← Book details Ta Fita Zakka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 193

Sashe 47

Ta Fita Zakka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Wlh in na yarda Allah Tsinan..Kin manta jiya ma da muka dawo agidanku na sauka keman yau namu zaki sauka yarinya..!
Amina ta fada tana Faman Jam hijabin Hanne Hamida na gefe tana musu Dariya dukkansu kayan makaramta ne ajikinsu da Uban jakunkuna Hanne Fadi take"Sakeni Amina..Nace ne bazani ba..?
Amina tace"In sake ki ki shige gida..?naki wayon..?Hamida karbe jakarta..?
Hamida ta warce Jakar makarantar Hanne Tana Dariya ya Zeenati tazo shigewa gida da Katuwar jakarta Sabe a Hannu ta bisu da kallo kafin ta Tabe baki tana Fadin"Miye haka..?
Kudai bazaku bar yarinta ba..Kuna girma kullim kuna cin kasa..!
Baki Amina Ta tura batayi mgana ba Hamida ce tace"Ba ruwana Amina ce..!
Karamin Tsaki taja ta shige gida Abunta ya Abida ce Daga nesa ta hangosu kusan itace Karshen sauka Daga Motar,yau a waje idi ya ssukesu motar ba Lafiya Dakyar ta kawo su gida gareji yace zai kaita shiyasa ya Saukesu anam waje su Sa"adatu tuni sun shige gida abunsu su Ya Akilu ne ke wajen jikin Motan.
Abida ta kalli Zubairu tana Fadin"Kalli yaran chan..?
Akilu yace"Bari na Tarkatasu su shige gida..!
Yafada yana Daukan Sanda ya fara Tafiya yana Fadin"Ya shamsu..Eh gasu nan suna wasan banza a waje..!
Kamar sun ga Shamsu da gaske suka Zura aguje su kuma suka kwashe musu Dadariya Abida ta shige get din gidansu ita da Zubairu Akilu yabi bayansu su Amina suka Tsaya suna maida Numfashi Amina tace"Wlh Ya Akilun mugun dan saka ido ne..!
Hamida tace"So yake ya zama makwafin ya shamsu tunda shi ya gama..!
Akwai son yayi Displine..!
Amina tace"Barni dashi Watarana zamu mganinsa ne..!
Hanne tace"Badai kara kara zaki sakamai ba irin na ya Shamsu..!?
Atare suka Saka Dariya Tun abunda ya Faru wanchan satin Amina ta samo kaikayi a makarantar Islamiyansu taji su mariya na Fadin abun na saka kaikayi ta tsinko ta Dinga tusama Mutane Cikin Hijabi a ajinsu suna ta Soshe soshe,Shine ta sakama Shamsu Saboda ya Rankwashesu ita da Hanne basu gama Rubutu da wuri ba har aka tashu sun bata musu Lokaci shine suka Fakaocesa da Daddare Amina taja Hanne sukaje suka Watsamai akan Katifarsa da Safe suna Daki sukaji Hajiya na Fadin shamsu wani abu ya Sameshi jiya da Daddare kwana yayi susa da wanka sai da mallam ya dinga mai addu"a.
Sai da Amina ta kwanta Saboda Dariya Hamida ma bata sani ba Labari Hanne ta bata.
Amina na Dariya tace"Ai mallam Auwal ya saka an sare Ganyen mai kaikayin..!
Hamida tace"Ina Fatan kada ya Shamsu yaji Wlh sai na Lahira yafiki jin Dadin Amina..!
Hararanta Amina tayi kafin tace"To in ma yaji wlh ke kika fada!
Hamida tace"Ni kuma..?
Amina ta Bude baki zatayi mgana keman Idonta ya Fada kansa yana Tsaye Daga Kofar gidansu bai yadda sun kariso da Motarsu ba Tana baya Nura ke ciki yana kallon Ikon Allah
Sun fi awa Daya suna wajem ne agaban idonsu Motan makaranta tazo ta Sauke su Amina suka Firfito.
Ko alama bata manta dashi ba gani su Hamida sukayi hankalinta ya koma Chan gabansu yasa suka juya suna kallonsa yana Tsaye sanye Cikin Riga da wamdo bakake sai ya Dora Farar Jaket ya saka F.cap ya Rufe Fuskarsa sai dai ya Janyeta kadan.
Amina cikin mamaki tace"Laaa..Kai ne..!?
Mirmishi ya sakar mata kafin yace"Nine..Amina kina Burgeni..!
Fadin haka da yayi yasa ta washe baki ta fara takawa gabansa shima ya tako suka Tsaya daidai kofar gidamsu Amina Hamida da Hanne suka saki baki suna kallonsu.
Amina Hannu ta Fara tafawa tana Fadin"Kai..Daman ina neman ka..?Ashe kai mawaki ne bansani ba..?
Ido ya zaro yana kallonta kafin yace"A ina kikaji..!
Kai Tsaye Amina tace"A wayar wata ajinmi mana..naji suna mgana suka ambaci mai irin sunanka nace anunamin Hotonka kuma Wlh kai ne..Yauwa daman ina ta so na Fada ma su hanne don Allah ba kai kace ina Burgeka ba..!
Kallonta kawai yake yi yanjin wani Farinciki sai da ya ganta ya kara ganin yarintarta tana mgana ko Tsayawa ta kasa yi.
Kai ya gyada mata yana kallonta juyawa tayi ta riko hannun Hanne da Hamida ta kawo gabanshi tana Fadin"Yauwa don Allah sake fada musu..Kila su yarda..!
Tafada tana wani juya ido Dariya abun ya basa cikin gyara Tsayuwarsa yace"Amina Kina Burgeki..?Wani ya Taba Fada miki u arr so Beatufull..!
