← Book details Ta Fita Zakka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 193

Sashe 22

Ta Fita Zakka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kamar ta kifa haka ta sauko daga kan Kujeran tana Raba ido Cikin Kifta ido Tace"Sannu da zuwa ya D'anmallam..!
Bai amsa mata illah Falon Dayake bi da kallo kafin yace"Ina Anty..?
Da Sauri ta mike tana Fadin"Tana Dakinta ita da Ya Sakina..!
Baima ce ta Kirata ba yaga ta wuce sai bai kirata ba Hannayensa Cikin Aljihun wandonsa ya kurama waje Daya ido kamar mai nazari.
Sa"adatu sai da tayi knooking Domin Tun isowar Sakinar tana kuka suka Kule Cikin Daki ita da Anty basu Fito ba,Kuma sun kulle kofar Daga ciki Anty Amarya da Ranta ke bace domin ta gaji da Lallashi da Tambayan Sakina meke Damunta taki gayamata gabadaya Tunda suka iso take kuka taki mgana ballatana tasan meke Faruwa..
Dagachan tace"Waye..?
Da Sauri Sa"adatu tace"Nice Anty..!
Tashi tayi taje ta Bude Kofar da Sauri Sa"adatu tace"Anty Ya D'anmallam yazo yana Falo..!
Da sauri tace"Yazo .?
Ta daga kanta Sakina ta juya tana kallo wacce ta Dunkule kan gado tana kuka kafin ta Dawo da kallonta kan Sa"adatu tana fadin"Kice mai gani nan zuwa..!
Daganan Sa'adatu ta juya ita koma ta maida kofar ta Rufe ta Dawo bakin makeken gadon Dake Bedroom din inda Sakina ke Dunkule ta Dade tana kallonta kaf ta gama Hasashenta bata hango abunda zai sa Tunda suka iso Sakina ke wannan kukan ba ta kuma yi Tambayar Duniyar nan Sakina taki Mgana.
Kai ta kada Kafin tace"Ai shikenan Tunda bazaki mgana ba..ga Umar din chan yazo..Bari naje na tambayesa kila shi ya fadamin abunda ke faruwa..!
Har ta bar Dakin bata Dago Daga kukan datake yi ba ballatana tasaka ran zata kalleta
Ta iskeshi Tsaye bai ko zauna ba Sadiya ta fito sun gaisa Sa"adatu ta shiga Dakinsu ta Fadamata zuwanshi.
Yana ganin Fitowarta ya Rage tsawonsa ya Durkusa kan kafafunsa yana gaisheta ta amsa Lokaci Daya Tana zama kan Daya daga cikin kujerun Dake Falon.
Daga gaisuwan ne bai kara cewa komai ba kansa na kasa yana kallon adon Zanen jikin Tattausan Cafet din Dake Falon.
Anty ta kalli su Sadiya kafin tace"Ku tashi ku shiga ciki..!
Ba musu suka mike zuwa Dakinsu sai da taga Shigewarsu kana ta maida Hankalinta kansa kafin Tace"Umar meke Faruwa ne..?ko kun samu Sabani da Sakina ne .?Tunda kuka iso take kuka gatachan kwance kuma nayi Tambayan Duniyan nan tayi banza dani har yanzu taki cemin komai..Shine nace bari kai na Tambayeka meke faruwa ne .?
Kansa na kasa bai Dago ba abu Dayane ya kara bashi mamaki me Sakina ta Dauki kanta ne..?tana Tunanin kukanta da Rigimanta zai sa afasa komai..?ai ta makaro Domin bakin Alkalami ya riga ya Bushe..Sannan bata isa yasa ya Sauya abunda Allah ya Tsaramai ba Duk da karin aure bai Cikin Tsarinsa.
Yasan yana da Sanyin Hali baya son Damuwa da Hayaniya ammh tasanshi Yana da zuciya mai karfi wanda in yagaji da baka baki bazai biyema iskancinka ba zai Fita batunka ne kamar ita yadda tayi mai tun suna Madina yake bata baki ganin yadda Hankalinta ya tashi bayan ya gayamata bayan an Daura auran Abunda yasa ya Biyemata yana ganin ya bata mata Tunda shima abun Daga sama yazo mai ammh akallah ba Dadi Kaji Mijinka yayi aure Lokaci Daya sai dai ya gaji da Lallashinta zai kyaleta In ta gama kukan don kanta ta Hakura shi bai kuma san da wani Kalma zai kara lallashinta ba.
Anty Amarya ta gaji da jiran amsar sa bai ce mata komai ba gabanta nata Faduwa kada matsalan yazama babbace Fiye da Tsammaninta.
