← Book details Ta Fita Zakka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 189 OF 193

Sashe 189

Ta Fita Zakka Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

"Amina..!

Da farko taso tayi Ficewarta ne sai kuma ta ja ta tsaya bata juyowa ba Da Hanzari ya taka har gabanta ya ja ya Tsaya yana Binta da kallo ita kuma ta Kara Hade rai cikin mamaki yace"Me kika yi haka?
Amina tace"Dani da ya"yana bamu da Muhalli a wajenka..saboda banga amfani Daukan su da zakayi ba..!
Baki ya saki yana kallonta Duk da yasan za"a rina Daman rigima sai wacce ya gani sai dai bai nuna ya karaya ba ya mika mata hannu yana Fadin"Bani su..Sai muyi mganar Daga baya..!
Amina ta kallesa Daga Sama har kasa kafin tace"Wadanan ya"yan Amina ne sai ka bari in Sakina ko Sarood dake da Mutumci a idonka sun haifan maka sai ka Dauka..Bani waje na fice kafin Raina ya kara baci kaga abunda baka Taba gani ba wlh..!
Sai mamakinta ya kamasa yadda take kallon Tsabar idonsa tana mai rashin kunya sai ya tsawarta mata yana Fadin"Ban sauke kaina kasa don ki raina ni ba Amina ki shiga Hankalinki..!.
Wata Dariyan Rainin Hankali ta sakamar kafin ta raba ta gefensa ta Fice Daga dakin ransa ya baci yabi bayanta yana Fadin"Amina ki dawo nace..Nace ki dawo ko..?
Amina ko Sauraransa batayi ba ta Fada Dakin Yakaka shi bai yi zaton Yakaka na Dakin ba ya bi bayanta kawai sai suka Hada ido da yakaka Amina na Tsaye ta Cika kamar ta Fashe Daman Yakaka tasan yadda Amina ta Zuciya Danmallan bazai ji Da Dadi ba.
A matsayinta na Babba yasa ta mike Daga zaunen Datake ta mikama Amina Hannu tana Fadin"Bani yaran..Ki koma ku cigaba da Rigimarki kada ku saka yaran da basu san me Duniya ke ciki aciki ba. !
Sanda ta Fadi haka sai Danmallam yaji kunya ya koma da Baya ya fice Daga Dakin Amina sai ta sakama Yakaka kuka ita kuma ta karbi Aba ta kwanto Mallam Dake baya tana Fadin"Ban son Sakarci kin gama kuma Nuna mai Matsayinki ya tako ya Biyo ki sai ki Bata wayonki..?
Maza Share hawayenki kada ki sake mai kuka kije ki karbi Lallashin shi ko Banza yasan Darajan ki yanzu..!
Amina ta Share Hawayenta sannan ta juya ta Fice Yakaka ta bita da kallo aranta tana Fatan Allah ya Daidaita Tsakanin Ma"auratan..!
Amina na komawa Dakin ta iske shi Zaune gefen gado yayi Tagumi yana ganinta ya taso zai riketa ta kauce ta sakamar Jajayen idanuwanta tana Fadin"Bana so..Kada ka tabani..!
Sai ya Janye mata Kan gadon ta koma ta kwanta ta Juyamai baya sai kawai ya koma ya zauna ya kara yin Tagumi.
Yana mamakin Amina zata Haukatasa ganin kamar ma batasan yana Dakin ba yasa ya Sauko Ya Duka a Gaban gadon inda yake kwance yana Kiran sunanta..!

Amina..!
Noor..!
Chapter 189 · 0% Book details