← Book details Ta Fita Zakka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 193

Sashe 49

Ta Fita Zakka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Satuttuka sun zo sun shude har an shiga wattani Amina bata kara Haduwa da Aminu ba,Sai abun yadan Fara Sakinta ta fara dawowa Daidai ta Fara Dawowa da walwalwarta har ya Zeenatu na fadin"Daman ai na Fada muku wanchan watan Salihan ne suka zo mata..! Lokacin baki ta Murguda mata tana Fadin"ni bani da Aljanu..! Sun saba gwara suyi mgana ta maida su ko Yaya Amina ta sauya suna ganin Alamunta sannan in xasu fadi gaskiya basa jin Dadin ganinta asanyaye. Har ta manta dashi ranar jumma"a Bayan La"asar Mamanmu ta aiketa ta kaima Hajiya kuka da aka aiko musu dashi mai kyau Daga gusai bata so zuwa Hamida ce ba Lafiya Cikinta na ciwo yasa Mamanmu ta matsa sai taje. Tana Tura baki ta saka Hijabinta ta Fita Tana ji ya Zeenati na Fadin"Mamanmu Amina fa bakinta take Tura miki alamun bazataje ba..! Mamanmu tace"Zeenatu fita daga idona..Bana son sharri..! Sai da ta Murmusa wani Lokacin bata san in akace ta zabi Tsakanin Mamanmu da yaya wacce zata zaba ba.. In tace zabi zatayi to sau goma mamaanmu zata zaba itace komai nata,Laifinta Dubu sai ta kare mata Ita da baba mallam Har Abada bazata manta dasu ba shi baya samun zama yanzu saboda suna ta zuwa gwaruruwa Da'awa ko ya zauna na dan kwamaki ne kuma suna makaranta sun Dade rabon da su samu Zama da Baba Mallam din Hakika tana kewarsa. Leshin Bikin su ya Zulahait ne ajikinta da Farin hijabin mamanmu Dogo ita nata duk sun Yamutse ba guga. Mamanmu ta wanke mata Hamida baafiya balle ta goge mata ya zeenatu kuwa ko mamanmu ta saka kafin ta Goge sai taci zagi da Mita da Dunguri in ma Zata gogen kenann. Lokacin data fito kanta na kasa ko alama bata gansa ba Kamar inuwa taji daga gefenta da kuma jikimta ya bata ana kallonta Tana Dagowa suka Hada ido. Gabanta sai da ya fadi gabanta ta kallah Masallaci yana kulle ne Baba Mallam baya gari ba kowq sai yara Dake wasa da Famfo bakin masallacin bayanta ta kallah ba kowa yasa ta fara Sauri ta shige gidansu Hanne bata san ya Biyota Muryansa taji. "In kika shiga baki Tsaya munyi mgana ba..Wlh zan biki cikin gidan..! Amuryansa tasan zai aikata abunda ya Fada yasa ta Tsaya tsoro take ji wannan Jidalin yafi karfinta in wani ya ganta kashinta ya Bushe ko Baba Mallam bai isa ba sai su ya Jafar sun kusa Kasheta. Ta daga kafa taga yana Binta sai ta Rude kawwi sai ta Mike maimakon ta shiga gidansu Hanne shima yabi bayanta kafa kafa har sai da suka sha kwanar Layin kamar tana jira ta Dakata azafafe ta juyo tana Kallonsa Cikin Juya mamya idanuwanta Tace"Kayi wa girman Allah ka daina Bina..Zaka jamin bala"i..! Waka taba ganin yana Tsayawa da wani agidanmu..? Kada ka jamin bala"in in ba so kake akasheni in wani ya ganmu tare ba..! Yadda yake kallonta yasa ta gane baya Fahimtarta yasa ta Damke Ledar hannunta zata Ruga da Sauri ya riko Gefen Hijabinta Amina taji kamar ta Yanka ihu ballatana ma datags wata Mota kamar ta ya Nasir da sauri ta Fizge Hijabinta tana Fadin"Innalillahi..Ka sakeni don Allah..! Da sauri ya saketa Lokaci Daya yana Fadin"Zan kyaleki Amina..Ammh sai kin jiyi kin kalleni kin ga yadda Sonki ya maidani..? Kamar bazata juyo ba yanayin muryansa yasa ta juyo tana kallonsa kallon ya shiga har cikin jikinta