Yasa ta gyara zama tana Fadin"Kayi Shuru..!?Ina fatan Allah yasa abun bai kai ku ga Saki ba..?
Sai alokacin ya Dago yana kallonta bata ga wani abu a Fuskarsa ba Illah Haibarsa da Zatinsa Cikin kakkausan Muryansa mai Cike da Sanyi yace"Babu ma mgana makamancin wannan Anty..!
Ajiyar rai ta sauke na samun natsuwa kafin tace"To me ke faruwa..?
Nan ma Shuru yayi mata ta kara kallonsa tana nazarinta har ta Fidda rai da zai yi mgana sai chan taji yace"Tunda bata gayamiki ba..Bakomai kenan..!
Kai Tsaye ya fada batare da Tunanin wani abu ba ya mike yamata Sallama ya Fice Daga Dakin tana Binsa da kallon mamaki.
Aranta tana ayyana wani abun Meke Faruwa..?meyasa Sakina taki mgana..?tana ji ajikinta koma miye babban al"amari ne sannan ta godema Allah daya kasance ba Zencen Saki bane Komai miye ai zai zo da Sauki.
Tashi tayi ta koma Dakin ga mamakinta sai ta iske Sakina ta shiga wanka sai taji Dadi,Yasa ta fita da Sauri zuwa Dakin su Sadiya tace su tafi Kitchen su sama ma Sakina abunda Zata karya dashi Dakin ta koma ta iske Sakina ta fito Fuskarta Duk ta kumbura idanuwanta duk sun shige Saboda kuka.
Anty Amarya ta kalleta tana Fadin"Ko kefa Sakina..?
Dagowa tayi ta kalleta Fara ce kyakyawa Daidai Misali sannan ita din mai matsakaicin Tsawo ce Tana da Jiki kadan da Jikin mata.
Kai Tsaye tace"Ya gayamiki wani abu..?
Anty tace"Kema kinsan bazai yi mgana ba..Umar yafi Ubansa Miskilanci da kyaluwa..!
Dan Mirmishin Fatan baki tayi Lokaci Daya tana Cije bakinta Towel ne Babba ajikinta taja Kujeran gaban madubi ta zauna ta Fara Shafa mai,Acikin Ranta tana jin kanta yayi mata Girma kamar zai Rabe Biyu Saboda Tsananin Kunar da zuciyarta ke mata.
Tana gama Shafaa mai ta Sauya kaya Cikin Wata Riga da wando Saukakku,Lokacin Sadiya ta shigo mata da Faranti shake da kayan karyawa Tea kadai ta sha bata iya cin komai ba,Bakinta ba Dadi Saboda yanayin Datake ciki.
Tagama kenan sai ga Anty Amarya ta shigo Dakin tana kallon Farantin Dake gabanta take fadin"Ya haka..?naga baki ci komai ba..?
Sakina na Sake komawa kan gadon tace"bakina ba Dadi Anty..!
Anty ta waro ido kafin ta karisa gefen gadon ta zauna tana Dafata Lokaci Daya tana Fadin"Ke na tabaki da Alheri Sakina..Allah yasa abunda muka Dade muna jira ne..?
Cikin Mamaki take kallonta kafin tace"Me kenan..?
Kai Tsaye tace"Ciki mana Sakina..Naji kince bakin ki baya Dadi..shine nake Tunanin kodai kodai..!
Da Sauri ta katseta ta fadin"Ba ciki bane Anty..Wannan al'amarin yafi gaban na..Rufo kofa kizo kiji..!
Da Sauri tatashi ta Rufo kofar ta Dawo ta Zauna kusa da ita kamar wata kawarta.
Sakina ta Fara matsan kwallah kafin tace"Anty Umar fa aure ya kara..!
Anty tayi wani Sansarai rai kafin tace"Aure wani irin aure kuma..?
Sakina ta ballo Hawaye saman kumatunta kafin tace"Aure da kika Sani Anty..Abun bakin cikin ma bai Fadamin ba sai da aka Daura auran. !
Anty Amarya ta Dafe Kirjinta kafin tace"Daman da gaske kike yi Sakina..!Wani irin aure kuma ana Zaune kalau..!
Sakina tace"Uhm yadda kikaji haka naji Anty..Ni ba komai yafi Tadamin Hankali ba..Irin matar daya aura..Anty Balarabiya ina ni ina kishi da Balarabiya..?
Ta karishe fada tana Kuka Wiwi Anty Amarya ta Dora Hannu akanta tana Fadin"Na shiga tara ni Marliya..?wannan wani irin kaddara ne..?
