← Book details Ta Fita Zakka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 163 OF 193

Sashe 163

Ta Fita Zakka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bangaran Amare kuma suna gidan su ya jafar Kamar yadda aka saba Su da sauran yan"uwansu su ya Zeenatu ya Abida ya zulaihat da su ya Ikram da su ya Sadiya har sa"adatu bata ware kanta ba wannan karom duk suna Tare ya Aisha Kadai ce bata iso ba,Abida tayi ta Kiranta sai tace mata tana tafe yau komai Dare insha Allahu. Hanne da Hamida kam sai a hankali duk sun yi wani irin sanyi su Ya Abida nata musu tsiyan Amare,gwarama Sa"adatu ta saki jikinta ana ta harkokin yin Meatpie din walima da ita tunda su ya Abida ke yinsa anan gidan shi da Donut,su damuwar su Daya ayadda biki ya zo ammh ba Amina sannan ai Hajiya ta musu alkwarin Amina zata zo ammh basu ganta ba ko da Safen nan da suka je gidan sun mata mgana ta musu Dariya tace kada su damu Amina Zata zo insha Allahu. Ya Danmallan kuma tunda suka Dawo basu hadu dashi ba Sunga dai Sakina,shima a shashen Anty Amarya,Sai sarood dake shashen Hajiya tuni Sakina ta Daina janta kusa da ita da sun iso garin zata janye mata sai dai ka ganta zaune bangaran Hajiya tana Bin kowa da kallo in taga mutum kuma ta fara mai Mirmishin ta din nan tunda ba jin abunda mutane ke cewa take yi ba. Misalin karfe Daya na Rana Hajiya ta kira Wayar Danmaallam yana gida alokacin domin tun bayan da ya kawo Sarrod ya koma ya kwanta Gidan mallam ya cika da Hayaniya damam sun gama mgana da Aliyu kenan shima suna tafe shi da matarsa da ya"yansa sai Jibi asabar zasu koma sai ga Kiran Hajiya daman tunda ya Dawo ban da gaisuwan da sukayi Jiya basu yi wata mgana ba gwara ma mallam sun samu zama shi da Aba sun yi Hira sosai saboda gidan ya cika da Jama"a banda ma shashen Hajiya bai shiga ko"ina ba. Da Hanzari ya sake yin wanka ya sauya kaya Cikin shigar Wani Farin yadi Dinkin riga da wando na Zamani da Hula,Allah ya taimakesa ko da ya iso ana salla nan masallacin mallam Duk da bai samu duka ba ya samu Raka"a Biyu mallam ma baya nan ya Shiga Cikin Collage din Gumel ta Fce suna da taron da aka gayyaceshi. Ya Shiga gidan cike da Mutane Kansa na kasa yana gaisawa da duk wanda ya Hadu dashi har Falon Hajiya inda ya Duka yana gaisheta da goggon ninsu na maiduguri,sauran yara yaran matan kuma suna gaisheshi yagana ne tace mai Hajiya na Ciki yasa ya tashi ya shiga sarood na Dakin su Hanne ta shiga Sallah shiyasa bai ganta ba. Koda ya shiga Dakin Hajiya suna waya da ya Aisha Shi dai baisan me tace ba yadai ji Hajiya na Fadin"Shikenan Allah ya kawo ku Lafiya zaku iya tasowa yanzu..Munyi mgana da mallam kafin ya fita..! Daganan sukayi sallama shi dai yana Duke agabanta kansa a kasa Hajiya ta gama wayanta ta juyo tana Fadin"Mutanen madina..!. Kansa ya shafa yana fadin"Hajiya mun same ku lafiya..! Hajiya ta amsa da Lafiya lai daganan suka gaisa da Tambayan Hidima shuru yadan Biyo baya kafin Hajiya ta gyara Zama tana fadin"Kun yi mgana da Amina tunda ka dawo..? Kansa na kasa yace"Eh Sau daya mukayi mgana da ita Hajiya..! Hajiya ta jinjina kai tana Fadin"Daman kan mganar tahowar su ne ita da