tana jin kamar Zazzabi zai kamata. Ya rame sai dai ya kara Fari Wayarsa ya zaro yayi wani Danne danne ya kara kunni Lokaci Daya taji yana Fadin"Gata nan Nenne..Don Allah ki Roketa..ta ce tana sona..kada ki rasa Aminunki Nenne..! Dagachan Bangaran Nenne tace"Bata wayar Aminu..Ni don kakimin ne..da na Share kafata nazo har gabanta na Duka mata..! A speaker ya saka wayar Cikin ido yake kallon Amina kafin yace"Nenne tace..Itace Duniyata..Takasa gane kaina na bata labarinki ammh nace kina Wahalar dani..! Nenne tana jinki ki roketa don Allah ta Saurareni..! Amina bata gama mamaki ba sai da taji muryan matar tana Fadin"Amina..Kina jina..Amina don Allah ki Saurari Aminu wlh yana sonki..Da gaske yake Aminu bai taba zuwa ya Duka yana min magiya kan mace ba sai akanki Amina ba don ni ba..Don Allah ki tsaya ki Saurareshi Yana sonki so na Tsakani ga Allah..! Amina taji gwiwanta ya saki karamar kwalkwlwarta ta saka Fassara mata. Sai da taji Nenne tace"Ko na Duka kan gwiyoyina ne Amina..? Ina son ganin Aminu cikin Farimciki maraya ne bashi da kowa Amina don Allah ki tallafamai..! Amina taji kwalla sun cika mata ido Tana ji Nenne na fadin"Kina jina Amina..Amina..! Dakyar tace"Naji zan saurareshi Saboda ke Saboda ke..! Da sauri Nenne tace"Nagode Amina..Allah yayi miki albarka Nagode..! Take ta fada kamar zatayi kuka yanke Kiran yayi yama kallon Amina Cikin Galabaitar da yayi kwana Biyu da bai ganta ba yasha zata nemesa bata nemesa ba shi kuma ya kasa jurewa ya Fadama Nenne komai tayi tayi ya bari ta gayama Alhaji Babba sai atura manya Tunda gidan malamai yaki barinta yace sai ya samu Soyayyar Amina bai sani ba wannan kuskuran wannan Soyayar itace zata yi katanga Tsakaninsa da Amina har Abada Zanen kaddara yayi riga ya zana bawa bai isa ya kauce masa ba. Yaga tana Shirin juyawa ne batace mai komai ba yasa da Sauri yace"Kin ce mata zaki Saurareni fa Amina..! Tsoro take ji wannan Tsoron ya shigeta Daga Fara Haduwa dashi. Tasani wannan abun bai Dace ba ammh bazata iya Ture alfarman matar nan taji nauyinta. Yasa ta waiga taga ba kowa sai yara Dake wucewa Daman anguwan bata da yawan Zirga zirgan jama"a Wani Lungu tagani kamar hanya yasa ta Nufi chan tana Fadin"banda karfin Gwiwan Tsayuwa Dakai..Ina jin Tsoro ka Shigo nan..! Bai musa mata ba ya bita Daga Farko suka Tsaya kanta na kasa tace"Meyasa sai ni.? Agidanmu bawanda na Taba ganin yayi wata soyayya kowa da Lokacinta yayi Baba Mallam zai turi mta mijinta haka akeyi tun kafin a haifemu har kuma yau da muke bata sauya ba..Ka tafi kabarni ban dace Dakai ba ni ba wacce Kake nema bane..! Bai barta ta Dire ba ya karbe da Fadin"Sai afara ta kanmu Amina..Ina sonki..Kuma soyayyarki bazata taba barina na kyaleki ba ki yarda dani..Ki soni na Rantsw miki komai zai zama Daidai da kaina zan samu Malan namai bayani bazai hanani ke ba Amina..! Kamar yana da wani abu a mganarsa yana mgana tana jin gaskiya a mganarsa ganin ta tsaya tana kallonsa yasa ya fara bata Labarinsa Tundaga Farko har karshe sai taji Tsausayinsa maraye cikin Sanyin jiki tace"Allah ya jikansu da Rahma..! Ya amsa mata da Ameen yana Fadim"Kin ji kadan Daga Labarina Amina..? Ke nasan komai akanki bana bukatar ji..Kice kina sona ko Hankalina zai kwanta..! Ido ta zaro kafin tace"Komai fa kace..? Kai ya gyada kafin yace"Eh..Harda Bakin Tsiwanki nasani..! Sai