← Book details Ta Fita Zakka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 193

Sashe 19

Ta Fita Zakka Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

*******

Ya Shamsu ne ya fara shigowa Shashen Hajiya babba da wata Jaka ta matafiya irin ta yan Saudiya haka,Hajiya na cikin Dakinta Hanne da Ya Aisha afalon suna ganinsa suka Mike gabadayansu Cikin Murna Ya Aisha tace"Shamsu har sun iso..?
Yana ijiye Jakar nan Tsakiyar Falon yace"Eh suna Haraban gida..Ina Hajiya..,?
Hanne tace"Tana Dakinta..!
Juyawa yayi yana Fadin"Ya Danmalam yace ku gyara Dakin ku akwai bakuwar zaku sauke..!
Daga haka ya fice Hanne bata Tsays ba ta Ruga Dakin Hajiya tana Kiran sunanta suka kusa cin karo Cikin Fada tace"Miye haka ke kullum baki abu Cikin Hankali..?
Tana Dariya ta makaleta tana Fadin"Hajiya su yaya sun iso..!
Kwace jikinta tayi tana Fadin"Shi ne me..?kika rikeni kamar zaki gadani..!
Ta fada tana karisa cikin Falon kafin ma tace wani abu Shamsu ya Sake shigowa da irin Jakar Dazu Ko kafin Hajiya ta samu bakin mgana taga ya Bada Hanya yana Fadin"Bismillah..!
Gabadaya Kofar suka Zubama Ido Hajiya tasan ba Danmallam bane Domin shashen Malam yake fara isa in ya Dawo kasar kafin ya shigo wajenta sannan in Sakina me Shashen Uwarta take sauka sai Daga baya take zuwa ta gaisheta.
Bata gama wannan mamakin ba wata Farar balarabiya Jajir da ita kamar ka Taba jini ya fiti ya bayyana agaban Shansu Cikin Shigar Doguwar Abaya baka tayi Rolling din gyale asaman kanta irin yadda matan Larabawa sukeyi,kyakyawace sosai ko gasan kyau zata iya shiga kuma taci sannan Doguwa ce mai Jiki kadam Hannunta Dauke da wata karamar Jaka ta mata Hannanyenta sunsha Jam kunshi kwanin Sha"awa da Burgewa Tunda ta shigo Ta saki Fararan Hakoranta da suka kara Fito da kyanta Tana kallinsu Hajiya.
Suma ita suke kallo Cikin mamaki harta Hannr data saki baki da Hanci tana kallon Tsabar kyau yau datake jin Labari yau ta ganin ma Idonta.
Ya shamsu ne ya Katsesu da Fara gaida Hajiya ta amsa tana Dan Biye mamakinta.
Da Sauri yace"Hajiya bakuwa ce..Ya Danmallam yace na kawota Shashenki kafin ya shigo..,!
Hajiya bata nuna wani Damuwa ba ta Washe baki tana Fadin"Toto..Nifa nace bakin labarawa da Safen nan..Maraba maraba Sannu da zuwa..!
Tafada Cikin Sakewa Duk da batasan me Hajiyar ke fadaba Tunda batajin Hausa sai larbci ance Tabarman Fuska tafi ta tabarma yadda take ta mata Dariya yasa ta gane tana mata Lale ne.
Shamsu ta kalla daya ijiye jakar hannunsa inda ya Sauke Dayan Dazu tace"Shukran..!
Mirmishi yayi mata shima aransa yana Fadin ina Yaya Danmallan ya Samo Balarabiya mai kyau haka sai da bai tanka ba ya Fice Daga Falon.
Hajiya ta kalli SAROOD tana Fadin"Maraba lale..Kariso mana..!
Hanne ta saka Dariya tana Fadin"Hajiya wayace miki tana jin Hausa..?
Hajiya tace"Oh to..To ku da kuke yara yanzu kwalkwakar take ku mata labarcin mgana kuce tazo ta zauna ai bata ta tsayuwa ba..!
Aisha ce taje ta kamo hannunta tana mata Sannu da zuwa Cikin Harshen Larabci batayi mamaki ba Sanin Daman Umar ya fada mata zataji Radin zama a Nigeria Domin agidansu akwai masu jin yaranta.
Har kan Daya Daga Cikin kujerin Falon ta zaunar da ita sai dai bata Zauna ba ta Zame ta Zauna kasa Cafet kanta na kasa Umar ya fadamata Shashen Mahaifiyarsa za"a kaita Shiyasa kanta na kasa ta shiga gaida Hajiya da Harshenta Hajiya na jin Larabci tun abaya don ma Shekaru da kuma Rashin yinsa Lokaci zuwa Lokaci.
Cikin jin Dadi ta amsa mata da Tambayan Hanyan ta amsa da Alhamdulillah kanta na kasa Muryanta Dadi Cikin Harshenta.
Hajiya ta kalli su Aisha tana Fadin"Aisha ce mats ta tsshi a kasa..Ta zauna kan kujera..ke kuma Hanne kwashe kayan nan kika Dakin ku..Ki kuma Shiga Kitchen ki Hado mata Ruwa da Lemo..!
Daga haka ta wuce zuwa Dakinta Aranta tana Tunanun ti wacece wannan yarinyar da Danmallam ya Taho da ita kuma kai Tsaye a bata Masauki a shashenta da wannan Tunanin ta karisa Dakimta bazatayi gaggawa ba koma me ke ciki tasan Malam ya sani Tunda tasan yaronta bazai Taba zuwa da wata garin nan batare da Izinin Malam din ba..!
Kowacce tayi abunda Hajiyar ta sakata Hanne ta kwashi kayan zuwa Ciki Aisha kuma tace mata ta Hau kujera sai taki Mirmishi Kawai tayi.
