Sashe 32
Ta Fita Zakka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Lallabawa sukayi suka shige Dakin da suke kwana suna jin Hayaniyar su ya Jaleela a chan Tsakar gida,da kuma Hayaniyar Mutane,Har alokacin suna Tsakar gidan suna kamallah aikin su. Suna shiga Dakin Zafira ta yaye Hijabin Jikinta ta zauna Dabas kan Cafet din Dake Dakin ta Dago tana kallon Amina Dake Tsaye kyam takaicinta Daya yadda Ya Uzairu ya karbi Namanta bai bata ba Shi yafi kona mata zuciya ba Dukan Ya Nasir ba. Zafira tace"Amina ke kam baki jin Duka ne..? Amina ta wani kalleta a kaikace kafin tace"Me kika gani..? Zafira tace"Gani nayi kina Tsaye sai Dukanki ake yi ko kiyi Tunanin Guduwa ma ballatana ki bada Hakuri..! Hameda da gajiya yasa har ta kishingida tace"Tab Aminan ne zata bada Hakuri..!ai mutun Daya Amina na taba ganin ta bama Hakuri..! Hanne na gefen ta ta karbe da Fadim"Yaya..Yaya ce kadai Amina ke bama Hakuri bayan ita ko Aba Tsayen nan take mai .Zuciyarta kamar ta Kafuran Farko..! Zafira ta jinjina kai kafin tace"Tabdijam Haka kurum na zauna ayi ta Jigana kamar wata Jaka..! Amina ta Daga idonta Sama kafin tace"Duka ai baya kisa..Daya na kisa da Tuni ba Sauran Amina Zafira..Sannan mganar na bada Hakuri ma bai taso ba..Me nayi..?Amina bata bada Hakuri matukar tasan ita keda gaskiya..! Zafira tace"Uhmm..Ko dai aljanu gareki. ?su suke saka ki wannan Taurin kan Amina..? Amina ta mata kallon Tara sau ra kwata kafin tace"Sai dai in naki ne suka Dawo kaina yanzu .! Da Sauri Zafira tace"Ni bani da Aljanu..! Amina ta tari numfashinta tana Fadin"Nima haka..! Daga haka ta samu chan Lungu Bayan ta Nanannde Hijabin jikinta tayi matashi Dakin ba Katifa Cafet ne kawai sai tarkacen kayansu da suka Kwaso zuwa nan baya ta juya musu aranta Allah yasa kawai take antayama Ya Nasir da ya uzairu kafin ta Muskuta tana Fadin"Ai shima ba Zubar da naman zai yi ba ci zai yi..Wlh In na yafe Allah Tsinan..! Suna jinta ba wanda ya tanka mata suna Hiransu sama sama Tsakaninsu Amina ko kala bata kara cewa tun tana jinsu sama sama,Har sanda Hanne tace"Naga fa ga Ya Danmalam Dazu da su ya Nasir suka Turlemu..! Hamida tace"Nima na gansa ammh bai yi mgana ba..! Hanne tace"Baida Hayaniya ne..duk acikin Yan gidanmu yafi burgeni..! Hamida tace"Gaskiya..! Amina na jinsu batace komai ba Domin kwarjinsa ma ya isa yasa kakasa mai gaddama Dole ace baida Hayajiya. Har barci ya kwasheta ba ita ta farka ba sai da taji an Fara sallah Cikin Wata Zakkan murya cikin Sanyi da Haiba Muryan Ya Danmallam ne tunda ya Dawo Duka Khansin Salawatun shi ke badawa ko da tatashi ta iske Hamida da Hanne na Sallah har da wasu ma yab gusai adakin suna Bin Jam'i. Tashi tayi ta fice Suka kusa cin karo da Zafira ta Dauro alwala Daga cikin Gida. Kallonta Amina tayi kafin tace"Meyasa baku tasheni ba..? Zafira tace"Hamida ta gaji da tadake kin ki tashi..! Wucewa tayi tana Fadin"Bansan munafunci barcin mutuwa nayi da har aka tanadi naki tashi..!? Zafira dai bata tankata ba ta shige Dakin ta tada Sallar Amina Raka"a ta Samu Allah yasa ma a Rak"ar farko Suratul Muhammad ya karanta ita kanta yana karatun acikin Zuciyarta wani natsuwa take samu wanda ta rasa Dalili ammh aranta take fadin Muryansa nada Dadi in yana karatu. Suna Idar da Salla Mamanmu ta shigo Dakinsu suka Taru wajen gaisheta