Amina taji wani Sanyi acikin ranta Cikin Alhafari ta kalli su Hanne da mamaki ya sa suka kasa mgana tace"Kun ji ko..?ai in na Fada muku sai kuce Karya nake..Nima fa ina Burge mutane
Kunga wannan babban mawaki ne.yana tare dasu Umar.m sharif..?
Dasu Ani nihu kasan su ko kilma abokan ka ne..?
Take Fada tana kallonsa Cikin Dariyarta Kai ya gyada mata Cikin Dariyarta yace"Ai Ani nuhu abokina ne..yama ce yana gaisheki..!
Ido ta zaro kafin tace"Da gaske.?
Ya sanni ne..?
Yana Danne Dariyansa yace"Sosai ai yasan Amina..Amina ta Gumel abakim Aminu..!
Amina ta Dafe kirji Murna Duk ya Cika Hanne taja gefen Hijabinta tana Fadin"AMINA kada wani ya fito fa ya ganmu..?
Hamida kuwa uwar tsoro sao waige take yi kafin tace"Amina kin sanshi ne..?
Hijabinta ta Fizge kafin tace"Dillah..ku na sanshi ba..Shagon chan muka hadu kwanaki da mamanmu ta aikeni..!
Har yace ina Burgesa ko..?
Tafada tana wani juya ido Kai ya gyada yana kallonsu Hamida kafin yace"Sosaima
.gaskiya kuma Laifin ku me da baku taba Fada mata ita din abar Burgewa bace!
Amina ta washe baki kafin tace"Kun ji ko..?yauwa gayamusu..Ni da suke cemin ina naga abun burgewa
Sai ma ma gundiri mutane da Halina..!
Tafada tana bata Fuska da Sauri yace"Kada ki damu..Ni kina Burgeni..!
Hamida taga Amina ta Zake da yawa hannunta ta Fincika tana Fadin"Amina kada wani ya ganmu fa..?
Hanne tace"Bawan Allah don Allah ka tafi jidalin Amina ne kawai..In wani cikin yan gidanmu ya ganmu Dakai yau mun shiga uku..!
Amina ta kwace hanmunta tana Fadin"Dillah sai me..?iyaka duka ne kuma baya kisa..!
Hannw tace"Baba Mallam kinsan baya nan bamu da maceti sai Allah Amina..!
Wa kika taba ganin ya tsaya da wani..?ko su ya Abida kin taba gani..?
Amina ki shiga Hankalinki..!
Sai kuma tayi shuru ta tsaya tana kallon Hanne kafin tace"Kuma fa hakane..muje..bawan Allah sai an juma..Yauwa don Allah ka kara gaida min Ani nihu..!
Hamida tace"A ina kikasan Ali nuhu mu da ba kallo muke yi ba..?
Amina tace"Dillah Ani nihun ne baki sani ba..?dam wasam hausa fa ki bari gobe zan miki hotonsa a bakin Unity ashagon nan ma kusa da Bola gasu nan kala kala!
In Tana mgana Nishadi ke kamasa Shiyasa ya shagala yana kallonta baisan sun wuce ba suna gabda Shiga gidan ya Daga Muryansa ya Kirata.
Amina..!
Dukkamsu suka juyo suna kallonsa Cikin wani yanayi yana kallomta yace"Wlh da gaske nake yi kina Burgeni...
Sannan KUma..INA SON KI..!
DAM!
dukkansu gabansu ya Fadi Amina ta zaro ido ya sake Daga mata kai kafin yace"Wlh da gaske nake ina sonki.!
Zam dawo ki jirani..!
Yafada yana kallomta Hanne da Hamida ta kallah kamar sun ga abun Tsoro suka Rumtuma suka shige gidan da gudu kai ya girgiza kafin ya Furta"Finally dai na gano abunda ke Damuna
Son yarinyar nake yi..!
Daga haka yajuya ya fara Tafiya wajen Mota Nura na gamin haka ya Tuko motar zuwa gabansa da azama ya Budamai gaban Motar ya shiga ya maida Rufe suka fara barin anguwan ammh Idanuwam Aminu na kallon Kofar gidamsu Amina kamar tatafi da ransa Nura na binsa da kallonbTsausayi.
Nura ya kada kai kafin yace"Inau muka Nufa Oga..?
Idanuwaansa na shigewa kamar mai barci yace"Mu koma Hotel..Nura son yarinyar nan nake yi..Bazam koma kano ba sai na samu Soyayyarta..!
Nura yace"Ta wata hanya..?
Dokar gidansu ce ba sa soyayya kuma na Fada maka..!
Bai damu ba kai Tsaye yace"Koma ta wata hanya ce
.Zan sakata ta soni
In ta soni komai mai sauki ne..!
Nura ya kasa mgana ya fara Tunamin Amina mayyace ta kama Ogansa.
Su kuma su Amina a haraban gidan sukac Burki suka tsaya suna maida Numfashi.
Hamida tace"Amina mutumin bai da Hamkali ko..!?
Hanne tace"Ke ina ga wasa yake mata..!
Duk Amina na jinsu karo na Farko yau aka taba cewa ana sonta acikin Idanuwam Aminu gaskiya ta gani ita kanta Zuciyarta ta kasa Fassara yanayinta yasa ta Biye ma su Hamida da Fadin"Bai da hankali..Inaga bai da hankali..!
Kai suka gyadata mata atare suka Furta"Gaskiya bai da hankali..!
Da haka suka watsar da mgamar sukanufi Cikim gida Ammh banda Amina ta kasa goge Kalaman Aminu ko wani juyi tayi acikin Ranta sai taji muryansa.
Amina..Kina Burgeni..Kuma WLH INA SONKI.!
Batasan Dalili ba taji abun ya zauna acikin ramta sannan tana ji tana so ta kara ganinsa taga wannan Gaskiyan Data gani acikin idonsa..!

