← Book details Ta Fita Zakka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 64 OF 193

Sashe 64

Ta Fita Zakka Part 1 Complete Hausa Novel · about 9 min read

haka kurum mallam awannan Lokacin bazai kirata ba,Dazu Shamsu ke fadin yana asibiti wajen Sa"idu Har wayar ta kusa yankewa bata Daga ba sai Daga baya ta Daga kiran tana Fadin"Assalamu Alaikum Mallam..!
Dagachan Haraban asibitin Baba Mallam yace"Marliya kina ina ne..?
Cikin mamakinsa tace"Ina gida mana Mallam..!
Kai Tsaye yace"Marliya abunda ya faru jiya gidan Sa"idu kuskure ne da Rashin Fahimta ko..?
Cikin Mamakinsa da Tunanin inda ya Dosa tace"Hakane..!
Cikim Dattakonsa yace"To mu barsa ahaka..Kada na sake naji mganar nan ta fita..In har najita a waje Nasan kece..Bana son surutu da mgana Hajiya kinsani bata da wannan Halin Saboda haka ki kiyaye..!
Anty Amarya taji ta Muzanta Ranta ya baci wato Hajiya ba ruwanta itace mai Surutu ko lalle ne Mallan dinnan.!
Danne bacin ranta tayi tana Fadin"Ah..Wlh ban fadama kowa ba Mallam..yanzu dai nake shirin shiryawa na shiga gidan na Duba Amina ya jikin Sa"adun..?
Fata ya samu Sauki..!
Cikin son Dakile mganar yace"Yaji Sauki..Kada ki fita ko"ina nima ganinan zuwa. !
Bai jira cewarta ba ya Datse kiran yana wani nazari yasanta da kananun mgana sarai shiyasa ya taka mata Burgi in ba haka ba,kafin wani Lokaci ta gama Fesama ya"yanta su kuma su fara yawo dashi mgana har ta fita wacce bata da wani amfani..
Ita kuwa Anty Amarya Sororo tayi da waya a Hannunta mamaki bakin ciki da Kishi sun Turniketa wayar ta Dangwar nan saman gado tana Fadin"Aikin banza..Abunda kake son ka Rufe mallan bazai taba Rufuwa ba..Ko ba"a bakina ba Lalacewar Amina sai ya fita Duniya..!
Abunda bai sani ba ta Fadama ya"yanta Sa'adatu da Jidda da Sadiya Jidda ce kawai bata Dauki mganar ba Ammh Sa"adatu har tana Fadin daman idanuwan Amina na rashin gaskiya ne sannan abakinta Anty Amarya tasan Amina na karancen karancen Littafan hausa Sadiya dai da Uwar ta fadamata batace komai ba Domin bata cika Hayaniya ba.
Wayar Sakina tayi ta nema ta Tsegunta mata bata sameta ba Shiyasa da Tuni Labari ya isa Saudiya Arabia..!
Tana shiryawa tana Tsaki ita kadai ta rasa me Hajiya Babba tafi su da Mallam yake Fifitata akansu ta manta tun Tale tale Take tare da Mallam din kwafa tayi afili tace"Daga ita har Sa"idun duk sai nayi mganinsu Algumgumai duk su ke zuga Mallam..Da basu da Tuni nice Tauraruwa awajensa da gidan gabadaya..!
Abunda bata sani ba,ba irin Mallan ake ma haka ba ko ta manta Malami ne wanda bai zauna ba,kariyar Allah Tana Tare dashi kuma ilkonsa bazai bari acutar da bawansa ba..!
Baba Mallam na asibiti kafin ya baro ya Kira ya Jafar yace ya siyamai Dabono da Goro mai yawa zai yi amfani dashi bai damu ba sanin kila Mallam din zai yi wani abu dashi sai dai abu daya ya bashi mamaki Dayace su samu sallar azahar anan masallacin gida shima gashinan zuwa..!
Koda ya tafi Aba na barci Nurse tazo tamai allura kila tana saka barci ne shi kuma sai bai tashesa ba Idi Direba ya Kira yazo ya Daukesa zuwa gida Kai Tsaye Shashensa ya wuce domin ya Shirya Tunda azahar din ta kusa Shi kadai kawai yake jin karfin Gwiwa da alhafarin wani abu akaron Farko zai cika wani Burin Daya Dade acikin ransa bai Mutu ba kuma da Ransa..!
Wanka yayi ya shirya Cikin Shadda Fara harda babban Riga dataji aikin Hannu ya Dora rawaninsa sai ya Fito Tar dashi Farin gemunsa na kyalli yana tashin kamshinsa kamar koda yaushe adaidai Lokacin ya samu wayar Jafar yana Fadamai ya siyo abunda yace asiya din Baba Mallan yace yana cikin gida gashinan Fitowa..!