Hamida ta kallah tana Fadin"Hamida ku tsefe kanku na Roki Wasila zata yi muki Kitso da kunshi kafin Lokacin Walima..! Hannatu kema ki tsefe Tunda nasan kema baki Kitson ba..! Cikin Fara"a suka amsa mata Hanne ke fadin"Mamanmu irin kunshin Zafira za"amin..! Tafada tana nuna mata Kunshi naSalatif ne mai gidan siga Mamanmu tace"Ba matsala sai tayi miki..Jiya Da Daddare ya kamata ayi muku..Nayi ta Cigiyarku baku dawo ba kuna gidan Baba Mallam..! Amina taso na Tsefe miki kan na wanke da ke Wasila zata fara ta yar fa miki iri iri mai kyau..! Ba musu Amina ta Mike tana Sosa kanta kafin tace"Mamanmu da kin barni..Ban yi niyyar kitson nan ba .! Mamanmu tace"A"a Amina kan ya Dade ba..yafi wata biyu tun Wanda nayi miki din nan ne fa..?ki bari a Tsefe a sake wani..! Amina ta make kafada kafin tace"Ammh bazan yi Kunshi ba..Bana son zama Mamanmu..! Kallonta tayi ta Tube Dankwalin Dake kan Amina tana Fadin"Bakomai kiyi kitson kawai..! Mamata Mahaifiyar Zafira Dake Dakin Tace"Balaraba gaskiyan Ya Sa"idu ne dayace kike kara bata Amina..Ammh wannan Katuwar Budurwan da yau ko gobe Gidan miji ne kike lallabata Ta gyara kanta..?bayan ke zaki mata Tsifan ki kuma wanke mata..?Anya Balaraba..! Mamanmu tace"Amina fa yarinya ce..?nawa take..?in Lokacin ta fara gyara kanta yayi zata gyara Mamata..! Mamata ta tabe baki kafin tace"Ai shikenan..adai taimaka ayi kunshi ta Rufe wannan Farar kafar kamar ta kato..! Amina ta Tura baki hararan Mamata kawai take ta gefen ido Tana ganinta tace"Hararata kike ko..?na tashi na Gafjeki Wlh..,! Amina ta kauda kai tana kunkuni Mamanmu taja hannunta suka Fice tana fadin"Don Allah ku kyalemin Diyata hakanan kada kambun baka ya kamamin ita..! Da kallo suka bita har ta Fice Da Amina wacce ta Juyo tana musu gwalo.. Zafira tace"Wai Amina sai an mata Tsifa an wanke mata kai..? Hamida tace"Ko kayanta bata wankewa sai Uniform Duka mamanmu ke mata ko ta sakani..In ba ita ta mata tsifa ta mata Kitso ba sai Kanta ya shekara bata Damu ba..! Mamata tace"Kuma wamman ba so bane..Watarana ake ji ranar da zata gidan kanta sai ta gane bata da wayau..Irun su Amina kazaman mata za"ayi in an hadu da kishiya kuma ta ran mata ta zama Bora..! Hanne tayi dariya kafin tace"Waya ga Amina tayi aure..!ina so naga mijinta yadda zasu zauna ballatana Har da Kishiya..!tabdijam..! Hamida tace"Zasu ga Tijara ne da Jidali ganin idonsu..! Mamata tace"Ubanta zata ci..Daman na Fadama Ya Sa"idu ya mata aure. tsab zata Saitu don Ubanta ai chan ba Balarabar da zata kare mata..! Dariya suka saka Zafira na Fadin"Nima ina son ganin zaman auran Amina akwai Comdy..! Dariya suka kara sawa har da Tafawa chan ma Tsakar gidan haka mutanen Gusai suka taso ma Mamanmi ganin ta Tasa Amina tana Tsefe mata kai. Fadi suke"Balaraba kina sangarta Amina..?Tsifan ma sai anyi mata..? Ita dai Fadi take"Eh mana..Nawar Aminar take?Sai fa wannan shekaran ne zasu shiga Sha shidda ita da Hamida..? Yaya na jinsu ko tankasu batayi ba suna chan suna Hidiman yin waina da Za"a rabawajen Walima su ya Jawahir kuma suna Daki suna Tsara Memo da Turaran wutan tsinken da Zulaihat zata raba wajen Walima. Ya Jaleela dai sai ta fito tayi mgana bayan ta kalli kan Aminar tace"Amina wlh ba karamar kazama za"ayi ba Watarana..kanta har Tsakan kitso ya bace..?in taje gidan auran naga