Amina..Sun gama shirin su ni na Tsaidasu saboda Wani Dalilina..Naso Da sun sauka Amina ta wuce gidanta sai mallam yace bai kamata ba nan zata sauka tukunnah Shiyasa sai na sauya Shawara yanzu dai nace su taho ita da Aishar ne da Aminar sai yakaka da zasu zo tare da Direba..! Danmallan kansa na kasa yace"Allah ya kawosu lafiya..! Hajiya ta amsa da Ameen tana Fadin"Yau dai abunda muke Boyewa zai bayyana..Amina Zata dawo ammh ba ita kadai ba da abunda kowa zai yi mamaki..! Shidai bai ce komai ba kansa na kasa Hajiya tace"Shikenan tashi kaje kiran da nayi maka kenan daman..! Ba musu ya mike yayi mata sallama ya Fice yana tunanin murnan da Amina ke Ciki jiya da sukayi mgana sai shagwaba take mai kan sun gama shirinsu Hajiya tace su Dakata shi ya Lallasheta da fadin kada ta damu da ita za"ayi wannan sha"anin. Yau kuma bai samu ya Kirata ba,Zumudin tafiyar ne yasa ko kiransa ma batayi ba sun dai yi mgana da Aisha da Safe kan asibitin da Amina ke zuwa awo sun je sun amso Takardun duka report dinta sannan ya basu shaidar ko a ina Amina zata Haihu in suka nuna wadanan takardun Babu matsala. Yaji Dadin Hikimar Aminar da Mijinta Saboda shima yana Tunanin ba lalle Amina ta koma ba,Duk da Hajiya bata fadamai ba ammh ai tace gidanta zata Zauna ta Haihu tayi jegonta. Yana fitowa daga shashen Hajiya suka ci karo da Anty Amarya ta fito Daga kitchen nan suka gaisa har tana cemai bazai shiga ya duba Sakina bane..? Sakina na ciki kwance Zazzabi ya rufeta bai damu ba yace zai mata waya mata sun yi yawa ya samu ya fice aransa kuma bai yi niyyar kiranta ba ai tasan dashi tun shekaran jiya bata nemesa ba Shima ya shareta ai ba ita kadai garesa ba balle ya Damu sannan Ciki kuma ai ba kanta Farau ba shi Allah ya tuba ma ko ZUMUDI bai yi ba wannan karln to me za"a a nuna mai shi da ke da mai Ciki haihuwa ko yau ko gobe..? Ai karyar barazana kuma ta kare yadda ta ke wani tsirfa ma mamaki take basa shiyasa tunda suka zo tace wajen Anty Amarya zata zauna bai damu ba Ko a kwalar rigarsa. Dakin su Uzairu ya shiga suna taba Hiran inda yake sarvice daya ke shima ya Dawo shima da Safen har shamsu ya iso Dazu shima wannan Bikin fa na musamman ne kowa da kowa yana nan Saboda bikin mata ne kuma Sune na layim karshe daga su sai maza su Nazeem in sun tashin yin kenan nan kusa Har Mutanen bazanga mata da basu Cika zuwa ba sun zo wannan karon Bikin su Hamida kan kowa yasan yayi goshi. Sun Dade suna hira dashi tare sukaci Abincin Rana da Hajiya ta aiko musu dashi Tunda tasan suna cikin Gidan sai La"asar suka fita Danmallam ya bada salla bayan sun idar ne sai ga Aliyu sun iso ya fita ya tarbesa Suka gaisa da Aliyu ya Dauki karamin yaronsu Hammad ita kuma Aliya da yar macen da Cikin jikinta Daya fara fitowa suka nufi Cikin gida. Sai da ta fara zuwa shashen Hajjya suka gaisa har taga Sarood tana ganinta ta fara bashe mata baki taga wanda ta sani ammh Aliya ko kallonta batayi ba Ko Dadewa batayi ba ta baro Shashen Hajiya zuwa na Anty Amarya wajen sakina daman sun yi waya tun kafin ma su fito Daga gida. Anty Amarya sai ina ka saka da Aliya take yi ita kuma Sakinar na kwance Dakin su Sa"adatu wai bata