← Book details Ta Fita Zakka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 56 OF 193

Sashe 56

Ta Fita Zakka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gabadaya jikin Aba rawa yake saboda Bacin rai idanuwansa sun rufe jijiyoyin kansa sun mike cikin Tsananin Fushin da ko su yaya sun Dade basu gani ba ya Nuna Mamanmu da wayar hannunsa yana fadin"Wayar waye wannan..? Nace wayar waye wannan Balaraba..? Ya karishe fada cikin Tsawa Lokaci daya yana sakar mata jajayen idanuwansa da suka sauya Launi Saboda bacin rai. Awannan gabar kowa bai da bakin mgana Yaya bazata kare Amina ba Daman Hamida da Zeenatu bazasu iya cewa komai ba Mamanmu ce Daman ke da wannan ikon itama ta rasa mafita Domin Amina ta bata komai wannan kiran wayar da kalaman Aminu ya gama tabbatar da cewa Amina ta aikata abunda ya Fada din. Amina kuwa jikin Mamanmu ta shige jikinta ba inda bai rawa shikenan ta gama wayo wannan Ranar daman take tsoro gashi tazo ta sameta bata shirya ba. Aba baya duka sai dai Fada baya Hukunci da kansa sai dai su ya Jafar ammh duk ranar da ka shiga hannunsa sunanka Sorry bai iya Duka ba in ya fara bai iya bari ba,Shiyasa wani Lokacin baya son bacin ransa kuma baya son yayi duka. Tasani komai ya gama baci bata kuma da kalmar da zata kare kanta ballatana Har Mamanmu ta samu kwarin gwiwar kareta kamar yadda ta saba. Aba ganin mamanmu tayi shuru ta kasa mgana sai kuka take taya Amina yasa yayi mirmishin Saman baki Mirmishin Dayafi kuka ciwo yace"Balaraba mgana nakemiki..? Nace wayar da Amina ke amfani da ita wayar waye..? Mamanmu ta Dago cikin wani yanayi kafin tace"Wayata ce..,ammh wlh..! Bai bari ta karisa ba ya Daga mata Hannu Cikin wani yanayi muryansa ta Cunkushe waje Daya yace"Basai kin ce komai ba Balaraba..Na Fahimci komai..Duk Abunda Amina ta aikata ko take aikatawa da saninki da kuma Daurin gindinki Balaraba..! Mamanmu ta Kallesa cikin wani yanayi haka ma Yaya bata samun Zarafin mgana ba ya cigaba da Fadin"Eh da saninki mana..in baki sani ba Meyasa kike barinta da wayar..?ai na Fada muku ku daina bari suna Daukan wayoyinku saboda gudun irin wannan ko ban fada ba..?ammh baki ji ba..Komai Amina zatayi mai ko mara kyau Daidai awajenki Balaraba baki Taba nuna mata Tayi ba Daidai ba wannan ne so..?wannan ba So bane Balaraba..Kuma kin Cuceni kin Latatamin Tarbiyan da nayi shekaru ina ginata kan ya"yana bazan yafe miki ba..! Yake fada cikin wani yanayi muryansa kamar ya yi kuka,Yaya mamaki yasa tama kasa mgana ballatana Mamanmu data kafe Aba da ido zuciyarta na suya mamakin kalamansa ya kamata. Amina kuwa rudewa tayi da kalaman Aba da sauri ta mike daga jikin Mamanmu ta rarrafa gaban Aba cikin kuka take fadin"Aba Wlh Mamanmu bata sani ba..Bata sani ba..! Kafa yasa ya Shureta in ya kalleta ransa har wani kara baci yake,Dukewa tayi awajen tana kuka cikin Fusata yace"Karya kike ta sani..Tasan komai akanki..Balaraba tasan komai akanki Amina..Hadizam haihuwanki kadai tayi ammh Matsayin Uwa balarabace gareki baki yarda da kowa ba sai ita..Abun bakikciki ace kamarni acikin gida na samu mai Bijirema Umarni na..SAnnan Tsorona Daya tun yaushe kika fara haka Amina..? Na Dade ina addu"am kada watarana ki Zama Zakkan da mutame ke Fada sai gashi Tun ba"a je ko"ina ba Abunda nake tsoro ya faru....! Yake