Sashe 134
Ta Fita Zakka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Rarrafawa tayi kamar mai koyon Zama saboda ta kasa tashi ta Dage labulen Dakin mamammu na ciki ta gefe kadan so take ta Tabbatar da abunda taji domin gani take yi kamar ba Mamanmu din bace mai irin Muryanta ne sai gashi taga Fuskar mamanmu cikin yanayin da bata taba ganinta ba Tana Tsaye tana waya ta cigaba da mgana cikin Zaro ido tana Fadin"to maza ki kira mallam..Ayi mana mganinta mu koma gefe muna Cin Duniyarmu da tsinke a Matsayin Dayyaba da Madina chan gefe kuma muna Cigaba da yaudaran mutane da Salihan Fuskokin mu na Balaraba da Marliya..!
Bata tsaya ma ta gama ji ba ta juya Cikin Rarrafen har ta fice Daga Falon batare da tayi wani motsi ba Hawaye kuwa kamar an bude Famfo haka wasu ke fita wasu na kara Bulbulowa Idanuwan mamanmu ya rufe shiyasa kwata kwata bata ji wata alaman akwai wani acikin gidan ba.
Amina na fitowa Tsakar gida tayi tayi tatashi sai ta kasa Domin gabadaya jikinta ya Saki Lokaci Daya ta kasa gasgasta abunda taji kuma ta gani Mamanmu kadai kanta ke iya fadi da sunan yaya Anty Amarya bata wani bata mamaki ba jin sunanta Daman ita Tuni Tasan Halinta ammh acikin wannan yanayin ace Mamanmu ce ke da Alhakin Duka abubuwan da suke Faruwa ta yaya zuciya zata iya Daukan wannan Gaskiyan..?
Dakyar ta iya mikewa sai da ta rike Karfen barandan su sannan gabadaya kanta juyamata yake Bata gani Dakyau wani irin Biji Biji take gani Allah ya taimaketa taga Hijabin Haddar Hamida kan igiya data wanke ta Taka Sannu sannu tana Nunfashi Sama sama ta Daukosa ta sakasa ko Takalmi babu a kafarta haka ta Fice Daga gidan Cikin wani yanayi duk Takun da Zatayi sai kalaman mamanmu sun mata amsa kuwwa acikin kunnuwanta Daki Daki Dayasa Cikinta ya Cure waje Daya Dakyar take iya taka kafarta a Haraban gidan taga Jawaad yana kwallo yana ganinta ya nufeta yana Kiran sunanta sai kawai Amina ta kallesa ta kara kallonsa Tabbas sai Allah ya Tsine ma balaraba ko da Hakkin Jawaad aka barta sai Rayuwarta ta D'aida'ice Rumgumesa kawai tana so ta Fashe da kuka ammh ta kasa acikin Kirjinta take jin wani zafi kamar zata mutu batare da tamai mgana ba taja Hannunsa suka fice domin gabadaya gidan ne yayi mata wani zafin Datake jinsa har acikin jikinta suna tafe yana Fadin"Ya Amina ina Takalmin ki. ?
A islamiya an ce mana ba kyau tafiya ba Takalmi..!
Bata ma Sauraransa ita dai kawai Jefa kafa take yi Allah ne ya kaita Falon Hajiya ba Domin tana ganin Hanya Dakyau ba suna shigowa Hamida da Hanne suka Dago suna kallonta gabansu ya fadi ganin Hawaye Kaca kaca a Fuskarta Hannun Jawaad ta Saki ko barayin bata kallah ba Ta nufi Dakin su Hanne tana jin ita da Hamida na Faman kiran sunanta suna tambayanta me ya faru take kuka ko Waigowa batayi ba a yanayin Datake Ciki ba kowa zai iya Fahintarta ta ba Tunda bata da Uwa a raye a Duniya to ta samu kadaicin da zata Zauna Tayi Tunanin makomar ta a wannan Duniyan da Rayuwar data ke cike da Tarin azzalumai maciya amana..!