Uban da zai rika zama yana mata Tsifan..! Ya zulfa tace"Kila mijin zai rika zama yana Tsefe mata..! Wata daga cikin kannen Aba Daga Gusai Talatu tace"Sai dai taci Ubanta..aai nan ba gida bane..!na jaki zata ci barin ma mazaj wannan zamanin..! Dariya suka saka Amina ta tura baki Tana Fadin"Kina jinsu ko mamanmu..? Wai har fata suke nayi aure mijina ya Dake ne..! Mamanmu tace"Kyalesu..Zulfa Jaleela zan saba muku..Ba ruwanku da Diyata..! Basu kara mgana ba ganin Mamanmu ta Hade rai ba wanda ya kara tankawa har ta gama mata Tsifan wajen taje kan Amina sai Wash Wash take Ya Jadwa ta fito Daga Daki tana kallonta kafin tace"Kai Amina kin ji Haushi Wlh..! Mamanmu tace"Jadwa..Zan saba miki Wlh..! Jadwa ta juya tana Fadin"Nayi shuru mamanmu..! Amina aranta fadi take"Bana ga jin haushi ba Ehe..! Dakyar ta bari aka gama Taje kan mamanmu ta Debo ruwan zafi ta fara wanke mata kan wajen Famfo Amina Har Hawayenta Wai Zafi take ji mamanmu na Faman Lallashinta Su Jaleela na kallonsu Tsausayama Aminan sukeyi ko domin gaba Watarana ba Mamanmu a kusa da ita. Tana gama wanke mata yasha Iska ta Shafa mata mai kitso ta kara Sharce mata taja hannunta suka koma Dakin da Wasila ke ma su Hamida kitson. Har ta kusa gama ma Hanne daman kanta a Tsefe yake Mamanmu ta kalli Wasila tana Fadin"Da kin gama ma Hanne ki fara ma Amina Wasila..! Wasila tace"Dole zan yi ma Amina kitsin nan..Kada ki kullaceni Balaraba..! Mamanmu ta fice tana Fadin"Tunda bata som kunshi a kyaleta..! To daman waZai matsa mata Ana gamama Hanne aka fara ma Amina Wasila tace"Wani iri zan miki..! Amina tace"Chiku..Guda goma..! Wasila tace"Daman bai wuce haka..In akayi miki mai yawa ina zaki iya Tsefesa bakar kazama..! Amina ta Juya idanuwanta kafin tace"Nifa ba kazama bace..! Wasila ta Dungurr mata kai Tana Fadin"Rashin kunya Kadai kika iya ni gyara kafin na fasa yi miki kitson wlh..! Amina bata kara mgana ba tana kalloj su Hamida na kuskus Amina ta Daga baki Tana Fadin"In aan ci namata Allah ya isa Wuta bal bal..! Suka kwashe mata Dariya Amina tayi kyafci Tana Fadin"Munafunci dai Dodo ne..! Suka kara saka mata Dariya Sai suka kara kunnata ta rika Hararansu Wasila ta gaji da motsinta tace"Zaki Taaya ko kuwa na saki kan naki ne na kama na Hamida..! Amina batace komai ba aranta Fadi take"Yadda kike baka a fuska har aranki ma haka mata sai Masifar Tsiya..! Dakyar aka samu aka gama ma Amina Kitso kafin Lokacin Zafira da Hanne sunyi wanka har zafira taje raka Hanne gida ta Dauko kaya Hamida aka Fara mawa itama ita kuma Amima taje tayi wanka duk wanda yayi mata mgana sai ta Turamai baki tana kunkuni ta Zagesa shiyasa ma su Ya Jaleela suka yi kamar basu ganta ba Mamanmu ce sai yaba Kitson take tana Faman fadin sai tayi ma Wasila kyauta. Amina koda ta fito wanka ta Iske Sabbin kaya Atamfa Hajiya Babba ta Dinka musu su uku ita da Hanne da Hamida da Dogayen Hijaban angon Walima da su ya Zulaihat sukayi. Amina ta Daka tsalle Saboda Murna Tana Fadin"Jar uba..Yau din ba wanda zai fimu na Rantse..! Hanne tace"iri daya da nasu ya Abida Hajiya ta mana fa..? Amina ta sha Dariya kafin tace"Su ya Abida yau kuma za"a sa anko da yara..! Dariya suka dinga yi sai da suka jira an gama ma Hamida kitso kana suka karya da kunu da kosai da waina basu kayan ba Saboda su Hanne zasu kunshi Amina