fada cikin bacin rai kafim Lokaci Daya ya Dago Amina wuyanta ya Shake Cikin Zare mata ido yana Fadin"Ban yarda Dake ba Amina..Dom Ubanki ki Fadamin saunawa kika yarda yayi Lalata Dake..? Ki Fadamin yaushe kika san maza haka ban sani ba Amina Duk kafa kafan da ni da Baba Mallam muke yi a kanku..? Ki fadamin nace kafin raina ya baci na Shake ki mutu na huta..! Zuwa Lokacin Amina ta fara kokuwa da Numfashinta Yaya bazata ce komai ba Tana baya hankalinta atsshe Hamida da Zeenatu kuka Mamanmu kuma kalaman Aba sun gama kashe mata jiki ganin Amina ta kusa Mutuwa ne kada ayi kisam kai yasa Mamammu ta mike da Sauri ta isa garesa tana kokarin bambare hannunsa a wuyan Amina Lokaci Daya tana Fadin"Haba Abansu zakayi kisa ne..? Kalli fa zaka kasheta Amina bata Numfashi..? Take fada Cikim kuka Hannu yasa ya Tureta da karfi da sai da ta Fadi kuginta ya Bugu wani kara ta saki da yasa Yaya dasu Hamida sukayi kanta da yatsa ya nunata yana Fadin"Kada ki kara sakamin baki in ina ma ya"yana Hukunci balaraba..Domin ke ba Matata bace Yanzu NA SAKEKI Saki Daya..Tunda na Fahimci kin bada gudummuwa a Lalatamin tarbiyar Amina..! Ya fada Cikin bayyana bacin ransa Ba su Hamida Dake rike da Mamanmu ba Hatta Amina Dake kokuwa da Numfashunta sai da kalaman Aba suka Girgizata ta zaro ido tana kallon Aba Cikin Firgita da rawan baki Hamida hanmu ta Dora akai Zeenatu kuwa hanmun Yaya ta kamkame tana kuka wacce ta saki Mamanmu kamar bata laka ta koma ta zauna Dabas kanta na juyamata ji take kamar amafarki komai ke faruwa Cikin Muryan da basu taba sanin Yaya tana dashi ba ta Kira Aba Cikin Tsawa"SA'AIDU..Me ka aikata haka..? In har baka gode mata kan Amina ba bazaka zageta ba..Kayi kuskure kayi kuakure Sa"idu kayi saurin gyarashi kafin Lokaci ya kure..! Kallonta yake yi bai yi Nadama yace"Kema Kada ki kara sakamin baki..In kuma ba Haka sai ranki ya baci..! Yaya sai hawaye Amina ta zama bala'i tayi sanadin mutuwar auran matar da ta zama bango gareta Kallon Amina kawai take ta Durkushr tana wani kuka kukam Nadama da bakin ciki acikin Ranta Tana Tunanin Dama ace .Dama ace bata Hadu da Aminu ba Dama ace bata yarda dashi ba..Da duk haka bata faru ba me ta aikata..? Ta kashe auran Matar da ko Uwar data Haifeta bata kaita sonta ba Matar data kasance wata aba mai Daraja a wajenta ita kam Amina wannan Ranar bakar Ranace a wajenta soyayya bata mata adalci ba ta Datse mata komai alokacin da bata tsammaci Lalacewar abubuwa kamar yadda suke Faruwa. Kuka take kamar ranta zai fita ta Rararrafa ta kama Kafan Aba cikin kuka take fadin"Don Allah kayi hakuri..naji ni ka Hukuntani kayi ta Dukana har sai na Daina Numfashi ammh kada ka saki Mamanmu Na Rantse da wanda Raina ke hannunsa Mamanmu bata sam komai ba Wlh bata sani ba! Take fada tana kuka wannan karon ba Aba bane ya Tureta Yaya ce Lokaci Daya ta shiga Dima ta Dundu kota ko"ina Bataji bata gani tana kuka Tana Fadin"Kin yi asara Amina..Kin yi asara Tunda rashin jinki yasa,kikayi Sanadiyar Mutuwar auram matar da bata barinki ke kadai ba akowani Hadi Tana Tare Dake..Kin Fita Zakka Amin Da gaskr ne ke Zakka ce..Tunda kika Rama Alheri da Sharri..Ki kuma yi Sanadiyar Mutuwar auran da yi Shekaru na rasa da wani suna Zan kiraki ji nake in na barki da Raina bam Huce ba..! Kowa ya kasa hanata Yaya