Tana shiga Dakin ta Ture kofar bata ma iya karisawa Kan gadon ba ta Sulale nan saman Cafet a kofar Dakin Tana Dafe Saitin zuciyarta Daya Dunkule waje daya ga cikinta Daya Cure waje Daya yana murdamata Sosai da sosai Hawaye da majina Har da Miyau haka suke kara kaina akan Fuskar Amina batare data Damu Data Share su ba.
Achan Falo kuwa Hamida ta kalli Jawaad tana fadin"Wai me ya faru ne Amina ta shigo tana kuka..?
Shima ya girgizamata kai kafin yace"Bansani ba nima ina kwallo na ne tazo tana kuka taja Hannuna muka zo nan..!.
Hanne ta mike tana Fadin"Hamida muje mu gani..;
Tare suka Dumguma suka Nufi Dakin suna Tura kofa suka kusa cin karo da Amina atare suka saki Salati Hanne ta Duka gaban Amina tana Fadin"Amina meke Faruwa ne..?
Amina ta runtse ido sai wasu Hawayen ta Dafe saitin zuciyarta Dake mata Zafi bakinta yayi Nauyin da bazata iya mgana ba.
Hamida ta kalli Hanne Cikin wani yanayi kafin tace"Ko zaki je ki kira Hajiya a shashen Baba mallam ne..?
Hanne ta mike tana mai yarda da mganar Hamida da Sauri Amina ta Rike kasan Sikat dinta bata so ta Kira Hajiya domin in tazo bata san me Zata Fada mata ba, ta tabbata ita kanta ba Domin taji ta gani ba ko Duniya Zasu Taru su fadamata Bakaken Halayyar mamanmu bazata taba yarda ba shiyasa ta Dago Jajayen idanuwanta Dakyar tace"Kada ki kirata..!
Hanne tace"To kuma kina ta kuka..!
Amina ta Runtse ido kafin tace"Ba..bani da lafiya ne..!
Hamida tace"Kan ki ke ciwo..?
Daman tasan Amina da Raki ciwo kadan sai ta Fara kuka da Sauri Ta gyada kanta Hanne tace"To ki tashi kici abinci ki sha mgani sai ki kwanta..!.
Saboda su kyaleta yasa tace musu tasha mgani agida Muryanta a Dakushe Hamida ne tace Hanne ta Taya ta su taimaka ma Amina ta koma kan gado tunda bata da Lafiya haka suka taimaka mata ta hau kan gado ta Dunkule ta Runte ido kamar mai barci har Hamida ta Lallube kafarta da Bargo suka fice bayan sun turo mata Kofar sai da suka fita ta Bude idanuwanta Allah Sarki Hamida mai kyakyawan zuciya tunda Take da Hamida bata taba ganin wani sharrinta ba sai Alheri ya zata ji in ta ji Halin Mahaifiyarta..?
Kai Innalillahi Yaya ashe ashe kasheta sukayi Shiyasa ta kwanta Lafiya lau sai gawanta aka gani shin me yaya ta Tsare ma Mamanmu..?
Ta bar mata ragamar gidanta ta bar mata Ragamar duka ya"yan data Haifa ace ko don haka mamanmu bazata Raga mata ba..?
Tunda take bata taba ganin Aba yayi bambamci tsakanin Mamanmu da Yaya ba har tana Kwatantashi Cikin masu adalci Tsakanin matansa.
Ashe ashe alheri yana komawa Sharri ashe ashe haka Duniya ta gada..!
Sai yanzu ta Fahimci Bakin Zaren Ta Dade tana Tunanin da wa Anty Amarya take waya kwanaki tana ambaton sunanta da kokarin Hanata Tarewa a gidan ya Danmalam sai yau Sirrin Boye ya fito Filo ashe mamanmu da Anty Amarya Bakin su Daya..?