Bai Fadama kowa komai ba acikin gida yayi alwalansa ya fito Mutane basu wani mamaki ba in yana gari dashi ake yin sallah duk da akwai Limamin masallacin Mallam Muhammad Dayyab in Baba Mallam bai nna shi ke kula da masallacin har ya jafar da Ya Nasir suna bada Sallah da Mangariba haka ko isha"i Mallam din ke sakasu saboda gaba in watarana ya fadi ya Mutu ace akwai masu bin bayansa Koda Umar da Nazir basa kusa akwai Jafar da Nasir manyan dake bin bayansu..!
Kowa ya zata Baba Mallam din zai bada sallah sai dai ana shiga masallacin yace Mallam Muhammad yajasu Sallar,to sai mamakin bai yi yawa Tunda yana haka sau tari dadama.
Mallam Muhammad ya bada salla ana Idarwa Baba Mallam dake sahun gaba ya matsa gabansa sukayi kuskus kafin Mallam Muhammad din ya sanar da Daurin aure da za"a Daura shi yanzu Baba Mallam sai annuri yake yi Ya Jafar da Nasir Dake layi na Biyu ya yafito da Hannu Sai Shamsu Dake gefe duk suka taso suka kariso gabansa gaban Liman Mallan Muhammad..!
Suna karisowa yace su zazzauna suka zauna nan gefensa Cikin Dattakonsa yace"Jafaru dauko sakon nan..!
Ba Musu ya mike ya fita daman acikin Motarsa ya bar Huhun goron da Ledan Dabibon yaje ya Dauko ya kawo ya Mikama Mallam ya karba ya Mikama Mallam Muhammad yana Fadin"Araba shi Liman..araba ma Jama"a..!
Ba Musu Limam ya bama Ladani Umarnin ya rabama kowa Dabino da Goronsa kamar yadda aka saba Cikin Kankanin Lokaci yabi layi layi ya bama kowa,Mutane basu yi mamaki ba sanin Daman amasallacin bazanga koda yaushe cikin kawo Daurin aure akayi shiyasa ba wanda ya damu ammh su Ya Jafar sun Tsargu ballema da suka ga yadda Baba Mallam ke ta Annushuwa kuma yana gaba gaba kan komai ko auransu Zulaihat bashi ya bada ba su ya Danmallam ne suka Zama Waliyansu..!
Basu gama mamaki ba sai da Liman yace"Allah ya gafartama Mallam an gama Raba Goron da Dabinon har yayi saura ma..!
Baba Mallam ya Jinjina kai kafin ya karkace ya zaro Bandir din kudi Sabbi yan Dubu Dubu ya ijiye gaban Liman Cikin Dattakonsa yace"Walicci zakamin Mallam Muhammad..?
Cikin mamaki yace"Waliccin wane kuma Allah gafarta mallam..?
Baba Mallan sai da ya kara Fara"ar Fuskarsa kafin yace"Waliccin Umarun Faruku zakamin aure zan kara masa ayau din nan acikin wannan masallacin..!
Liman yace"To..To..Masha Allah ai babu Laifi Allah gafartama Mallam sai Waliyan ita yarinyan su matso afara siga..!
Baba Mallam ya Murmusa kafin yace"Nine Waliyan Amarya..Ga Sauran yan"uwanta nan..!
Ya nuna su ya jafar da suke zaune mamakin kalaman Baba Mallam ya cika su.
Cikin karin mamaki Liman yace"Au kace Abun duk na gida ne..To masha Allahu..Ba bu laifi sai mu fara gabatar da siga ya sunan Amaryan..?
Sai da Baba Mallam ya gyara zama kafin yace"Sunanta AMINA..AMINA SA"IDU..!
Jafar da Nasir suka kalli juna kafin su juya suna kallon Baba Mallam Shamsu kuwa Kunni ya saki yana jin abun kamar almara..!
Liman ya washe baki yana Fadin"To..To..Masha Allahu wannan abu yayi kyau..Allah yasa a kulla alheri..!
Zamu fara gabatar da siga..Ladan ya Ciremana Lasifika..!
Da Sauri Baba Mallan yace"A"a abarta Liman..!
Liman cikin mamaki yace"Dokarka ce Allah gafarta Mallam ba"a Daura kowani aure cikin Lasifika..!
Baba Mallam cikin Annuri yace"Na yau kadai na Sauke Dokar liman..So nake naji Sautin Tattabatuwar auran Uwata da Umaru so nake na ji Sosai acikin kunnuwana Liman..!
Liman bai yi gaddama yace abar Lasifika,cikin Abunda bai fi mintina goma sha Biyar ba aka gabatar da siga aka kuma Tabbatar da Daurin auran AMINATU SA"IDU GUSAI da angonta Mijinta UMAR YUNUS ABDURRAHAMAN BAZANGA akan Sadaki Naira Dubu Dari Cif..!
Adaidai Sanda Muryan Ladan ta Karade Lasifikan yana kara Jaddada Daurin auran Amina da Umar din Akan Sadakin da uban Amarya kuma Uban ango ya Biya Mallam Yunus Abdurrahaman bazanga..!