Kafin Lokaci an cika gabanta da Ruwa da kunun ayan da sukayi Jiya da Daddare.
Bata taba ko Daya ba tana gefe kanta na kasa tana wasa da adon Kwalliyar Dake Cikin Jakarta Hanne da Ya Aisha suna gefe suna kallonta kowacce aranta tana ayyana kyau kamar ita tayi kanta wannan Balarabiyar da Tambayan Ina Ya Danmlam ya samota..?
Hajiya tana Shiga Bedroom dinta Wayarta Dake kan gado na neman Dauki tana Dubawa taga Danmalam ne,Da Sauri ta Dauka Tana Fadin"Danmallam kun iso Lafiya..!
Dagachan Falon Baba Malam Baba Sa"idu na zaune akasa kuda da Baba Malam Dake kan kujera Cikin Farin Raawani suna mgana shi kuma yana Daga chan gefe kamar zai bar Falon kansa na kasa yana Shafa Sumar kansa da bata da yawa.
Cikin Tattausan Muryan da ban taba jiba wacce ta Chakule da Labarci Yasa bata fita saosai kamar yana Koyonta yace"Mun sauka lafiya Hajiya..!ya muka Sameku..?
Hajiya tace"Duka muna Lafiya..!
Sai kuma Shuru ya biyo baya Hajiya Bata Damu ba Sanin Halinsa ko Waya ya Kirata sai ya bata Lokaci kafin ya ce wani abu bayan sun gaisa.
Kamar ana Fizgan mganar Daga bakinsa yace"Hajiya kinga Bakuwa ko..?
Hajiya tace"Eh fa..Yanzu na Dawo Ciki Shamsu yace kai kace ya Kawota Shashena..!
Karkaace kai yayi kamar mace kafin yace"Eh Hajiya..Aisha na kusa ko Hannatu..!?
Hajiya tayi mirmishi tace"Suna Falo Tare da Bakuwar Danmallam ko na fita na kirasu ne..?
Sai da yayi shuru jin bai yi mgana ba yasa tasan yana jin nauyin yace ta kai musu wayar ne yasa ta Nufi kofa tana Fadin"Kada ka damu..bari na fita na kai musu wayar..!
Da kamar yace ta barshi bari ya Kira Sarood din ammh Hajiya Har takai Falon ji kawai yayi tana Fadin"Lafiyanku kuka zauna kuka tasa Bakuwa agaba kuna kallo..?bana son Shanshanci..Ke Aisha karbi Waya yayanku na son mgana Dake..!
Tafada tana mika musu wayar ganin yadda suka wani tasa Bakuwa gaba suna kallon Dariya sukayi harda Hanne yana ji sanda tace"Wlh Hajiya tana da kyau baki gani ba..?
Hajiya ta tsaki kafin tace"Bangani ba..!
Daidao Sanda Aisha tamai Sallama Cikin Girmamawa ta gaisheshi ya amsa Lokaci Daya yana Fadin"Keda Hannatu meyasa bakuje makaranta ba..?
Da Sauri tace"Yaya ai muna Jarabawa ne.kuma yau bamu dashi ni da Sadiya da Ikram duk muna gida Hanne kuma sun gama Jssce suna gida suma sai an koma Firsttime..!
Kansa ya kara shafawa ya manta fa ko Dazu Shamsu ya fadamai haka da sukaje Dutse suka Daukosu Daga Filij Jirgi,Dayake ta Kano suka SaukavDaganan suka Hawo Jirgin Daya kawosu Dutse.
Cikin Muryansa mai Cike da Zati yace"Kunga bakuwa ko..?
Tace"Eh yaya..Mai kyau da ita wlh ya sunanta..!
Dan Bakinsa ne ya Motsa kafin yace"Sarood..sunanta batajin Hausa ki rika mata Labarci yanzu dai me kuka bata..?
Kai Tsaye tace"Ruwa da abun sha..Muka fara bata yaya..,!
Kamar bazai yi mgana ba sai chan yace"Aisha ki kaita Dakin ki kice mata tayi wanka..Ta huta tukunnah kina jina..?
Da Sauri tace"To yaya..!
Kai Tsaye yace"Mika mata wayar na Fadamata..!
Ba musu ta mikamata tana Kallomta Tace"Yaya..!
Karba kwwai tayi ba Domin ta gane ba tana kara a kunme taji muryansa Nan da nan ta washe baki basu san me ya Fadamata ba suka ga ta mike Lokaci days tana mika Aisha wayar Ita kuma tayi gaba sai gata tana Binta abaya Har Dakinsu Hanne ta Bisu da kallo kawai
Har Toilet din sai da Aisha ta nuna mata sannan ta Fice ta barta bayan ta ja mata Kofar Dakin Hajiya ta shiga ta Isketa tana Duba wani Turaran wuta da aka aiko mata Daga garinsu Maiduguri duk yanzu Saboda Rashin Zaman lafiya Danginta duk sun Dawo Cikin maiduguri wandanda suka Rage Mahaifinsu ya Dade da Rasuwa.
Mikama ta wayar Tayi Hajiya ta karba batayi mgana ba ita bata wannan Shisshigi sai Aishan ne tace"Hajiya Dakin mu yace na Kaita tayi wanka ta Huta..!
Kai kawai hajiya tw gyadamata bata ce komai ba ba irin si Daya da Abida ba mai Shigen Surutu ba ko Hanne yaasa bata Damets ta fice ta barta sai Faman Raba Turarenta take zata Bama abokan zamanta Sauran ta aika ma su mamanmu Dashi haka Hajiya take Ko sun san da abu ko basu sani ba Sai ta Dibar musu wannan Kirkin nata kowa yana Girmamata Saboda shi.
Chapter 19 · 0% Book details