Sakina ta kwanto da kanta Saman Cinyar Anty Amarya kafin tace"Kaddara mai muni ma Anty..Kinga kyan yarinyar..?wlh ko gasar kyau ta Shiga sai taci..Tafini komai da komai ta bangaran kyau da Zati da nasaba da asali Wlh Anty wannan suka fara zama da Umar ni Bora zan zama..!
Ta karishe Cikin gunjin kuka Anty Amarya gabadaya jikinta rawa yake yi Cikin Tashin Hankali tace"Wai garin Yaya haka ta faru...?Diyar wacece ya auran..?
Sakina tace"Diyar abokin Baba Mallam ne..!
Anty Amarya tace"Kattab..?
Da Sauri ta Daga kai kafin ta cigaba da Fadin"Ita..Diyar su din nan kwara Daya Sarood..yadda Umar din yace min shi Abu kattab din ne ya bashi Auran kuma bazai iya kin karba ba..Ni ban sani ba saida aka Daura auran a Satin da zamu taho..!
Anty Amarya gabadaya Hankalinta baya Jikinta Har Sakina ta cigaba da Fadin"Tashin Hankalina Daya Anty..In tazo ta Haihu fa..?wlh Bora zan zama a idon Umar da Danginsa na zama bani da wani amfani..!
Da Sauri Anty Amarya tace"Ina.karya ne..Ba wanda ya isa wlh..!
Ta fada Lokaci Daya tana Ture kan Sakina Daga Jikinta ta mike tana Mazari Cikin bacin rai tace"ba wanda ya isa ya maidake baya Sakina..Kamar yadda ban zama baya ba..Wani Cikin ya"yana bazai taba zama baya ba..!
Take Fada tana Huci Sakina ta Mike Zaune tana Sharan kwallah kafin tace"Nama zama..Domin da ita muka zo kasar nan..!
Da Sauri ta zaro ido tana Fadin"Eyee...!
Sakina ta Daga kai tana Fadin"Eh tana ma Cikin gidan nan..Inaga Shashen Hajiyarsa yace shamsu yakaita..!
Anty Amarya ta rike Haba Kafin tace"Kenan iyayen nasa sun san da Labarin auran shine mu bamu ji ba..?
Sakina tace"Ni bansani ba..Ammh dai Malam ya sani Da Baban su Jafar tunda naji suna mgana tun muma chan..!
Anty Amarya ta Lailayo Ashar ta Dankara kafin tace"Sa"idu...Sa"idu..Ko bai kira Malam ba..Ina mai Tabbatar miki Sa"idu zai fara kira..Sa"idu ne ja gaba kan komai..Ko Malam da Hajiya basa tsallaken Shawaran Sa"idu abunda yace shi akeyi acikin Gidanan Sakina..!
Sakina ta Sharce majina tana Fadin"Anty ya zamu yi..?wlh karki so ki ganta Kinga kyanta..?
Anty Amarya Haushi ya kamata ta Ballama Sakina Harara tana Fadin"Kyan me..?kyanta na banza..Takai ki wayau ne..?Kyan ne kawai ammh batakai Budewar ido ba ..ina taje ina ta taka..?Irin wadanan kyan ne kawai da zaman waje Daya na Tabbata bata samu wata Sakewa ba..!
Sakina tayi shuru tana kallonta kafin tace'"Eh kam..kamar sakara haka take..Sai dai namiji ba ruwansa da wannan..!
Anty Amarya tayi Mirmishi kafin tace"Kada ki damu kanki..Ki Share Hawayenki kada ki kara kuka..Waannan auran wani matakin Nasarmu ce Sakina..!
Sakina tace"Taya ya..?
Anty Amarya ta kama Hanyar fita tana Fadin"kidai ki saka ido kawai..Mu zuba mu gani..!
Shege ka fasa..!
Daga haka ta Bude Kofar ta Fice tana Tafe tana Mirmishi ita kadai kamar an ce mata an biya mata aikin Hajji.
Falo ta koma ta Zauna ta Dora Kafa Daya kan Daya tana Kadawa kamar wata yar yarinya yar shekara Goma sha.
Sakina kuma tana Fita ta koma ta kwanta Damuwarta ya ragu,Saboda tasan duk abunda Anty tace kada ta Damu to tasan cewa kada ta Damun komai zai zama Daidai,Daman ga Rashin barci ga Damuwa yasa batasan Lokacin da barci ya kwasheta ba Cike da Mafarkin yadda makomarta zai kasance Tsakaninta da Umar da Sarood.

******
Chapter 22 · 0% Book details