Ita tanayin komai Saboda Aba ne ita kuma Anty Amarya saboda Sakina ne..? Ita fa Haj.uwa dataji suna ambatkn sunanta ita me ta ke aikatawa..?! Sannan domin wa take yin abunda take yi har suke Tunanin in zata basu matsala su kawar da ita..?
Lalle Duniya ba abun yarda bace abunda ko a mafarki ko Finfinan India dana Hausa bata jiba ai ko a karance karancen datake yi bata taba Haduwa da makirci da mugunta irin wannan ba Shekaru Goma sha Shidda Mamanmu ta kwashe tana kassara Rayuwarta ko da da rana Daya bata taba bari ta rabu da Yaya tasan Dadi da Martaban uwa ba shekaru sha Shidda ta kwashe tana Gurgunta Rayuwarta sai alokacin abubuwa suka Dawo mata Daki Daki Tun Farko kovsau Daya mamanmu bata taba Zaunar da ita tayi mata Fada kan wani abu ba sai dai ta rika Fadin yarintace in ta girma Zata Daina Ammh ai Hamida bata mata Haka bama ita ba kaf ya"yanta tana Dorasu kan Hanyar mai kyau tun daga bangaran Tarbiya har bangaran Ayyukan gida da Sauraran abubuwa ashe da gangan ta Sangartata ta Shagwabata Duk cikin Lalata Rayuwarta ne bata sani ba Kaiconta ashe ashe duk wasu abubuwan datake yi ba yin kanta bane tasan wasu abubuwan na tadda Hali ammh wannan Rashin Tsoron da Zafin Zuciyar duk ba nata bane Mamanmu ne taso ta kassara Rayuwar ya Jafar sai abun ya Tsaya akanta ta Godema Allah da abun ya Tsaya kanta Domin daman karamin alhakin daka raina Watarana shi zai tsole maka ido.
Tafara Tunanin yadda ta rika turata sai taje ta ce ma Hajiya ko mallam bazata tare ba batasan Dannallam sai yanzu ta Fahimci komai wato tana Taya Anty Amarya ne kamar yadda ta Taimaka mata ta kashe musu uwa anya Balaraba zata ga Annabi kuwa..?
Idan ta Mutu kila kasa bazata taba karbanta ba ashe ashe bata son tarewarta da ya Danmallan ta Tabbata Auran ma Allah ne yaso da bazasu taba bari ba ta Tuna sanda take tusa mata ra"ayin tace ya saketa Tsoho ne bai dace da ita ba ta tuna yadda take Zaunar da ita tana Dukan ruwan cikinta in taje gidan Danmallan tayi Weekend ta Dawo tasha Turketa ta Tambayeta ko suna waya sai tace mata A"a data ga kuma kamar abun yayi musu yadda suke so ne ta fita Sabgarta ashe Duniyar ce ta Fara Samuwa ba shakka Taga Aba ya Rage damuwa da wasu al"muran sannan ko Jawad sai ya kwana wajen su a ashashen Hajiya Aba bai Damu ba abaya kuwa yana Dawowa sai ya nemi Jawaad inda ya Saka kafa nan yake sakawa shima sai da Mamanmu ta rabasu taji Dadi ashe ashe Sihiri ne ajikinta shiyasa take Fama da Zafin zuciya bata sani ba..!
Sai ta Tuna Aminu sanda yake Fadamata watarana ga Mamanmu din ammh har Abada bazata Shafe mata matsayin UWA BA..ta yarda kuma ta amince a wannan Ranar kewar Uwa ne ya Taso mata da tana Raye da a kan kafadarta zata kwanta tayi wannan kukan ammh ina Duk da Lokacinta ne yayi domin mamanmu bata isa ta yi Ajalin yaya ba tunda ita ba Allah bace ta sani Daman chan kwanakin da suka Rage mata a Duniya kenan