jin dadi Zazzabi ne ya rufeta Ammh ganin Aliyan sai ta mike tana wani yamutsa Fuska. Aliya na kallonta tana Dariya tace"Masu Ciki..Yan Laulayi..! Sakina tayi far da ido kafin tace"Kedai bari tunda muka iso ban jin Dadi..komai ma baya min Dadi..Chan gidan fa warinsa tadamin Hankali yake yi na baro sa na dawo nan..! Aliya tace"Sannu sai Hakuri..Zuwa gaba zaki ji Dama dama in Laulayin ya ragu..! Sakina tace"Allah yasa ya hanya..! Ina Aliyun da hammad..? Aliya tace"Suna wajen tare da Umar..! Sakina tace"Yazo kenan..? Aliya tace"To nadai gansa a waje fa..! Sakina tace"Rabona da ganinsa tun shekaranjiya da muka zo nan..! Bai sake nema na ba. ! Ta fada cikin wani yanayi Aliya tace"To kinsan kila saboda mutane..! Sakina tace"Waya fa..! Ai sai ya Kirani yaji ya nake duk wannan wahalan da nake sha duk shine Sila fa..! Aliya tace"Kuma fa hakane..kimai Uzuri dai ammh ai naga kishiyarki dana shiga Shashen Hajiya sai wani washe min Baki take yi nayi kamar ban ganta ba. ! Sakina tayi tsaki tana fadin"Bar munafuka ita wai ta ganki ta ganeki mana..! Aliya tace"Ta gane Ubanta..!!? Aiko taga wulakanci domin ko kallo bata isheni ba..! Sakina tace"ai tunda muka zo bata kara ganina ba..Na yakiceta ajikina..! Aliya tace"Ai hakan ya kamata ina Wani Cigaba ka hada kai da kishiya..Duk fa Kirkinta sunanta Kishiya..! Sakina tace"Ai saboda na sami abunda nake so ne..kuma na samu shiyasa na yakiceta Daga jikina..! Aliya tace"Wlh hakan ma yafi..! Daganan suka cigaba da Hirarsu suna ta zagin Sarood Aliya ce ta kalli Sakina tana fadin"Wai ina ita Labarin Kazamar yarinyar nan .? Sakina tace"Wace wai..? Aliya tace"Amaryanki mana..Waa ma take da suna..? Amina take ko wa..? Sakina ta ja wani Dogon Tsaki kafin ta mike tana Fadin"Ina na sani..! Nifa na manta ma da ita kwatakwata sai da kikayi mganarta..! Aliya tace"Wato ma kin manta da ita..! Ni fa ina mamakin ina Hajiya ta kaita..?har Aliyu na Tuntuba yacemim bai sani ba bama suyi mganar da Umar ba. !. Sakina tace"Ai hashashemu ya tabbata. inaga ba auran nan..! Aliya ta zaro ido tana fadin"Ta ya akayi kika sani..? Sakina ta Bude kofar Tiolet tana Fadin"To in da auran da baki ganta ba. ?ai ba haka ake aure ba Aliya. Bari nayi alwala ban yi sallah ba .! Aliya ta bita da kallo tana fadin"Nima ki fito nayi muna hanya ta same mu..! Ammh a kasan ranta tana Tunanin Ta yaya Umar zai saki Amina..? Hajiya da mallam kuma sun sani basu ce komai ba..? Gaskiya tunanin hakan bai zauna mata ba sai dai in wani abun ne Dabam ammh banda mganar Rabuwa. Sakina na fitowa itama ta shiga tayi alwala sukayi sallah bayan sun idar Aliya taci abinci suka kimtsa Sakina tace su leka wajen Walima ana ta Tafiya,Koda suka fito duk an watse har Anty Amarya ta tafi da wasu yan"uwansu Daga Dutse Hajiya ce kadai ya rage bata tafi ba sai wasu yan maiduguri,Sakina gaba sukayi ita da Aliya sai a hanya ne suka hadu da su Zulfa da Yara sun dauko musu waina da za"a raba awajen Walimar suka Dumguma zuwa haraban makarantan koda sukaje har an fara Amaren ma sun iso sun yi shigar bakaken jallabiya da Farin Hijabi Sa"adatu ne dai Fuskarta acike ammh Hanne da
Chapter 163 · 0% Book details