bada wasa take dukam Amina ba Fadi take"Abun kunya zaki jawo musu Amina..? Su kike ki kasheta ki huta..? domin ita kadai ke Daukema Jidalinki Amina kin fara bin maza? Aure kike so baki fada anyi miki ba.? Gwara na fara kasheki na Huta kafin ki zo ki Kashe sauran Rayuwan da suke kare miki..! Dukanta take yi kamar bata cikin Hayyacinta Amina na kuka bakimta na Zubar da jini take fadin"Wlh yaya bana bin maza Wlh ni ba yar iska bace..! Bakinta bai mutu ba..Daman bazai taba Mutuwa ba yau da Mamanmu zata Ceceta bata ceceta ba tana gefe har alokacin Shock din Daya kamata bai saketa ba sannan ko tana son tashu ta kasa kugunta ya Bugu da Gadon Hamida ta kasa tashi Kuka take daga Zaune ba kukan kalaman Sa"idu kukan yadda Amina ke kuka Yaya na Dukamta Cikin karyewan Murya tace"Yaya ki daina dukan ta don Allah..Ki bari raina na kuna..! Yaya ta Dago idonta jajir tana Fadin"Yau dai..Yau dai Kadai ki bari na Shiga Lamarin yarinyar..Ki barni na yau kadai! Mamanmu sai ta kasa mgana Ya Zeenatu ne taga Abun ya rikice Aba na Tsaye bai yi mgana ba Shima baya son ya kara saka mata hannu ne ssi ya Illlata,Rugawa tayi ta Fice Daga Dakin ba Mayafi ba Takalmi ta nufi waje ita ta Bude gida sai gidam Baba Malam an Rufe get haka ta Dinga Bugawa da karfi megadi yana Lekowa ya ganta ya Bude Mata da Sauri yana Tambayanta ko Lafiya ina bata Tsaya Sauraransa ba da Farko Cikin Gida ta so ta wuce sai taga Falon Baba Mallam abude ssi ta kwashi gudu zuwa chan. Yana Tsaye gaban makeken Dirowan Dake falonsa mai shake da Littafai da Farin Gilashinsa da Jallabiya yana Duba wani littafi ne samda Zeenatu ta Fado kamar an korota tana Haki Sama Sama Hakinta yaji da Numfashinta yasa ya Juyo da sauri ganinta Cikin wannnan yanayin yasa Hankalinsa ya tashi da sauri ya baro inda yake Tsaye ya kariso gabanta Cikin Dattakonsa yace"Zeenatu meke farruwa ne..? Ganin yadda ta Duke ne tana kuka Jikinta ba inda baya rawa yasa yace da Sauri"Kada kicemin wani abu ne Mummuna ya samu Sa"idu bayan yanzu bada Dadewa ba yabar nan wajen..! Zeenatu na kuka Dakyar ta iya cewa"Aba..Ya saki mamanmu..Sannan ga yaya chan na Dukan Amina..Baba mallam kazo kafin su yi kisan kai..! Hankalinsa nan da nan ya tashi Cikin wani yanayi ya shiga maimaita"Innalillahi wani"inna ilaihirraju"un..! Muje gidan muje..! Yake fada yana karisa wajen Daya Ijiye wayarsa ya Daukota yabi bayan Zeenatu data Fice da Sauri Lambar Hajiya Babba ya Kira bai rude ba sosai Saboda yana ta Kiran sunan Allah.. Itama ta tsorata data ga Kiran nasa Domin bata Dade da komawa Shashen nata ba ba ita keda dashi ba Hajiya Nasara ce,Cikin Wani yanayi ta Daga Wayar tana Fadin"Mallam lafiya dai ko..? Cikin Dattakonsa yace"Ki sako mayafinki ki Sameni gidam Sa"idu..! Zumbur ta mike daga kwancen Datake tana Fadin"Innalillahi me ya Faru ne Mallam? Cikin Natsuwarsa yace"Bansani ba..Sai mun je zamu ji..Ki yi Sauri..! Daga haka ya Datse kiran cikin Sassafa ya Fice Daga falon bayan ya saka wayar tasa aljihu Tuni Zeenatu ta fice Daga gidan megadi ganin Mallam ya fito da kansa yasan ba Lafiya bai Tsaya tambayansa ba ya shuga mai Fatan Dawowa lafiya Gudu gudu sauri sauri Baba Mallam ya isa gidan su Amina kamar zai fadi Saboda Damuwa zeenatu na shiga Dakin ya shiga Saboda ya Jiyo kuka da
Chapter 56 · 0% Book details