamamsa sai taji kamar tana yawo a gajimare. Sauri sauri tayi dataje gidansu Hanne Ko zama batayi ba Duk da Hanne tayi ta janta da Hira don ta zauna ta kosa ta ganta agida ta Nemi katin nan kada ace ya bace data Shiga uku. Ko Rakiyar Hanne bata jira ba Data Shiga Daki ta Dauko Hijabi Tana jin Ya Abida na Fadin"Amina yau Ba"a son zama kuma..Sai faman sauri take..! Hajiya ma sai da tayi mgana ita dai Amina gaba tayi koda Hanne ta fito ta wuce abunta Baki Hanne ta tabe kafin tace"Amina tsiyanta nada yawa..! Amina bata ji kwanciyar Hankali ba sai da ta Binciko Katin nan Cikin Dirowarta bayqn ta gama yin Daidai da kayanta. Mamakinta ya ishi Hamida batayi dau mgana ba Ya Zeenati ne tace"Wlh Amina ki kwashe mana kayan nan..Nasan Halinki sai kice kansu zaki kwana..! Amina batabi ta kanta ba Sai da taga Katin nan sannan ajiyar rai ya kwace mata da sai da suka kalleta Dukkansu Hamida tace"Me kike nema ne wai..? Amina tace"To kuma ina Ruwanki Uwar saka ido..! Hamida ta tabe baki tana Fadin"Ki gyara kayanki kuma da kanki Wlh..! Jin haka yasa Amina ta marairaice Tana Fadin"Kayya Hamida..Yi hakuri badake nake ba..Anty Hamida yar aljannah..Allah yasa ki auri Shugaban kasa Buhari muje Villah mu Bude Hanci wai waya Amina Aminene a Villa Jar Uba akwai Daga kai..! Yadda ta karkance nen yasa Dole har ya Zeenatu sai da Dara tana Fadin"Ke ai Tun get din farko Sojojin Villa zasu Wurgoki waje..! Amina tace"Tab kaji ya Zeenan nan..Mune fa kalan masu kudi kalan yan gayu..! Take Fada tana wani Fari Zeenatu na Dariya tace"Aifa kalan masu kudi a bushen kirji gandas Amina kamar kin shafi kasan kabari Ko Hannen ta Fara Nanna banda ke suna chan makale a kirji kamar na maza..! Amina ta Chuno baki itama abun na Damunta kafin tace"Wlh nima abun ya isheni kaf yan ajinmu baki ga nasu ba Tumbul tumbul..Ni don Allah ko Hamida zata san min nata ne..? Kalli nata kamar Lemu sun yi Bulbul dasu..! Salati Zeenatu ta saka Hamida kuwa har da cin Tuntube wajen Fita ya Zeenatu tabi bayanta tana Fadin"Mamanmu ki fito..kiji Abunda Diyarki ke fadi..! Da gangan ta koresu suna fita ta Dauko Katin tana kallo acikin Haban Sikat din ta Boye shi ta fara maida kayan tana kwalama Hamida kira. "Hamida.Haba mana Hamidas..Zan yi miki zaman Daki na sati Daya zan tayaki gyaran gado..Yaya Hamida..Anty Hamidassassas..! Take fada Hamida na jinta tayi mata banza Daga Tsakar gidan tace"Bafa zan tayaki ba ki gyara da kanki..! Kamar Amina tayi kuka tace"Shikenan Baza"a ma ace Antyn ba Hamidu..Hamidu din..! Ba Hamida ba Hatta Yaya Dake Dakinta tana jinsu sai da ta Dara Mamanmu na cikin Bedroom dinta ko ta jisu ma bata fito ba Jawaad ne ke wasa ya kyakyalce da Dariya yana Fadin"Ita kuma Aminuu ba..! Zeenatu da Hamida suka saki Dariyan Amina na ciki na jinsu taji sunan Daya ambata yasa ta Daga Murya tana Fadin"Jawaad ina wasa dakai ko..? Wlh in na kamaka sai na yi kasa kasa Dakai..! Tagumi tayi tana maimaita sunan Aninu acikin ramta Tsikar jikinta sai da ya tashi wani yanayi ta shiga da batasan Dalili ba. Sai ta gama gyara kayanta Tsab har aHamida data shigo sai da tace"Yau wata rana Amina anyi abun kai..! Tana Hararanta tace"Yau jumma"a munafus aga ban gyara ba..! Dariya take mata Lokacin data fita alwalar mangariba ta shiga Dakin Mamanmu tana Tiolet din Cikin Dakinta yasa ta Dauki wayarta ta Sakea Sikat sai dakoma Daki tayi sallar mangariba Lokacin Yaya da Mamanmi da su Hamdiya sun fito baranda kamar yadda suka saba suna Hira ta Lallaba ta shige Dakin mamanmu har cikin Makewayi ta kuma Sakama Kofar key. Kan abun mahaya ta zauna ta fito da waya da katin Duk yadda Tsoro ya Cika kalaman Aminu na yana jirantacCike da yakini yasa ta kwashe Daya Cikin Lambobin ta Doka mai Kira. Sai da ta shiga har taji an Dauka sannan wata zuciya tace"Amina me kika aikata..? Da sauri ta kashe sai dai ta makara Tunda yace ta kirasa yaji ajikinta zata kira din yana ganin bakuwar Lamba yasan itace. Karar wayar yayi daidai da Daukewar Nunfashi Amina kafin gabanta ya koma ya Fadi Dam..! Ta rude yasa batasan tq Danna Dauka ba sai da taji muryansa yana Fadin"Hello Amina.. Nasan kece..Daman ina da yakinin zaki kirani..! Fitar muryansa kamar wani Sinadiri ne ajikin Amina hakanan taji kamar komai yana kwance mata wannan Tsoron kuma yana Fita Daga cikin kanta. Bata sani ba wannan wayar itace mafarin Kaddaranta Itace mafarin FITA ZAKKAN da tayi acikin Yan"uwanta da Danginta..!
Chapter 50 · 0% Book details