← Book details Ta Fita Zakka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 193

Sashe 45

Ta Fita Zakka Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

*Janafty*
[11/3, 2:05 PM] Sweet sis: *TA FITA ZAKKA..!*
_(Aminene)_

*Wattpad:JamilaUmar351*
*Mallakar:Janafty❤️*

*🅿️16*

*Yola..*
BAYAN WANI LOKACI..!

Kwata kwata bai ji kiran sunansa da take yi ba sai da ta Daddage ta Dirkamai Duka a gadon bayansa kana ya dawo cikin Hayyacinsa Dago Shanyayyun Idanuwansa yayi ya zube akanta cikin kosawa yace"Haba Nenne..!
Haba..!
Ya ke fada yana sosa bayansa Hannu ta kai zata Dukansa ya mike Tsaye da Sauri yana Fadin"Haba mana Nenne..!
Wannan ai cin zali ne..!
Tana Hararansa tace"Awa na nawa a Tsaye akan ka ina ta mgana baka ji ba..?
Anya Aminu wani abu baya Damunka..!Tun shekaranjiya da ka iso naga ke ganinka cikin Zurfin Tunani ko Mtsalan wajen aikin naku ne..?
Bayansa yake sosawa kafin yace"Shine Zaki Saki karfin da Allah yayi miki Dake ne..?
Haka ake yi Nenne..?
Kunnensa take neman taja ya matsa yana Dariya yace"Tsaya..Tsaya..Wlh hannunki kamar na maza saboda zafi..Nenne akwai karfi..!
Kinsan mu Jiki mai Laushi Nenne zata yi kisan kai..!
Yana yi yana Dariya itama Dariyan take Farar mace kamar sai itama bata da wani Tsawo kamarsa Suna da Diban kama ta Hasken Fatarsa ba wata babba bace domin Iyakarta wajen Shekaru arba"in da wani abu.
Ganin ya shagala yana Dariya yasa ta Shamacesa ta Murdo Wuyansa yar kara ya saki yana Fadin"Wayyo Allah..Jama"a
Haba Nenne zaki karyamin wuya ne..?
Cikin Fada tace"Kamaidani kakarka ko Aminu..?
Ga Breakfast dinka chan tun dazu har yayi sanyi kana zaunr tunda ka zauna sai faman Tunani kake yi..!
Da sauri yace"To naji Sake ni in miki Bayani..!
Sakinsa tayi kafin ya juyo Kafadanta ya Dafa yana Fadin"To banda abunki Nenne duk duniya wa nake dashi bayan ke..?kece uwata kece Ubana..?kuma kece kakata..Dole nayi wasa dake..!
Mirmishi ta saki kafin taja Hancinsa tana Fadin"Nima bani da kowa sai kai..Kasani ko..?
Yana yar dariya yace"Sai kuma Sabuwar suruka in na kawo miki..!
Baki ta washe gabadaya tana Fadin"Aminu da gaske kake..?
Innalillahi a ina take..?
Ganin yadda ta Rude ne yasa yace mata"Nenne..Haba..Nace in na samo miki Suruka bawai na riga na samu bane..!
Duka taso Dirkamai ya Zura da gudu zuwa Bangaransa yana Dariya itama Dariyan take Lokaci Daya tana Fadin"Zaka zo ka sameni karyan Tsiya kake..!
A tsakiyar kayattacen Dakinsa ya Tsaya Kafafuwansa ya Nitse kan Tattausan Cafet din Daya malale Falon,Hannunsa Duka ya saka saman kansa yana Birkita gashin kan nasa meke Faruwa dashi..?
Yarinya karama taki barin Tunaninsa Tun sanda ya baro Dutse ko da rana Daya bai iya mantawa da ita ba a dukkkan abunda yake yi Tunaninta da yanayinta da mganarta suna Gilmarta ya Dauka da gsske mganarta da Tsiwarta ke Burgesa sai dai yanzu da Lokaci ya tafi abun bai sauya ba.
Duk Yanmata hadaddu Da suke Rubibi akansa bai ga wacce ta kasa barin Tunaninsa ba Irin Amina Yazo Yola gida ne domin ya Huta na kwana Biyu ammh tunda yazo bai da aiki sai Tunani ko yaso ya kaucema abun ya kasa bai kara Tabbatar da ba iya Burgesa yarinyar take yi ba Harda wani abu Dayake jansa wanda bai gama Sanin koma Miye ba.
Abu Daya yana sani zai Nemota kusa dashi Domin ya samu Tabbacin Burgesa take yi ko kuma wani abu ne Dabam wanda baisani ba.
Da wannan Tunanin ya karisa samam makeken Gadon Dake dakin ya Dauko Farar wayarsa Kirar Samsumg.
Nura yaronsa ya Doka ma kira da Sanyin Safiya sai da ma ya Kira ya Duba Lokaci 10:00am na Safe tun jogging din Safe Daya fita ya Dawo ya shiga Dakin Nenne suka gaisa yazo Falo ya zauna ya shiga Tunani Tunanin yarinya karama wacce Bai taba Tsamannin zai taba Haduwa da ita ba.
Sai da yayi ma Nura Kira Biyu sannan ya Daga kiran cikin Alamun barci yace"Oga Lafiya kuwa..?
Karamin Tsaki yaja kafin yace"Bansani ba..Dillah mallam ka wartsake..Wani aiko zan saka ka..!
Da sauri Nura yace"Afuwan Oga ina Sauraranka..!
Sai da ya gyara Tsayuwa kafin yace"Yarinyar da muka Hadu da ita kwanaki..Nake sonkafin nan zuwa Dare im ji komai akanta in nace komai ina Nufin komai..!
Cikin Mamaki Nura Dagachan bangaran yace"Wata yarinya kenan Oga..!
Cikin Bacin rai yace"Bansan yawan Tambaya kasani Nura..!
Shuru yayi mai domin bai gane wata yarinya ba Yanmatan ai suna da yawa ganin yayi shuru yasa yace"Ina yarinyar nan da muka hadu da ita a Dutse..Oh..Ba Dutse ba yama sunan garin da mukaje Shooting din wakar nan Last Month..!
Nura yace"Munje Hadejiya da Gumel sai Jigawa wanne Daga ciki..!
Aminu yace"Inaga Gumel in da muka Tsaya Shago siyan kati har naci karo da wata yarinya wata baka mai ido mai mgana tana da Tsiwa haka..!
Baki Nura ya Hamgame yana jin Ogansa mamaki duk ya cikasa Cikin mamaki yace"Wannan yarinyar Oga..?
Karama ce fa..!
Da sauri yace"Ina Ruwanka..Do as i say..in bazakayi ba zan kira Tt...!
Da Sauri yace"Zan yi..Zan yi..!
Bai jira cewarsa ya Datse kiran yana Fadin"Nura yana da matsala...!
Haka ya fada kafin yayi Cilli da wayar saman gado ya taka cikin Sassarfa ya Shiga Tiolet din Dake Cikin Bedroom din.
Chapter 45 · 0% Book details