Mafarin komai...!

*Janafty*
[11/3, 2:05 PM] Sweet sis: *TA FITA ZAKKA..!*
_(Aminene)_

*Wattpad:JamilaUmar351*
*Mallakar:Janafty❤️*

*🅿️17*

Da gaske yake yi Duk abunda ya fito Daga cikin zuciyarsa bai gasgasta haka ba sai da ya koma kano ya kasa zama kwama uku yayi ya saka Nura ya Tukosa zuwa Gumel,batare da Amina ta sani ba yake Bibiyanta ahotel yake zama In garin Allah ya waye zai zai kofar gidansu Amina Daga baya domin yaga tafiyarsu makaranta da Lokacin dawowarsu da Lokacin Tafiyarsu islamiya wasa wasa sai da yasan komai na Amina sannan yana Bibiyan dukkan Motsinta,Batare data sani ba Nura gajiya yayi ya koma Abunsa Tunda yaga alamun Ogan nasa ya kamun da gaske.
Baya sati bai shigo Gumel ba,Duk saboda Amina zai zo ya ganta yaji Sanyi aransa koda bata gansa ba koda bata sani ba ya gama yardan ma kansa Amina ta shiga ransa ta samu matsugunnun da bai zai iya cireta ba komai nata yana Burgeasa ne..
Amina bata son Aminu na binta ba Ba kuma wai don ta manta da mganarsa ba akowani Shafi na Tunanin kalamansa bai bace mata ba sai dai Tundaga Ranar bata kara yarda sun kara mganar da Su hanne ba suma sun Dauki abun a wani abu dabam shiyasa suka watsar da mganar suka Cigaba da Harkokinsu.
Chapter 47 · 0% Book details