ta rufe baki da Hijabinta tana kallonsa Yar dariya yayi lokacin Daya Hangi ledan hannunta yace"Wannan ledan fa..? Ina zaki..?na tsaya yau ne kawai ba Domin nasan zan ganki ba yau jumma"a ba makaranta sai dai jikina ke bani zaki fito..! Zuwa yanzu ta fara rage tsoronta Cikin Sanyinta tace"Sako ne Mamanmu ta aikeni na kaima Hajiya..! Kai ya gyada kafin yace"Zan so na ga mamanmu nima..Yaushe zan je na gaisheta ko kuma yaushe zan gabatar da kaina wajen Mallam..? Zai karbeni kuwa..? Wlh ba waka bace kadai Sana"ata ina saida Motoci da kayan Gyaransu sannan ina da shagon gwalagwalai anan kano..Nayi alkwarin zan rike ki Amana..! Amina ta katseshi da sauri ganin kamar baya cikin natsuwarsa yasa tace"Ba yanzu ba..Kada kaje ba yanzu ba..! Kai Tsaye yace mata"Saboda mene..? Bazata iya kallonsa ba yasa kanta na kasa tace"Yanzu ba Lokacin Daya Dace bane..! Shuru yayi mata akwai tsoro atare da ita yasa ya dan Sausauta mata kansa ya Shafa yana Fadin"Lokacin yayi Amina..Ko ba yanzu zamu auran ba ina son na Rika ganinki duk sanda naso..! Idi ta waro kafin tace"A"a bazai yuyu ba..! Shima kai tsayen yace"Zai yuyu Amina..tunda kin hanani bayyana kaina ki samin mafita..Zan susuce akanki baki ga alama ba..! Amina tayi shuru ta kasa mgana ganin yadda ya marairaice yana kallonta ta kasa mai gaddama yasa tace"Sai dai mu rika haduwa anan lungu ko wanchan layin da muka Fara Haduwa..In wani ya ganni dakai agidanmu kasheni za"ayi.. Idanuwanta yake sha"awa in tana Taoro yasa yayi dariya kafin yace"To ta ina zaki san nazo..? Amina tayi shuru tana Tunani kafin tace"Sai ka rika zuwa bayan kwana Biyu..! Da gaske take yi ayadda ta Fada yarintarta ya gani yasa ya yi Dariya yana shafa sumar kansa yace"Amina ina aiki fa..?garin nan bansan kowa ba sai ki bazaki Tsausayamin Zirga zirga ba..In Nenne taji zatayi Fada dani nima zata kusa kasheni in taji ina yawo Tsakanin Titin Kano zuwa Gumel..! Sai da ya fada Taga wautarta Ido ta Juya ta raaa me zatacemai bata so ta Fadi wani abu yaji ba Dadi Tsausayi yake bata ashe maraya ne. Ganin tayi shuru yasa yace"Ina katin da na baki kwanaki..! Kai tsaye tace"Yana gida cikin Dirowata..! Kai ya gyada kafin yace"kina Daukan wayan Mamanmu ko..? Kai ta gyada kafin tace"Tab...Ni kadai ke Dauka...Bata mgana in ko su Hamida ne sai ta Rankwashi mutum..! Ta karishe Fadw tana Dariya shima Dariyan yake yi kafin yace"Daga gani mamanmu din nan na sonki..Ko kice Auta..? Amina tace"A"a ina da kani Jawaad..Mamanmu ta Dabam ce..Kamar yadda kace Girman Nenne a wajenka haba Mamanmu duk da ba ita ta Haifeni ba nafi sonta akan Yaya..! Ido ya zaro yana kallonta kafin yace"Ba ita ce mamanki ba..? Tana Dariya tace"Kaima kaji mamaki ko..? Haka kowa ke fadi in aka shigo gidanmu Yaya kamar ba ita ta Haifemu dukkanmu mamanmu ce komai namu..! Gyara Tsayuwa yayi yana Fadin"Bani kadan Daga Labarin Mamanmu Amina..Naji ina sonta kamar Nenne ta..! Amina saboda Shaukin Labarin Mamanmu yasa Ta manta da Tsoronta da aiken da akayi mata ta shiga bata Labarin mamanmu da yaya da Aba da ya Jafar da su hamida ta karishe da Fadin"Ko sau goma akace in yi zabi Mamanmu zan zaba akan Yaya..Kwata kwata bata sona kullim bata Fadin Alherina..Mamanmu ko laifi nayi tasan shi bata Fadinshi sai ta Boye Laifina ko ya"yanta basu hada kansu Dani ni ta Dabam
Chapter 49 · 0% Book details