← Book details Ta Fita Zakka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 186 OF 193

Sashe 186

Ta Fita Zakka Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Amina taso taje gidajen yan"uwanta Mata Mallam ya hana yace ta shirya tabi mijinta alokacin Sai Hajiya ta hana tace sai dai yaje ya Dawo ,sai ya tafi da ita Lokacinn yaran sun kara wayau bazai Daukesu tana Danyen Jego ya Hau jirgi da ita.
Sannan kuma zatayi Jarabawaarta ta Fita alkawari tayi kuma sai ta cika.
Mallam sai yama kasa mgana Daga baya yaso ya nuna ma Hajiya bata isa ba sai dai data mai bayani sai ya gane gwara Amina tatafi da Tarkadunta sannan yaran su kara Wayau shi ya Lallashi Danmallam da bai da tacewa Hajiya ai tagama dashi.
Ya samu Amina yana mata magiyan taje tace ma Hajiya ita zata Bisa su tafi Amina tace bazata iya ba sai yayi Fushi batare da sanin kowa ba ya Nema ma kansa Visa shi da Sakina Sai ana Saura kwana Biyu Tafiyarsu yaje ya Daukota Sakina sai da tayi kuka har ta cire rai da auranta da Umar ganin san da suka zo ko fuska bai Sakin mata baHakama yan"uwanta nata jin Dadi,Gidan mallam ya fara kaita Hajiya da mallam suka Taru suka mata Nasiha mallam kanshi yaji Dadi yadda Umar ya zama mai Afuwa
Sai alokacin yake shaida musu jibi zasu koma Madina shi da ita Hajiya tasan don Turama Amina Haushi yayi sai bata nuna mai ba kuma bai Fadama Amina zai koma ba Dauke mata kafa yayi ana gobe Tafiyar yazo yaga yaransa ita tana barci sai da Safe Yakaka ke Fadamata,Bata san ya tafi ba Sai da sukayi waya da ya Aisha take Fadamata Ya Danmallam ya tafi da Sakina itama Hajiya ke Fadamata Ranar Amina wuni tayi kuka Yakaka na lallashinra abun fa da Ciwo aiko bai Fadamata komai ba ya Fadamata Zai Dawo da Sakina ammh Duk Sai dai Taji Daga sama itama sai ta Zuciya ta Cigaba da kula da kanta da ya"yanta.
An biya mata Jarabawar ta a Unity dinsu da an fara zata fara zuwa sannan Huce Takaicin abunda Danmallam yayi musu Hajiya ta saka Baki mallam ya barta sukaje Abuja suka kwana Biyu ita da Yakaka dagachan har da ya Aisha suka Dumguma sai Zaria wajen Hamida suka kwana Daya gidanta suka kwana Gidan ya Zulfa suna ta murna da ina suka saka da yan"uwansu sun je har kaduna gidan Abida sun je kano gidan ya Jidda Lagos ne da parthercourt yayi nisa basu je ba Amina ta taka yola Wajen Hanne sai gata agidan Aminu Taga Nenne Dangi kuwa sai zuwa ganin Aminan Aminu ake yi yara kam sun sha Dauka shi kanshi Aminun ya kasa sukunu ya siyo wannan ya siyo wanchan,Amina sai yi ma Hanne Tsiya take ganin ta da Ciki.
Kwanansu Biyu suka Dawo Gida suka Sauke Gajiya..
Danmallam bai nemeta ba itama kishi da Haushin Abunda yayi mata ta yi biris dashi,Shi ma Yayi zuciya ransa ya baci da abunda tayi mai sannan kuma bayan ya tafi bata nemesa ba abakin Mallam yaji Tafiye Tafiyen da Amina tayi ko izininsa ba"a nema bai Taba Jin Haushi in Hajiya ta yanke Hukunci kan matansa ba sai kan Amina ya Lura tafi son Ma Amina da kowa komai take so shi take yi..
Amina Taurin kanta bai barta ba,Tana nan dashi shiyasa ta nuna ma Danmallam kalanta Har Yakaka taji Haushinsa Sai dai tayi ta lallashin Amima kada ta Damu sai ya Nemesu.
Ana cikin haka suka fara WAEC ta Dinka sabbin kayan makaranta ta fara zuwa Ranar datake da paper yakaka take barin ma yaran Agidan mallam in ta Dawo sai ta biyo sai yammah su koma gida Domin yakaka bazata iya Ronon yaran ita kadai ba gasu sun fara girma da kiba suna samun kulawa sosai..
Tana kokarin ya kice Takaicin Danmallan aranta taurin kanta yasa bata ko nemesa ba shima yaki nementa Amina tasan yaushe zai nemeta yanan chan wajen Guzumanyen matansa ita kuma tana nan tana mai renon ya"ya..!
Zai gane shayi ruwa ne da Aminene yake zencen..!

*Godiyata ta musamman ga iyayena guda biyu da sune silar tsayuwa kan kafafuna da nayi ayau din nan Alhaji Umar Muhammad mailoki da Malama Hadiza Muhammad Ba"are,Baba, mama ina matukar godiya da jajircewan ku akaina Ina godiya da Goyon bayanku ina godiya ga Allah da kuka kasance iyaye nagari a wajenmu Allah ya saka muku da Alheri ya muku Tukwaici da gidan Aljannah Firdausi Ameen Ina matukar son ku Babanmu da Hajiya mama tamu Allah ya kara muku nisan kwana da kwanciyar Hankali Ababen Alhafarinmu..*

*Janafty*
[11/3, 2:16 PM] Sweet sis: *TFZB2031*

*Ki biya ki karanta cikin Salama kiyi ma girman Allah in baki biya ba kada ki karanta sannan kuma kada ki yada'ashi..Pay N500 via Jamila Umar gtb 0552179550 ko katin waya ta wannan lambar 09069067488*
Chapter 186 · 0% Book details