Awannan gabar Alkawarin Allah ne ya cika..!
Zanen kaddara ya tabbata..!
Auran ya Dauru.!
"fallasa wasu sirruka ne..!
Dalilin wannan auran za"a rasa rai..!
Fuskokin wasu amintattu zata bayyana..!
Zuciyoyin wadanda basu taba Tsammani ba zata girgiza..!
Abunda basu taba zato ba ya faru alokacin da basu shiryama hakan ba..!
Wasu sun makara..Saboda Alkalamin ya riga daya Bushe ko sunzo kafin Lokacin Allah bazai sauya wannan kaddaran ba SABODA RUBUTTACIYA CE..!
Daurin auran daya Faru a kunnuwan mutane Dadama da suka cika da Dimbin mamaki wadanda da basu yarda ba Sa"idu ba dan Mallam bane yau suka kara yarda da mganar wasu Mutanen yadda Baba Mallan ke Hannu da Mutane kawai zaka Fahimci yana cikin Farimcikin da bai Taba tsintar kansa aciki ba shi ya Hana Jafar ko Nasir cewa wani abu suma sai sukabi ayarin yan gaisawa da Mutane suna faman amsa Fatan Alherai daga kowani bangare..!
Baba Mallam Dakyar ya samu ya Fito daga masallaci su Jafar ya kallah yana Fadin"Ku scigaba gda amsan Fatan Alheri jama"a bari nayi wata waya..!
Daga haka yayi nesa da Masallacin ya Fiddo wayarsa ya Kira Danmallam..!
Tana gabda Katsewa ya Daga Kiran Cikin Mutuwar Jikin da Baba Mallam ya Saukarmai Tun Safe daya Kirasa yana Fadamai zai aura masa Kazamar yarinyar nan..!
Cikin Farimciki Baba Mallam yace"Umaru..!
Dagachan bangaram Muryansa a shake yace"Na"am Baba..!
Bai jira cewarsa ba ko yanayinsa ba yace"Yanzu nan aka Daura auranka Da Uwata..Ayanzu din nan AMINA ta zama Amanarka Umaru..daidai da Rana Daya in kaci Amanarta ko ka Dannen Hakkinta Allah na kallonka sanna amatsayina na Mahaifinka ban YAFE maka ba Umar daidai da Rana Daya in ka Zalunci AMINA.!
ya karishe Fada Cikin kaushin Murya
Gabadaya sai yaji kamar Duniyar na Juyawa dashi wannan shine gaba kura baya Damisa..!
Baba Mallam bai Damu da amsar ba ya Cigaba da Fadin"Ina Alfahari dakai..Yau ka cikamin Burina Umar..albarkata da addu"an Allah ya baka Zuru"ata tagari bazata yanke Daga bakina ba..Ina Rokon Allah yasa Amina ce Sillar Arzikinka da Daukanka..Ina ji ajikina Uwata ce Farincikinka watarana ko bana Raye alokacin nasan zaka Tuna dani Umar..!
Jin Mallam kawai yake ta ina wannan kwailar yarinya zata zama Farincikinsa watarana..?
An dai hadasa da aiki Yarinya kazama ga rashin Natsuwa da Taurin kai da rashin ji yana zaman zamansa Mallan ya Debo masa aiki Sai dai shi Yaro ne mai Biyayya har abada baya Fatan Ranar da zai Sabama Iyayansa..!
Shiyasa Cikin karfin hali yace"Nagode Baba..Allah ya kara girma..Insha Allahu zaka sameni mai biyayya..!
Baba Mallam cikin jin dadi yace"Nasani..nasan bazaka watsamin kasa a ido ba..Allah yayi maka albarka..!
Ya amsa da Ameen Daganan sukayi sallama bayan ya tambayi jikin Aba yace da Sauki sannan suka rabu da juna da cewar shi Danmallan din zai kira wayar Baba Sa"idun Baba mallam yace ya Kirasa Jafar ya Tahomai da wayarsa da Safe..!
Abunda kowa bai sani ba Tun Da Asuban nan da Danmallam ya Kira Baba Mallam yaji aransa wannan mafitan ne Allah ya nuna masa.
Bai yi shawara da kowa ba kafin ya tafi asibiti wajen Aba ya kirasa suka Tattauna Komai Daga farko har karshe sai da ya Fadamai duk abunda ya Faru kwanaki da na jiya Daddare da kalaman Baba Sa"idu da Rokonsa garesa ya kuma Roki Danmallam Daya auri Amina ba domin Umarni ba sai domin daman Yana da Burin Hada Dansa ko yarsa da Ahalin Sa"idu..!
Umar bai iya cewa A"a ba..Mallam ya wuce gaddama garesa Cikin wani yanayi ya amsa masa da cewa Ya amince wannan kalaman nasa su suka Tabbatar da Kaddaransa da Amina Kaddaran zama amtsayin miji da Mata..!
Chapter 64 · 0% Book details